GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A can kasa mai tsarki kuma,
Sheykh ne zaune a gaban Sitti, kana Haroon da Jannart na gefenshi Sheykh Aliyu Abdulkareem, kuma da Sheykh Jabeer Aliyu da wasu manyan malamai na zuriyar tasu duk suna zaune a cikin falon.
Jazrah kuma na gabanshi da wani tray mai masifar kyau da tsada.
Madara da zuma take zuba mishi a cikin wasu ƴan kananun kofuna masu masifar kyau da ɗaukan hankali.

Wannan ya kasance al’adarsuce ta baiyana nuna yarda da soyayya ko akasinshi, indan ana son a haɗa yara aure, to za’a tattauna tsakanin manya, bayan sun gama dai-dai-ta magana tsakaninsu kamar yadda yanzu su Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen, da kuma su Sheykh Jabeer Aliyu da babban babansu Sheykh Aliyu Abdulkareem da kuma Sitti suka gama haɗa zancen auren Jazrah da Sheykh Jabeer, to yanzu ta zuba mishi madara da zuma a gaban kowa, ta ajiye mishi, idan ya ɗauki kofin madara to yana nufin yana sonta ya kuma amince da ita da aurenta.
In kuma ya ɗauki kofin zuma, to yana nufin ya tsaneta baya kuma sonta bazai kuma auretaba bare ya zauna da ita.
Za’ayi komai a gaban manya ne, don suga zahiri kuma a tsarin ko ɗan uwanka zai iya yi maka zaɓin da kuma in dai am zaɓa maka sai ka aura.

Shiru sukayi baki ɗayansu falon, kowa da tunanin da yakeyi.

Sheykh Jabeer dake zaune a tsakiyarsu cikin shiga ta al’farma sai sheƙi al’kyabbar sa keyi, ga tattausan hirami a kanshi, ido ya lumshe daya gane manufarsu.
“Domin shi basu gaya mishi cewa, zasuyi wannan abun bane daya sani wallahi da yasan duk yadda zaiyi ya gudu, ya tafi harami, har sai sun gaji sun watse.
A hankali ya kalli Sitti dake kallonshi cikin rauni da alamun.
“Dan Allah kada kace, a a yar ɗan uwanane, kada ka bamu kunya nida kakanninka maza yar uwarkace kasan tarbiyarta”.
Kauda idonshi yayi daga kallon Sitti, wani irin kallo yayiwa Haroon daketa yi mishi, murmushin muguntan yau dai an titseka baka da hanyar tsira.
Cikin ranshi yake mgnar zuciya.
“Ta yaya zan amince ince zan aureta? Dame zan zauna da ita?”.
Sai kuma ya ɗan fidda nannauyan numfashi.
“To idan ban amince da aurentaba me zamcewa, waɗanannan bayin Allah’n da sukayi min dukkan gatan duniya, na zauna a gidansu tsawon shekaru masu yawa nayi karatuna har na gama, sukemin komai na rayuwa, suna nuna min soyayyar da mahaifinama baya nuna min, da wanne idon zan kallesu inna ɗauki zuma alamar na tsani yarsu?”.
A hankali ya buɗe idonsa, jin muryar. Sheykh Aliyu Abdulkareem kakan Mamanshi kenan, baban kakarshi Sitti dottijon daya yake sonshi tamkar ranshi yana cewa.
“Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, kayi zaɓin da ranka keso, bamu da nufin yi maka dole, sai dai ina da burin aurar maka jikata Jazrah ɗiyar mai sunanka. Ina so da fatan ganin nasabarka ta cika, cikar nasabarka kuwa, shene aure.”
Wani irin sassanyan numfashi ya shaƙa a hankali, wasu irin zafafan tunanuka ne ke zirya a zuciyarshi”.
Cikin harshen hausar katsinawa, Haroon yayi mgna can ƙasa yadda ko Sitti bazata jisuba.
“Sheykh kafa, shanyamu, nifa zan ɗaukar maka Madara”.
Ido ya lumshe tare da ɗan jingina da jikin kujerar da yake zaune, wanda yake kusa da Sheykh Abdulkareem.
Sitti ce ta ɗan kalli Haroon tare da mishi alamun ya taɓo Sheykh.
cikin harshen larabci Haroon ya kalli kakar tasu, tare da cewa.
“Sitti ai nasan zaɓinsa, bari ki gani in nuna miki”.
Ya ƙarishe mgnar yana kai hannunshi kan kofunan.
da sauri Sheykh Jabeer ya buɗe kekkyawar ƙwayar idanunshi da wasu ke kiransu da zaiba, wato kamar idon mage, idon ya ɗan zaro ganin Haroon yasa hannunshi kan kofin M…!

????????????????????

Masu cewa na kulle musu kai kada ku damu zan kuce kawunanne, lokaci ne????????????????????

                            By
               *GARKUWAR FULANI*

????????????????????????????????????????????

????????️????????????????????????

             *GARKUWA*

                    PAGE 12

                            NA
              *AYSHA ALIYU GARKUWA*

                 ????????????????????????????????

Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku ta wannan number 09097853276. KO kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz domin samun shiga Special Group, wanda cikin kwanaki ƙalilan za’a gama littafin da izinin ubangiji. Ga asusun kamar haka 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, 1k ne SPG sai ki turo min shaidar biyan
ki ta wannan number 09097853276.

Gareku iyayen ƴan mata da za’a aurar, akwai sittin amare mai kyau na gyaran jiki, bisa farashi mai sauƙin, akwai na manyan robobi akwai na ƙananan robobi, akwai haɗin masu jego, da na maida tsohuwa yarinya, sayan na gari meda kuɗi gida, in kayan gyaran kikeso ki fara min text message ta inbox ta wannan number 09097853276 sai ki gaya min kaya kikeso, kana sai ki kirani to nan zan ɗaga kirankin sai muyi mgn zaki turo kuɗi ta ACCOUNT number ni kuma zan tura miki kaya ta mota, duk garin da kike a Nigeria ina aikawa, in dai ba lungu yayi sosaiba. Kana mutanenmu mazauna ƙasashen ƙetare kamarsu Saudia, India, Gabon, Ghana, Niger, Cameroon, da dai sauransu in kinada dalili kayana na zuwa can cikin salama. Ina saida kaɗan-kaɗan ina kuma bada sari.

A dai-dai kan kofin madarar ya sa hannunsa, alamum zai mishi zaɓi kenan, murmushi yayi dan ya samu damar, da zai tserewa tsarinsu. Cikin ihima da sanin makaman kariyar kai daga jin kunya ko yin abinda zai ɓata ran wani, ƙafarshi ta dama dake kusa da hannun Haroon yasa cikin hikima ya bugi hannun Haroon da ke gab da ɗaukar kofin.
ture hannun yayi da babbar yatsarsa, wanda, hakan yasa hannun Haroon ya bugi kofunan da ɗan karfi, sai gashi duk sun tuntsure a tsakiyar tiren madarar da zumar kab suka malale cikin tray ɗin.
A tare suka zubawa tray idanu gaba ɗayansu.
Sitti kuwa wani irin kallo tabi Madarar dashi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin iya taku da kamalarsa murya a mutunce ya kalli Haroon daya kafeshi da idon tuhuma, cikin harshen larabci da kamala yace.
“Harooon meyasa baka da nitsuwa?”.
Cikin tarin mamaki Haroon ya gwalo ido tare da cewa.
“Haaahh”.
sai kuma ya kalli Sitti da ta kwaɓe fuska tamkar zata kurma ihun takaici.
Shi kuwa Sheykh Jazrah ya zubawa ido, ganin yadda ta zuba mishi kekkyawan idanunta, wanda suke sheƙin hawayen dake nuni da zazzafan son da takeyi mishi.
Kauda kwayar idanunshi yayi, da sauri.
Jannart kuwa hannun Sitti ta kamo ganin zata jawo tray.
A hankali Sheykh Khalillullah wanda yake ƙanin Sitti ya gyara zama cikin sakin fuska da murmushi ya kalli jikan nasu, nitse yace.
“Laaba’as”. Dib-dib haka ƙirjin Sheykh Jabeer Habeebullah ya fara bada sauti, fahimtar kakanun nashi zasu ɗaura zabin kan, fahimtar lafazin Haroon.
Shi kuwa Haroon, wani irin murmushi jin daɗi yayi.
Shi kuwa dottijon nan, ido ya zubawa ƴaƴanshi da jikokin ƴaƴan nashi, da wasu jikokinshi. Kallonsu yake yana nazartansu.

A hankali wayar Sheykh Jabeer ta fara bada wani sauti mai masifar sanyi da daɗin sauraro, sautin gwauraye yake da kukan sassanyan tsuntsaye.
da sauri ya zaro wayar a al’jihun tattausan al’kyabbar tasa.
Ganin sunan Maimartaba Nuruddeen ne, ya sashi sakin wata sassanyan ajiyan, cikin ladab ya kalli Sitti, kana a hankali ya kalli Sheykh Abdulkareem, cikin sanyi da nitsuwa yace.
“Mai martaba Nuruddee ke kirana, bisa alamu da babbar mgna domin baya kirana haka banza”.
Murmushi dottijon yayi, domin ya fahimci hanyar fecewa, Sheykh yake nema, hakan yasa ya mishi izinin tafiya.
Cikin sauri Sitti ta yunƙuro da niyar yin mgna, sai kuma tayi shiru, sabida nuni da tayi shirun da mahaifinta yayi mata.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya yunƙara, ya miƙe ya nufi hanyar fita bayan yayi musu, su huta gajiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button