GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Basubi ta kanshi ba duk suka meda hankalinsu kan Parvina da tsuntsuwar dan ganin ƙasan tsuntsuwar Bolerun yana zubda jini, wannan abun ya sasu cikin nazari to, amman sai mgnar Parvina ta katse musu nazarin da cewa.
“Allah sarki gashi sunji mata ciwo har sun fidda mata jini”.
Jin haka yasa suka sa a ransu yess jinin ne daya fita sanadin jin ciwo,
cikin kula Arɗo Babayo ya matso parvina da taketa shafa kan tsuntsuwar da suke gani a idanunsu a hankali ya kamo hannunta cikin lallashi yace.
“Parvina muje cikin gida ko, kinga dare yayi kiyi salla kici abinci, tsuntsuwar taki kuma ki saketa zata fire ta hau makwancinta”.
Da sauri ta fara jujjuya mishi kai hawaye na zuba tace.
“Baffa Arɗo ta fire kuma? Bata da fiffigefa mutunce fa,tare zamu kwana da ita wallahi ba tsunstsuwar bace, mutunce ku daina ce mata tsuntsuwa, karmu barta ta kwana a woje”.
Sai ta kuma kama fiffigen tsunstsuwar tace.
“Ga hannunta nan sun karya mata”.
Sai ta kuma kama ƙafafun tsuntsuwar tace.
“Baffa Arɗo kaga ga sawunta ga idonta tanata zubda hawaye ga cikinta ga kunnenta ga bakinta ga gashin kanta har bayanta”.
Kallon-kallon suka tsaya sunayiwa junansu,
domin kafiyar parvina kan cewa Wannan tsuntsuwar Boleru mutun ce bani Adam ce ya fara basu tsoro to ko dai ƴarinyar tayi gamone? Koko tsuntsuwar iskace?.
cikin tsoron daya fara rufe Appa baki na rawa ya kamo hannun ɗiyar tashi da yake masifar so tamkar ƙoƙon ranshi cikin kaɗuwa da muryar fillanci kasan cewar sam fulanin ƙasar Cameroon basa jin hausa koda kawo min wuƙa in kashekane shiyasa cikin fillanci yace.
“(Parvina tsonɗu on fa na ɗum innu adamajo, ko waɗi a vi’ata neɗɗo on) parvina tsuntsuwace fa ba mutun bace meyasa kicewa mutunce?”.
Kuka ta kuma fashewa dashi harda shessheƙan gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi ganin yadda jikin matar ke karkarwa. Ruggume tsuntsuwar kurciyar tayi a ganinsu yayinda ita kuwa cikekkiyar kamilar mace take gani hannunta matar ta kama ta juya ta nufi cikin gidansu dansu da Gainako suka shiga tana kukan shur-shur da hawayenta.

Zurui sukayi suka rakata da ido har ta ɓacewa ganinsu.

A mashigar gidan sukayi kiciɓis dasu Giɗaɗo da sauri ta koma gefe.
Shi kuwa Giɗaɗo wani irin dundu ya kima mata a tsakiyar bayanta tare watsa mata harare cikin fillanci yace.
“Hegiya muguwa wallahi sai na yanka tsuntsuwata muna fuka”. da sauri tasa jikinta ta kare tsuntsuwar, tare dayin sauri tayi cikin gida.
Seyoji ta samu tsaye gefen mamansu yana bata labarin tsuntsuwar da duk gidansu babu wanda bai san Giɗaɗo da itaba dan yanzu kimanin watanni takwas kenan kullum babu dare babu rana a nan gidan nasu tsuntsuwar take rayuwa kullum in Giɗaɗo yaci abinci ya rage inta kuma sai tazo tayi ta tsastsaga har sai tacinye duk abincin daya bari kana ya ajiye mata madarar shanu nanma tazo tasha,
idan tasha ta ƙoshine sai ta juya da tafiya take barin cikin gidan ta koma bakin kogi.

Da sauri Mamansu Giɗaɗo ta kalli Parvina tare da cewa.
“Parvina na zo nan zo keda tsuntsuwar ki kada ki damu babu mai yankata”.
Da sauri ta iso gaban matar tare da cewa.
“Inna ki hanasu yankata Allah kuwa ba tsunstsuwa bace mutunce”.
Cikin kula matar tace.
“To parvina kada ki damu babu mai yankata daga yau ta zama taki, yanzu ajiyeta kije kiyi al’wala kizo kiyi sallah”.
Da sauri tace.
“To”.
A jiye matar tayi bisa taburmar dake tsakiyar gidan, kana taje tayi al’wala tazo ta shimfiɗa sallaya a gefenta, itama Inna gefenta ta shimfiɗa suka sa baiwar Allah’n nan a tsakiya…

Kamar da wasa da abin ya girmama domin koda sukayi salla isha’i fir parvina taƙi ta rabu da tsuntsuwar nan.
Su kuwa su Arɗo Babayo sun mance batun tsuntsuwar ma, tunda sukayi sallan isha sukaci abinci.
Suketa lissafin kan dabobbinsu kama daga kan Raƙuma, Dawakai, shanu, tumaki, raguna, awaki, ɗawisu, tolo-tolo, zabbi, tattabaru, saida suka waresu baki ɗaya dan sanin adadin zakkar da zasu fitar sannan suka gama fayace na zakkar kowanne daga ciki da shariya ta umarci a bada zakkanshi.

Hira sukaci gaba dayi kan abinda ya shafi kiwon nasu.

A can cikin gida kuwa, tunda Inna ta gama yiwa su Arɗo Babayo gashin zabbi ta haɗa da madarar shanu aka kai musu taketa fama da Parvina kan yadda ta tasa tsuntsuwar nan a gaba tana mata magiya kan tasa hannunta taci abinci,
ganin bazata iya ci da hannun nata bane yasa iya tasa hannun tana bata abinci har baki tana amsa tanaci yayinda hawaye keta kwaranya a fuskarta babu ƙaƙƙautawa.

Koda taci ya isheta sai ta mirgina alamun zata konta.
Ganin hakan yasa parvina kallon inna cikin sanyinta da nitsuwarta tace.
“Inna tare zamu kwana da ita”.
Kai inna ta jinjina mata kana ta miƙe tace muje cikin ɗakin kinga gari yayi sanyi Giɗaɗo da kike tsoron kada kiyi bacci yazo ya ɗauke tsuntsuwar ma yayi bacci”.
Kai ta gyaɗa kana ta miƙe suka shiga cikin ɗakin,
bisa katifar gado huts ɗinnan ta zauna tare da tsuntsuwar a gefenta, yayinda ga hasken wutan da aka kunna janareta ya gauraye ko ina na gidan da kuma ɗakin.

Inna kuwa kan gadonta take,
suna ɗan hira,
yayinda sam hankali parvina kan tsuntsuwar nan yake.
Tashi zaune tayi lokacin da taga gaba ɗaya jikin matar nan yana ta karkarwan ga hannunta dasu Gainako suka karya ya kumbura simtin, hannunta mai lafiyan kuma ta ɗaurashi kan tirtsetsen cikinta, gaba ɗaya jikinta zufane keta tsastsafowa tako ina,
cikin tausayawa parvina tace.
“Sannu hannunkin ke ciwo ko? Kiyi haƙuri gobe da safe zamu kaiki gidan mai magani”.
Inna ce ta zubawa Parvina ido cikin yanayin tsoro tace.
“(Parvina ɗun sonɗufa) Parvina tsuntsuwace fa. ki dena magana da ita ba jinki takeyi ba”.
Da sauri ta jujjuya kanta hawaye na zubo mata tace.
“Inna Wallahi tallahi mutunce ku dena ce mata tsuntsuwa inna ki ganifa bata da lfy, jikinta duk rawa yakeyi”.
Kai Inna ta gyaɗa kana tace.
“To na yarda yanzu dai ki kwanta kiyi bacci sai gobe da safe zamu kaita gidan mai gyaran karaya da targade”.
Jin hakane yasa ta konta tare da lumshe idonta. Sai bacci ya fara saceta sai kuma tayi firgigit ta farka,
ta kuma tada Inna sabida, suntsuwar nan ta kasa nutsuwa, yayinda ita kuwa Parvina take ganin baiwar Allah’n cikin mawuyacin halinda ya rintane yasa bata gane cewa matarnan naƙuda takeyi ba.

A haka suka kwana, har garin Allah ya waye basuyi bacciba, sabida ita kanta inna yanzu tsoron tsuntsuwar ta fara haka kuma take tsoron parvina, ita kuwa baiwar Allah’n nan zafin ciwon naƙudane ya hanata bacci ita kuwa parvina tausayin matar da mutanen garin da gidan ke cewa tsuntsuwar Boleru ne ya hanata bacci.

Asuban fari suka tayi sukayi salla,
daga nan suka fito tsakiyar gida, kai tsaye sashin Arɗo Babayo suka nufa ita da Inna,
shiru sashin nashi alamun basu dawo masallaci ba, cikin alhini da tsoro Inna ta kalli Parvina cikin daburtacciyar murya tace.
“Ajiye tsuntsuwar nan haka kina rike da ita kamar kin samu uwarki maza ajiyeta”.
Cikin zubda hawaye ta tsuguna ta ajiye tsuntsuwar kan buzun Arɗo Babayo,
Wanda dai-dai lokacin ne kuma Arɗo Babayo da Appa, Gainako, Seyoji, Buba, Giɗaɗo, Ja’eh suka shigo kamar yadda suka saba.
Cikin mamaki suka zubawa tsuntsuwar Kurciyar nan ido ganin yadda taketa birgima a kan buzun tana wasu irin cure-cure tamkar ranta zai bar jikinta.
Ita kuwa Parvina kuka ta farayi bil haƙƙi da gskya tanayi tana yarfa hannu,
Buba ne yayi maza ya nufi kan tsuntsuwar kurciyar tare da cewa.
“Haukan banza a kan buzun salan Arɗo zaku ajiye tsuntsuwar.
Ihu mai ƙarfi parvina tasa ganin Buba ya ɗaga kafarshi da ƙarfin bala’i zai kaiwa tsuntsuwar harbi da naushin ƙafarsa,
Kamar a mafarki kamar gilmawar walƙiya tamkar daga sama.
Sukaga tsuntsuwar Kurciyar nan tayi wani irin ɗagowa ta karkaɗa fikafikinta cikin ƙudurar Ubangiji da hikimarsa da buwayarsa sai gata-ta d…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button