GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Tura baki tai tare da cewa.
“Izinin wa?”.
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“Ok haka kikace ko baki san izinin wanda zaki nema bama kenan ko?.”
A hankali ta ɗan kalleshi sai kuma tace.
“Kayi haƙuri. Ina son yin azumin, ka amince inyi?.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Uhuumm ai da kinyi ba neman izinin sai da yamma in karyashi”.
A hankali tace.
“Ka karya min shi kuma ɗura zakayi min ne?”.
Kanshi ya kauda tare da cewa.
“Aikin wani ladan zanyi dai in Kauda naki da nawan, Ni na samu lada biyu na niyan azumin da ladan raya Sunnah”.
Shiru tayi tana jin yadda yake murza yatsarshi ma nuniya cikin tafin hannunta.
Ganin lokacin sahur na tafiya ne yace.
“To tashi kije kiyi sahur”.
Miƙewa tayi ta fita.

Shi kuwa sahur ɗin ya fara.

To Alhamdulillah Azumin Arfa dai yayi zafi sosai kowa ka gani kamar yayi azumi goma.

Kuma yaune Lamiɗo ya ware raguna aka bada duk cikin masarautar Joɗa ahilinshi da bayinshi da hadimai kowa da ragonsa.

Sheykh Jabeer kuwa shima yasa su Jalal sunje sun raba a cikin gari sadaka.

Da yamma suna zaune Aunty Juwairiyya ta shigo gefen Ummi ta zauna.
Ita kuwa Aysha tana kwance bisa kujera kamar sumemmiya. Azaban ƙishirwa da yunwa ne suka dabaibaye kuzarinta.

Cikin sanyi Aunty Juwairiyya tace.
“Aunty Aysha sannu fa, Azumin da daɗi kam yau”.
A gyatsine ta kalli Aunty Juwairiyya, sabida zuwa yanzu zarginta da takeyi yamafi na baya.

Ummi ce ta ɗan kauda zancen da cewa.
“Ya shirye-shiryen aiyu kam salla”.

Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
“Alhamdulillah Ummi wannan karon ai aiyukan zasu zo mana da sauƙin.
Dan nan za’a kawo ragunan Jamil da Jalal Amarya ta gyara musu.”

Ni inji dana Ya Jafar da nawa dana Hajia Mama”.

Cikin murmushin Ummi tace.
“A a kada ki mana wayo kinada masu tayaki aiki ga Ladi da Lami duk zasu tayaki.”

“Ummi kuma ga Saratu ga Larai gaki ga Aunty Aysha”.
Cewar Aunty Juwairiyya.

“Duk da haka aikin da yawafa anan ga na Sheykh ga na Mamey ga ganawa gana Aysha kana ga na Jalal Jamil. Kuma suma su Saratu sunada aikin nasu.”

A hankali Aysha ta miƙe zaune tare da cewa.
“Ummi aiki ai ba abin tsoro bane, ba damuwa”.

Tana faɗin haka ta juya ta nufi ɗakinta.
Tazo gab da bakin ƙofar shiga falonta kenan taga wani irin duhu ya rufe mata ido sai jiri da sauri ta zauna.

Sheykh kuwa da yayi al’walan la’asar zai fitone ya ɗan zuba mata ido tare da cewa.
“A azumi ɗayan ne kike neman faɗuwa zaki sune min ko”.
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
“Azumin fa da zafi Sheykh”.

Kanshi ya ɗan juyo tare da cewa.
“Kaiya Ummi ragwanci dai”.
Murmushi sukayi ya wuce ya fita.
Ita kuma da ido tabi bayanshi ƙeyarshi ta liƙawa wani mayataccen kallo.
Kana ta miƙa tsaye ta nufi ɗakinta.

Ummi kuwa cikin gyara zama tace.
“Gsky Juwairiyya aikin nasu Jamil ayishi a sashinki.
Kinfa San na Sheykh ma biyu ne”.
Dariya Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
“Kai Ummi to shi Sheykh ba a ana tashi sallan idi a wurin ake yanka nashiba, tunda shine liman baza’ayi layya ba sai yayi.
Yanayi kuma a wurin ake rabashi sadaka.
Daga nan kowa ya dawo gida yayi nashi”.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Eh to ai akwai wanda Lamiɗo ke bashi kuma za’a kawoshi nan”.

Miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
“To shike nan Ummi a bar na Jamil tunda shi zaima je ya tayamu aikin ku ku gyara na Jalal”.

“To shike nan”. tace kana suka tafi salla.

Bayan sun idarne suka fito suka fara aikin buɗa baki.

Bayan sunsha ruwa sun hutane.
Suka shiga kitchen kimtsa kayan aikin da aka lodo musu sukayi.
Kana suka ɗan haɗa aikin da zai iya faruwa a lokacin.

Washe gari aka tashi ranar Sallan layya.
Yara da manya mata da maza al’ummar Annabi na duniya baki ɗaya anata shiryawa zuwa idi.

Babu wanda ya tsaya karyawa sabida duk suna azumi.
Wanda sai bayan an sauƙo idi anyi yanka mai layya yayi buɗa baki da hantar dabbarsa.

Sauri-sauri yake kimtsawa cikin wata kekyawar al’kyabbar mai taushi baƙa sai farar jallabiya da yasa a ciki.
Hiraminshi ya kimtsa kana ya fisa turare.

Sannan ya fito da sauri ganin lokacin nata gaba towa.

A falo ya samu Ya Jafar. Tare suka fito babban falon.
Nan suka samu su Ya Hashim, Jalal, Jamil, Imarn, Affan, Sulaiman. Da sai sauransu.

Nan suka rakaya suka nufi masallacin Masarautar Joɗa inda nan yake limancin Sallah idi.

Masallacin da ƙaton filin harabar masallacin duk ya cika yayi maƙil tako ina al’ummar Annabi ne keta shigowa.
Cikin shiga mai kyau ta al’farma da tsabtar addini.

Ita kuwa Aysha a hankali take kimtsawa sabida ciwon da mararta keyi.
cikin sanyi ta buɗe wodurob ɗinta.

Wani tattausan Boyel mai taushi da sheƙi mai ɗan karen kwai ta zaro, dinkin zani da rigace borno sitayel mai masifar kyau.
Kalarshi Sky blue an watsa mishi aiki da zare Pink color mai sheƙi.

Bayan tasa bra and pant wani tattausan ondawuya dan guntu iya guiwa tasa, kana tasa.
Ɗaura zanin ta dai-dai-ta shi.
Rigar ta zura a jikinta tayi mata cib-cib gwanin burgewa ƙirjinta ya zauna daɓas.

Ninke ɗan kwalin tayi tare, murza asetta ta ɗan karkatashi kaɗan jelan gashinta da bata kitseshi ba, ta barshi kwance a bayanta.
Turare mai masifar ƙamshi ta fesa.

Sannan tasa wani sarka da yan kunne masu kyau.

Gyale pink color ta yafa.

A hankali ta fito falo.
kiciɓis sukayi da Ummi tana cewa.
“Aysha mu tafi ko”.
A hankali tace.
“Ummi kuje kawai. Bazan jeba”.

Ɗan jim Ummi tayi sai kuma ta juya kawai ta tafi.

Ita kuwa Aysha kitchen ta nufa.

“Special Arish”. tace a hankali kana ta.
Ɗebo dankali da sauran kayan da zata buƙata

SPECIAL ARISH
1.dankalin turawa
2.nama, kwai, tumatur
3.kabeji, bama , maggi
4.tafarnuwa ,man gyada.
Da farko dankalinki ta fara ferewa ba tare da daddatsashiba ta wanke saita-ta tafasashi da ruwa da gishiri kadan.
Sai ta kada kwai da albasa d curry da Maggi Tafarnuwa.
Daga nan saita dinga tsoma dankalin tana soyawa.
Sai ta kuma tafasa nama da maggi da gishiri da curry da tafarnuwa da al’basa har yayi laushi saida ruwan ya kusa tsotsewa saita kara wata al’basa da timatur suka nuna saita kwashe.

Ta yanyanka kabeji kanana sannan ta dafa kwai ta yanyan kasa da. Dan girma sannan ta zuba Maggi da bama ta gaura yeshi .
Sai ta samu Foodflaks ta zuba Irish a gefe sannan hadin namanki ta shina ta sashi a wani kulan shi kuma haɗin kabejinki ta sashi a wani kulan shima

Kasan cewar da yawa ta ɗan yi shi.
Tana gamawa taje ta jerashi a kan Dinning area.
Sannan tazo ta kimtsa wurin.

Tuni kuma an idar da salla.

Affan dake kusa da Sheykh ne ya ɗan matso tare da cewa.
“Hamma Jabeer gacan ragon an kawo mutane nata son tafiya gida suna jiran kayi yankan.”
Da sauri yajuya tare da cewa.
“To muje”.

Bayan yayi yankanne ya juya ya tafi.
Yasan na cikin gidanma duk shi ake jira.

Affan kuwa a gefen wurin ya tsaya saida aka gama fiɗan dogarin dake raba naman ya yanko hantan yasa a leda ya miƙawa Affan.
Daga nan Affan ya juya ya tafi cikin gida shi kuma yayi ta rabawa mutanen wurin naman.

Yayinda duk sauran mutane gari kuwa aketa tafiya.

A can mayankansu na cikin Masarautar Joɗa nan Sheykh ya nufa shida Lamiɗo da sauran manyan masarautar baki ɗayansu.

Daga nan ya fara yanka bayi masu fiɗa suna amsa suna feɗewa ko wanne ana kaishi sashin maishi.

Affan kuwa kai tsaye Side ɗin Sheykh ya nufa.

A falo ya samu Ummi da Aysha,
ledan hantar ya miƙa mata tare da cewa.
“Gashi a gasawa Dr Liman Sheykh Akarmakallu Hamma Jabeer kafin ya dawo.
Yanacan yanata yanka zai dawo a gajiye a yunwace”.
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
“Gsky kam Aysha amshi ki fara da wuri”.
To tace kana ta amshi ledar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button