GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Aunty Kubra kuwa suna shiga ɗakin.
Ta jawo wani matsakaicin akwati.
wasu zafafan ɗinkuna ta fara fitarwa. Ko wanne da mayafinshi da takalminshi da jaka ko fosa.
Shigowar Aunty Hafsat ce yasa tace.
“Yauwa Hafsat Ni ina anko ɗin su na ƙawaye da a abokai wanda za’asa a kamun.
Zama tayi gefenta tare da cewa.
“Gashi nan gefenki ɗazu aka dawo dasu daga ɗinki.
Harda na Farida shine fa tun ɗazu ta buwayeni da kira kadafa a manceta”.
Jawo ledar tayi ta firfito dasu, kowa da sunanshi a jikin nashi, shiyasa babu wuyan ganewa.

Kala shida Aunty Kubra ta miƙawa Aysha tare da cewa.
“Gashi dana kamu dana walima dana Dina na wuni, ne a nan sai waɗannan kuma kyasasu sanda kikeso”.
Aunty Hafsat ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
“Dinar dai mijinta ya hana, gacan Haroon kamar yayi kuka, Jazlaan kuwa ya gama karya zancen a wurin Abban su Haroon ɗin”.
Dariya sukayi kana Hibba tace.
“Aunty Aysha zo muje ɗakina, ki gani nida Azeema ce kaɗai a can”.
Da sauri ta miƙe da tana jin nauyin sun Aunty Hafsat.

Suna shiga ta zauna bakin gadon Hibba tare da cewa.
“Iye ashe dai my Hibba ba dama wurin tsabta”.
Murmushi Hibba tayi cike da jin daɗin yaba mata da Aysha tayi.
Ita ko Aysha numfashin gajiya ta sauƙe tare da cewa.
“Yanzu bari inyi wonka wlh na gaji”.
Azeema da yanzu ta shigo ne riƙe da ƙaramin yaron Aunty Safiyya wacce itace ƴar farin Aunty Hafsat kuma itace matar Ibrahim.
Yaron bai wuce shekara Uku bane.
Tace.
“My Aunty kamar tafiyar mota kikayi”.
Hannu tasa ta amshi yaron tare da cewa.
“Masha Allah yaron waye wannan mai kama da Jalal”.
Hibba ce ta ɗan shafo kansa tare da cewa.
“Aunty Aysha kice kawai mai kama da Hamma Jabeer ko”.
Yi tayi kamar bataji Hibba ba.
Azeema kuwa cewa tayi.
“Yaron Aunty Safiyya ce, kin santa ko”.
Kai ta jujjuya alamar a a.
Da sauri Hibba tace.
“Itace matar Ya Ibrahim ƙanin Aunty Juwairiyya”.
Murmushi ta ɗan yi tare da cewa.
“Ok na gane masha ALLAH”.
Tace tana sumbatar goshin yaron.
juyowa suka ɗanyi jin motsin buɗe ƙofa da kukan yaro.
Safiyya ce ta shigo mai kama da Azeema sak.
murmushi Safiyya tayi tare da cewa.
“Iye Aunty Aysha kice kin gane Angon naki kenan”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Angona kuma”.
Azeema ce tace.
“Eh ai mai sunan Hamma Jabeer ne.”
Kai ta ɗan sunkuyar ta kalli yaron tare da cewa.
“Eyeh kai mun gode kuwa”.
Kallonta Safiyya tayi cikin sakin fuska.
gyara riƙon da tayiwa ƙaramin ɗanta, Salim tana bashi nono tace.
“Yanzu muka dawo kasuwa akace min kun iso ko ruwa ban shaba.
Azeema kawo min abinci tun safe muna kasuwa”.
Da sauri Azeema ta miƙa taje ta kawo musu abinci.
Bayan ta zubane tace.
“Aunty Aysha sauƙa kuci kema bakici komaiba tunda kukazo”.
Zatace a a .
Safiyya tace.
“A a dan Allah kada muyi haka dake sauƙo muci, Ni fa yar uwarkice kuma matar abokin wasanku kinsan ɗan kawuna aka auramin, ni matar abokin mijinki ne kuma Aminiyarki sannan ƙawar mijinki”.
Dole Aysha ta sauƙo sukaci abinci tare.

Sannan ta miƙa taje tayi wonka.
Tana fitowa Hibba na shigowa da jakar data amso a wurin Ummi a can ɗakin dasu Aunty Kubra suke.

Fita sukayi Safiyya kuma ta shiga Bathroom ɗin.
Nan ta samu ta kimtsa.

Wani Shadda lace red color sai ratsin white blue a jiki wanda kamar zanen bakan gizo ta saka doguwar rigace
Ta zauna a jikinta ras, tayi masifar kyau, bata wani yi kolliyar azo a ganiba.
Gyalen shi farine ta yafa, bayan ta murza ɗaurin ɗan kwalinta.

Turarenta mai ƙamshi ta fesa.
Kana ta ninke kayan data ciren.
Da sauri Hibba da yanzu ta shigo ta amshisu tace.
“Yauwa bari in kai a wonkesu agoge kadama su tarun miki.”
“To”. tace, kana ta maida marfin jakarta ta rufe.
Safiyyah na fitowa ta kimtsa itama nan suka zauna suna hira har dai aka kira sallan magriba.
Bayan anyi magriba anyi ishane.
Duk suka fito babban falon.
Sai Umaymah dake can cikin ƙawayenta da matan abokan Abbansu HAROON.

ita kuwa Aunty Hafsat ta Tara zuriyarsu kab sunata hira.

Suna tsara tafiyarsu da za’ayi gobe jumma’a da hantsi, zuwa Leddi julɓe.
Da yamma ayi kamu jibi a asabar ɗaura aure da hantsi sannan su dawo da amarya da daren ranar kuwa ayi walimar washe gari Lahadi kuma ranar wuni ce ayi fansan ido da yamma, da dare kuma ayi shagalin mother’s day.
Duk yadda sukaso ayi bidi’a da yawa, Sheykh ya karya musu logo daya samu Ibrahim da Abbansu Haroon da kawunshi Baban Aunty Juwairiyya dasu Ibrahim da amarya Jannart ɗin.
Ya dai tsara yadda yaga dama a bikin.
Haroon kamar ya rinka ihu.
In ya kufula sai Sheykh ya koma gefe yana kallonsa yana taɓe mishi baki.

Shi da Ibrahim dama su sunce sai jibi zasuje asabar zasu sammaka da tawagarsu zuwa ɗaurin aure da ɗaukan amarya.

Washe gari ranar Jumma’a da hantsi jirginsu Safiyya, Hibba, Aysha, Azeema, Aunty Kubra, da wasu ƙawayen Umaymah da ƙannen baban Haroon jirgisun ya isa birnin Jalaluddin.

Sheykh kuwa shi tunda sukazo idonshi ma bai sake ganin Aysha, duk da tana ɗan faɗo mishi a rai lokaci zuwa lokaci sai dai baya bin ta kanta.

Dan hidimomin sun sha kansu.

Suna isa masarautar Jalaluddin.
Kai tsaye suka wuce Side ɗin kakarsu.
Sitti kenan wacce taketa dakon zuwansu dan ganin Aysha matar jikanta mafi soyuwa a ranta.

Suna Shuga babban falonta Safiyya ta fara kiranta.
“Sitti! Sitti!! Sittin Jadda ko dai kina can wurin tsohon zumanki ne”.
Dariya tayi ganin Sitti ta fito da sauri.
hannu ta buɗe wa Aysha irin dai al’adar su ta larabawa.
Cike daso tace.
“Iye masha ALLAH Jazlaan ya samu kekyawar mace mai nagarta”.
A kunyace fuska ɗauke da murmushi Aysha ta isa jikinta.
Ruggume ta tayi tare da cewa.
“Sannu da zuwa masarautar julɓe, jikata”.

Cikin sakin jiki da ita Aysha tace.
“Yauwa Sitti na sameku lfy?”.
Alhamdulillah tace.
Tana kallon tsohuwar da kyau tana gani wasu kamannin Ummey a fuskarta.
Jansu tayi har cikin Bedroom ɗin ta.
Duk jikokinta ne.

Safiyya ce ta zaro wayarta ta kira Aunty Rahama tace mata sun isofa.

Aunty Rahma kuwa dake tsuma Jannart da kayan gyara na al’farma Juwairiyya da Jazrah da Saddiƙa na gefenta.
Da sauri tace.
“Gani nan zuwa yanzu kuwa, Safiyya”.

Tana katse kiran tace.
“Muje Side ɗin Sittiina.
Su Safiyyah sun iso.”

A tare suka miƙa suka nufi ƙofar Sitti.

Tafiyar a kwai yar tazara tsakaninsu.

A can Side ɗin Sitti kuwa, Bayan sun zauna Sitti tasa hadimanta sun kawo musu abin ci dana sha.
Sunaci suna hira.

Ita kuwa Aysha Ishma ƴar Aunty Rahma dake bacci kan gadon Sitti ta zubawa ido.
Duk da bata ganin fuskar yarinyar gaba ɗaya amman ta hango wani irin masifeffen kama da takeyi mata da Junainah.
Shiyasa gaba ɗaya hankalinta na kan yarinyar.

Hibba ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
“Aunty Aysha kici mana, kin tsaya kallon Ishma”.
da sauri ta ɗan rusuna ta fara cin Couscous da miyar hanta da Sitti tayi musu da kanta.

Suna shigowa Aunty Rahma ta tsaya tana kallonsu cikin sakin fuska tace.
“To yau duk kamar takuma ta zama ɗaya ina surkar tawa”.
Sitti ce ta kalleta cikin son yar autar tata tace.
“Gata nan a gabanki”.
Ta ƙarashe mgnar tana nuna mata Aysha dake zaune tana fuskantar gado.
Ɗan juyowa Aysha tayi da murmushi a fuskarta.
Da sauri ta juyo gaba ɗayanta tana kallon Aunty Rahma cike da mamakin tsananin kamarta da Ummeynta, hatta muryarsu iri ɗaya.

Da sauri tayi ƙasa da kanta, jin ta zauna kusa da ita.
Cike da Muryar mamaki tace.
“Aunty Rahama ina kwana”.
“Lfy lau Alhamdulillah my surka ya ɗana, Jazlaan”.
“Alhamdulillah yana lfy”. tace fuska a sake tare da alamun kunya da kuma al’hinin abin da take gani da ji na kamanceceniyar fuska da murya.
Sitti ce tayi dariya tare da cewa.
“Tab lallai kuwa da yana kusa da kinsha tsuka, kin san baya son kina ce masa ɗanki dan yace ya fiki”.
Safiyya ce tace.
“Tab ai Hamma Jabeer baya son ace ta fishi, sai yace.
“Dan wata biyun ne wani abun”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button