GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Duk garken da yaga yayi mishi to sai ya kwashesu tsan da wannan ya tara dukiyar dabbobin da shi kanshi baisan adadinshiba babu ƙasar da bashi da makiyayanshi kamar su.
Chadi, Nijer, Cameroon, Ghana, Gabon, Maroco, Senigal, da dai sauran kasashen makusantanmu kuma masu dabbobi, hikimar da yakeyi, muddin ya saci shanayen ƙasar Niger to sai ya cillasu ƙasar Senegal, in kuma makiyayanshi na ƙasar Sanigal sukayi sata to sai ya turo shanayen ƙasar Gabon, haka dai yake banbance mazauninsu.

Sai dai garin zamansa ɗaya ne Rugar Bani, inda nan aka haifeshi mahaifinshi Bukar wanda babarbaren Norba ne saye da sayar da kanwane ya ajiyeshi cikin rugar FULANI shiyasa ya zama dilan saida kanwa, sabida dole duk bafulatani makiyayi yana ta’ammali da kanwa dan ana zubawa dabobbi susha a ruwa ko asa musu a dusa ko harawa yana musu mgni.

Ba’ana ya shiga cikin Fulani ya saje dasu.
Yayinda hakan ya bashi damar da duk duniya ake ɗaukarshi matsayin bafulatani, koda yake hakan baya rasa nasaba, da kallon da mutanen duniya sukewa duk mutumin da akaga shanu, tumaki a gabanshi tofa ko wacce gabilace shi, ya zama bafulatani, wanda kuma sam ba haka abin yakeba.

Mahaifiyar Ba’ana ɗaya daga cikin ƙabilar ɓachama ce,
wacce Bukar ya aura tana a matsayinta na anniya, koda kuwa suka haihu ɗan su. Bukar ya rinjaye ta Ba’ana ya kasance musulmi, sai daifa a baɗini baƙar zuciyarsa da aiyikansa na kafuraine, sata kuwa a wurin babarsa ya gada.

Ba’ana kekyawan mutun ne ajin forko wanda ya gaji wannan kyan ne a kakarshi mahaifiyar babanshi wacce take shuwa Arabce, koda maƙiyinshi yasan tabbas Ba’ana kekyawane.

A duniya kab Shatu ce tasan sirrinshi ciki da woje,
sai daifa bata san yana sataba, amman duk wani abu na asiri da yadda za’a karya asirin da kuma yadda yake juyewa duk ta sani.
To hakanne yasa sam bata fatan ya zama miji a gareta bare uban ƴaƴanta, sai dai babu yadda ta iya. Domin ya mata babbar rana a rayuwarta ya mata taimakon da yasa aka ɗaukar mishi al’ƙawarin aurenta.
Gashi kuma duk wanda yace yana sonta karshenshi mutuwa, kuma yana gaya mata cewa duk wanda yace zai rabashi da ita zai kasheshi Wannan yasa kullum addu’ar shirya take mishi da fatan Allah ya rabata dashi lfy innshi ba mai shiryuwa bane.

Tafiya sukeyi cikin nitsuwa a hankali, murmushi yaketayi cikin so da ƙaunarta yace.
“Mata ya akayi na ganki da ƙaramar jaka?”.
Kai ta ɗan gyaɗa mishi tana kallon kekyawar fuskarshi, cikin murmushi yace.
“Kece kika ajiyeni a kasar Kautal a Rugar Bani, kina ƙare karatunki zamuyi aurenmu in ɗaukeki mubar ƙasar, kawai dolece tasa na hakura da batun aurenmu kiyi karatu, dan naga kina son karatun kuma nasan zaki karantar mana da yaranmu, kuma ina son ki zama babbar lawyer mai zaman kanta, sai ki zama lawyer na koda watan-wata rana, rana zata ɓacin min”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kamar yaune zan kare karatun, Ya Ba’ana”.
Kanshi ya rausayar tare da gyara riƙon igiyar jakar da yayi, kana yace.
“Allah ya nuna min wannan lokacin, in sha Allah sadakin aurenki Garken shanu ɗari zan bada”.
Cikin mmki ta zaro ido tare da cewa.
“Kai Ya Ba’ana garke ɗari bama shanu ɗariba, ya bana ina zaka samu wannan shanun kaida garken naku ko shanu hamsin bai cikaba”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Allah zai kawosu kafin lokacin auren namu”.
A hankali tace.
“Allah ya kawosu”.
Amin Amin yace tare da ɗan juyowa ya kalleta, murmushi yayi mata, kana ya miƙo mata jakar tata cikin so yace.
“Mun iso bakin Gari ki shiga.
Ni zan koma baya dama rakoki nazo nayi kar shaiɗanun bakin kogi su cutarmin dake”.
Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Ya Ba’ana lokacin sallah ya kusa fa ai gwara ka shigo sai kayi salla ka koma”.
Bakinshi ya ɗan tabe tare da cewa.
“No bar sallan nan sai bayan mako biyu ina ƙara dafa jikinane kuma in nayi al’walan duk aikin zai karye”.
Dafa kanta tayi da sauri tare da cewa.
“Wa’iyazubillah Wayyo Allah na Ya Ba’ana ka gane mana wannan abin da kakeyi shirka ne,”.
Kanshi ya jujjuya tare da cewa.
“Shiga cikin gari zanzo musha hira da daren”.
To kawai tace mishi ta juya ta nufi cikin garin.

Tana shiga ta kama hanyar gidansu, tana gab da shiga gidane ta haɗu da ɗan makotansu Iro cikin girmamawa tace.
“Ina wuni Ya iro”.
Fuska cike da fara’a yace,
“A a lale marhabin da ƙanwarmu yar al’barka anyi hutukenan?”.
Kai ta gyaɗa mishi sannu da hanya ya mata sannan ta wuce ya wuce.

A gindin bishiyar mangoro dake kofar gidansu gab da zaure ta hango Bappanta yana zaune bisa dakalin dake wurin yana al’wala, da sauri ta nufi in da yake fuska cike da jin daɗi.

Shima Bappa da sauri ya miƙe yana murmushi yake cewa.
“Maraba lale da ƴar al’barka.”
Da sauri ta iso inda yake tana murmushi mai nuna tsantsar jin daɗinta tace.
“Oyoyo Bappa na, Alhamdulillah na sameka lfy, ya Ummey na da Innata?”.
Dariya yayi tare da matsota yace.
“Duk muna lfy”.
da sauri suka juyo ta cikin gida jin muryar yayunta suna cewa.
“Oh wato mu kam bakiyi kewarmu bama ko?”.
Da sauri tayi gabansu cikin jin daɗi tace.
“Oyoyo ƴan uwana Ya Gaini, nayi kewarku mana, musamman Ya Giɗi sarkin son girma”.
Murmushi sukayi dukansu,
Seyo ne ya kalleta tare da cewa.
“Wallahi yanzuma mgnarki mukeyi da Ummey, har Junainah na cewa wai ai duk munfi sonki”.
Dariyar jin daɗi tayi tare da cewa.
“Ayyah ƴar ƙanwaliya tawa mai kishidani”.
Murmushi sukayi baki ɗaya kana Lado ya kalleta tare da cewa.
“Shiga gida mu zamu wuce masallaci ne”.
To tace kana ta nufi cikin gida tana cewa.
“Yauwa yaya Giɗi dan Allah a kawomin rake”.
Kai ya gyaɗa mata kana suka wuce ita tayi cikin gida.

Tana shiga da fara’ar jin daɗi da ɗan karfi ta buɗe murya tare da cewa.
“Assalamu alaikum, gani na dawo, ina Inna ina Ummey, Junainah ina kike?”.
Ai kusan a tare suka fito gaba ɗayansu, wani irin tsalle Junainah ta buga tare da rugawa ta nufi kan yayar tata cikin ihu da ɗaga sauti take cewa.
“Oyoyo Addana oyoyo”.
Da sauri Ummey ta harateta tare da cewa.
“Ke Junainah magriba cefa, kike irin wannan ihu ke sam baki da nitsuwa”.
Ita dai batama jitaba.
Da gudu ta faɗa jikin Aysha, itama Aysha wurgar da jakarta tayi ta ruggume yar uwarta.

Inna da Ummey kam ido suka zuba musu, suna masu jin daɗi irin soyayya da shaƙuwar dake tsakanin yaran nasu.

Dariya sukayi baki ɗayansu, cikin jin daɗi inna tace.
“To yanzu dai lokacin salla yayi ku shigo kuyi salla tukun sai ayita murna dan yau dai kam nasan kwanan zaune za’ayi”.
Murmushi Shatu tayi tare da karasowa gabansu cikin ladabi ba biyayya tace.
“Inna ina wuni”.
Fuska a sake tace.
“Lfy lau Alhamdulillah ya karatu”.

“Alhamdulillah karatu dai mun samu ɗan hutu.”

“Masha ALLAH yayi kyau”.
cewar Ummey
hannun Ummeyn ta kamo tare da cewa.
“Ummey ina wuni”.
Murmushi tayi tare da shafa kekyawar fuskarta tace.
“Lfy lau Shatu muje muyi salla ko?”.
Kanta ta ɗan sosa tare da cewa.
“Ummey ni nayi sallana a mota”.
Dariya Ummey tayi domin ta gano cewa Shatu na fashin salla,
Ita kuwa Junainah baki ta tura tare da cewa.
“To ba gashi ba, ba yanzu muka gama musuba ya Giɗi ba nace mishi nafi Addana son salla, tunda ni kullum sai nayi ita kuma wata rana sai tace a a ita tayi a makka ko kuma tace wai ai tayi kuma babu wanda zai ganta tanayin sallan”.
Ummey ce ta.
Buge bakinta tare da cewa.
“To Aku uwar mgna maza wuce kiyi salla, babu wanda ke son jawabin ki”.
Tura baki tayi kana ta wuce cikin ɗakin nasu, tana cewa.
“Ai dama nasan kunfi sonta”.
Ita kuwa Ummey harara ta watsawa Shatu tare da cewa.
“Ke kuma kada dai ki rinƙa kiyaye bakin wannan magananniyar”.
Murmushi tayi ta bita kana ta ɗauki buta ta shiga bayan gida dan gyara jikinta, sannan ta dawo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button