GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

HAƘƘOƘIN MA’AURATA GA JUNANSU.

bari mu fara da haƙƙin macce akan mijinta.

HAƘƘIN MATA A KAN MIJINTA.

Haƙƙoƙin mata a kan mijinta suna da tarin yawa.
Kuma ya zamo wajibi a kan mai gida ya tsareshi dai-dai gwargwadon hali, kuma wannan haƙƙoƙin Allah da Manzonsa sun tabbatar dashi, ga faɗin Allah madaukakin sarki akan haka inda yayi mgna cikin Suratul Baƙara aya ta 228:-
(WALAHUNNA MISLULAZII ALAIHINNA BIL MA’ARUF WA LIRRIJALI ALAIHINNA DARAJAT)
Mata sunada haƙki a kan mazansu kamar yadda aka sani. Sannan maza suna da wata daraja akan mata.
Haƙƙokin mace a kan mijin ta, suna da yawa amman ga wasu daga cikinsu.

(1) Wurin zama ga matar aure wajibi ne a kan mijinta. Miji zai tanadi wurin zaman matarsa gwargwadon ikonsa da samunsa kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin Suratul Ɗalak aya ta 6:-
(ASKINU HUNNA MIN HAISU SAKANTUM MIN WUJIDIKIM WALA. TUDAARUHUNNA LITUDHAYYIKUM ALAIHIN)
Ku zaunar da matanku inda kuke zaune wato gidajenku.
Ba mummunan wurin zamaba kada ku cutar dasu don ƙuntata musu.

(2) CIYARWA.
Ciyarwa yana daga cikin abubuwan dake wajabta kan miji wato wajibi ne miji ya ciyar da matarsa, kuma ciyarwar zai yishi ne gwargwadon ikonsa kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace a cikin Suratul ɗalak aya ta (7).
(LIYUN FIƘ ZUU SA’ATIH MIN SA’ATIH, WA MAN ƘUDIRA ALAIKU RIZKUHU FALYUNFIƘ MIMMA AATAHULLAH LAA YU KALLIFULLAHU NAFSAN ILLA MAA AATAHAA SAYAJA ALULLUHU BA’ADA USRIY YUSRAA).
Ma’ana.
Mawadaci sai ya ciyar da abinda Allah ya bashi na wadata, shi kuma wanda Allah ya ƙaranta masa arziƙinsa to sai ya ciyar daga abinda Allah ya bashi. Domin Allah baya ɗorawa bawa abinda bazai iyaba kuma ka sani Allah zai baka wadata bayan ƙuncin da ka shiga.
Dangane da hadisin Annabi (A.S.W) yace a hadisin da a ka ruwaito daga mu’awiyya Bin Haidatu Allah ya ƙara masa yarda yace:
Sai muka tambayi Manzon Allah (S.A.W) shin menene haƙƙin mata akan ɗaya daga cikinmu?. Annabi (S.A.W) ya ce.
“Idan kaci abinci to ka ciyar da ita, idan ka ɗinka sutura to itama ka ɗin ka mata, sannan kuma in tayi maka laifi zaka bugeta, to kada ka bugeta a fuskarta kada ka munanata, idan zaka ƙaurace mata to kada ka ƙaurace mata a woje sai dai a ɗaki.”
(3) Kyakkyawan mu’amala.
Shi mu’amala mai kyau babban abune ga ma’aurata.
Especially shi miji, yana daga cikin haƙƙin mace akan mijinta, yayi mu’amala mai kyau da sakin fuska a tsakaninsu, raha da barkwanci ta yadda zasu shaƙu da junansu.
Lallai waɗannan muhimman abubuwane da miji zai kiyaye su, kuma wajibi ne miji ya yawaita nasihi da wa’azi ga matarsa a kan harkar addini da sauran al’amuran yau da kullum sai dai a kula wurin nasihar da wa’azin kada ka tsananta kuma kada ka sake kwarai sabida sani yadda mata suke murɗaɗɗune sai anyi da lura.
Duba da wani hadisin da Annabi (S.A.W) yana cewa a cikin hadisin da aka samo daga Abu Huraira inda yake cewa. Manzon Allah (S.A.W) yace:
“Mafi cikar mumini a wajen imani shine wanda ya fiku kekkyawan ɗabi’a kuma zaɓaɓɓe a cikinsu shine wanda yafi Kyakkyawar mu’amala da iyalinsa.
A wani hadisin kuma yace.
Lallai ku sani cewa an halicci ƴa mace da ƙashin haƙarƙari ne bazata taɓa miƙewa gareka ba, wato ka sameta sak ba matsala, wannan kam bazai taɓa samuwaba in ka samu jin daɗinta to zaka samu jin daɗin ta ne a ƙarƙashin yadda take, (kuma ka sani in ka nemi miƙar da ita to tabbas zata karye.
Karyewarta kuwa shine SAKINTA saboda haka sai kuyi taka tsan-tsan acikin lamuran.”

Gyara zamanshi yayi da kyau, kana yasa hannunshi ya gyara gilashin fuskarshi da kyau,
Sannan ya sa hannunshi zai ɗauki goran ruwan dake gabanshi.
Da sauri ɗan agajin dake bayanshi ya ɗauki gorar kana ya buɗe ya tsiyaya mishi sassayan ruwan cikin kofi,
kana ya miƙa mishi sannan ya koma inda yake ya tsaya.

Amsa yayi yasha ruwan sosai kana ya ajiye cup ɗin.
Sunkuyar da kanshi yayi sosai sannan yasa hannunshi ya gyara hiraminshi ya rufe gefe da gefen fuskarshi.

Al’ummar jama’ar dake wurin kuwa kan sun nitsu sunyi shiru maza da mata manya da yara.
Kab an zuba mishi idanu alamun ana dakonshi yaci gaba.
Domin sosai walimar tayi armishi sabida dace da tayi da fasihin malami.
Shiru kakeji sai sauti A\C dana numfarfashi.
Aysha kuwa haka nan take jin wani irin mashahurin daɗi.
Gaba ɗaya tsikar jikinta tashi takeyi, tana jin Allah yayi mata babban rahama da ni’imar duniya da bata Sheykh Jabeer a matsayin Garkuwan ta mijinta.

Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi lokacin da yaji yace.

          (4)  SADUWA DA ITA.

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300.
0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa. Ta nan zaki turo kuɗin, sai screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276.

                    By
        *GARKUWAR FULANI*

Littafin nan na kuɗine, akwai Normal group 300 a wata biyu za’a kare Part 1 and 2, kiyi transfer’n dari uku ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276. In Kuma special Group kikeso wanda a wata ɗaya za’a gama Part one, two. 1k zaki turo ta ac no ɗin nan 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number da nake whatsapp dashi 09097853276.

                            Akwai kayan gyaɗa na amareni uwar gidaye sitin hawa-hawa ne, akwai na dedai talaka akwai na masu hannu da shuni, in kina buƙatar saya kimin mgn ta whatsapp 09097853276.

Idonshi ya ɗan lumshe kana ya ɗanyi ƙasa da kanshi cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
“Anan ana son miji ya dinga yin jima’i (Saduwa) da matarsa ko da sau ɗaya ne a cikin ko wanne tsarki ta, na Al’ada amman ƙaranci kada ya wuce wata huɗu ba tare da ya sadu da itaba kamar yadda wasu malamai suka faɗa, in bazai iya biya mata buƙatarta ba, kuma wannan za’a kauwacewa al’amarin jima’i kamar yadda al’ƙur’ani mai girma yace.
(Allah yayi mgna game da mazajen da suke barin matansu basu kula su har tsawon wata huɗu kai harma suna ƙarawa da rantsuwa bazasu tara (Sadu) da suba, to idan daga baya sun dawo ga iyalan nan to shike nan Allah mai gafara ne mai jinƙai.
Saboda haka idan muka dubi wannan ayar zamu fahimci cewa, idan miji ya bar matarsa tsawon wata huɗu bai sadu da itaba haka nan kawai ba tare da wani kyakkyawan dalili ba, to ya cuceta, kuma ana iya raba auren, Allah ya kiyaye.

Sai na (5) kiyaye mutuncinta kishi a kanta yana daga cikin mu’amala mai kyau tsakanin miji da mata ya zama miji ya kiyaye mutuncin matarsa da yin kishi a kanta, saboda haka wajibi ne ga miji yayi kishin matarsa ya kareta daga dukkan abinda zai taɓa mutuncinta da martabarta da dukkan abinda yayi kama da hakan domin mumini mai kishin gidansa ne, kamar yadda.
Dabarani ya ruwaito daga Ammar Ɗan Yasir Allah ya ƙara musu yarda, cewa Manzon Allah (S.A.W) yace.
Mutane uku bazasu shiga aljanna ba, 1 wanda baya kishin iyalansa 2 macen da take shigar maza, 3 wanda bai damuwa akan kowa da kowa ya shiga wajen iyalinsa.
Sai Sahabbai suka tambayi Annabi (S.A.W) suka ce,.
Ya manzon Allah shin dai bugegge sun san shi, to amman (Addayyus) wato mara kishi iyalinsa shine bamu sanshi ba. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace musu.
Shine wanda bai damuwa kowa da kowa kare da doki su shiga gidansa wato mutumin banza da wofi idan sun shiga gidansa baya damuwa.
Shi wannan hadisin ya nuna mana cewa dole mu tsare mutuncin matanmu. Wannan kenan sune kaɗan daga haƙin mata akan mijinta.

Sai kuma haƙƙoƙin miji akan matarsa.
(1) yin ɗa’a ga mijinta domin Allah ya faɗi a Suratul Baƙara aya ta 228. ( WA LIRRIJALI ALAIHINNA DARAJAH) Su maza sunada wata daraja a kan matansu.
(2) Kula da dukiyarsa wajibi ne a kanki haƙƙine wanda ya zama dole mata su kiyayeshi
Dole mace ta kula da dukiyar mijinta fiye da yadda shi zai kula dashi. Kamar yadda Allah Mai girma da ɗaukaka ya faɗa a Suratul Nisa’i aya ta 34.
(FASSALIHATU ƘAANITAATUN HAAFIZAATUN LILGAIBI BIMA HAFIZALLAH) Allah ya ambaci salihai mata masu ɗa’a ga mazajensu masu tsoron Allah masu kiyaye abinda ke ɓoye na al’amuran mazan aurensu sobada Allah yace su kiyayeshi, kiyayewar kuma ta haɗa da tsare mutuncin kansu dana mijinsu ko yana nan ko baya nan.
(3) Yiwa miji hidimar cikin gida kamarsu girki shara kula da yara da dai sauransu duk aikin macene.
Kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace.
(WALAHUNNA MISLULLAZZI ALAYHINNA BIL MA’ARUF) Mata suna da haƙƙi a kan mazansu kamar yadda suma maza sukeda haƙƙin a kan matansu.
(4) ikon canza mata wurin zama daga wannan garin zuwa wancan gari. Kamar yana aiki a jihar Ɓadamaya sai aka canza masa wurin aiki zuwa Tsinako to yana ikon ɗaukarta daga can zuwa nan.
Domin musulunci ya bashi dama kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace.
(ASKINU HUNNA MIN HAISU SAKANTUM MIN WUJDIKUM WALA TU DARRUWHUNNA LITUDAYYIƘUN ALAIYHIN) ku zauna dasu inda kuke kada ku cucesu ku ƙuntata musu wajen zama.
Idan muka dubi wannan ayar tana gargaɗin mazaje ne akan cewa kada ka sauya mata garin zuwa wani garin ya zama cutarwa a gareta.
In taga cutarwa ne nan zata iya ƙin zuwa in ya matsa ta gayawa waliyansu.
(5) kada mace ta shigo da wani mutun gidansu sai da izinin mijinta, domin wannan haƙƙine kuma damarsa ce.
Numfashi ya sauƙe tare da kallon taron mazan kana yaci gaba da cewa.
“A gurguje.
(6) Neman izinin miji dan yin azumi.
Baya halasta ga mace tayi azumi in dai na nafila ne sai tare da izinin mijinta matukar mijinnan yana gida tare da ita. Duba haɗisin daya gabata na haƙƙin maigida saboda haka ya zama dole mace ta nemi izinin mijinta kafin tayi azumi nafila amman banda na farillah”.
Haroon ne yayi wani irin murmushin jin daɗi kana ya kalli Jannart cikin raɗa yace.
“Kinaji kina ɗauka kina fahimta ko?”.
Longoɓar da kai tayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button