GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Rugar fulanin Bani yafi ko wani yanki na Ɓadamaya sanyi mai ɗan karen daɗi.
Koda yake hakan ya samune sanadin ƙawanya da wani babban dutse mai fesar da numfashin sanyi yayi musu, wanda ya kasance musu tamkar rufar garin.
Gefen hagun Rugar Bani kuwa wani babban fadama ne mai cike da lamɓu mai ɗauke da ababen more rayuwa wanda ya kasance mallakinmu Fulanin Rugar Bani, lambun yana da duk wasu kayan marmari kamarsu.
Lemu, mangoro, gwaiba, ayaba, dabino,kwakwa, kashu, kankana, abarba, da jefi-jefin tuppa da inabi.
Wanda wannan fili yake mallakin Fulanin Rugar Bini’nne, kana bayan filin kuma akwai wani rafin da ya kasance masarrafin noman shinkafawa ne wanda suke yinshi noman rani da damina, kuma shina mallakin Fulanin Rugar Bani ne, wanda komawa yasan iya filinshi,

Daga gaban Rugar Bani kuwa kogin Shikan ne malale a gabansu iya ganin mai hange da ido biyu gefen hagunsu kuwa nan garken shanunsu ke shimfiɗe bila adadin.

Rayuwar Fulanin wannan Rugar rayuwace mai cike da aminci da amana da hakuri da kauda kai duk da tarin zalunci da kafurai ƙabulun Ɓachamawa keyi musu.

“Kamar yadda duk kowa ya sani duk duniya anyi ittifaƙin ba fulatani ko ba fulatana basa neman tsokana ko tada husuma bare tada zaune tsaye. Akan cutar da bafulatani yayi kamar bai san an cutar dashi ba ko bai ganeba, wannan dalilin yasa duk ƙabilun ƙasar Afirka sukeyiwa ƙabilarmu kallon wawaye ne ko basu san abinda sukeyiba ko sokayene, masu ƙarancin wayewa Gidadawa.
Mu kuwa a namu sashin fulani mun kasance masu kauda ido kan cutarwar forko data biyu, sai dai a haƙiƙinin gsky bama lamunta ko jurar cutarwa ta uku! Domin rama cuta ga macuci ibadace. Kuma Ba’a sarar mumini a rami ɗaya sau uku”.
Wannan shine jawabin da wani farin dottijon bafulatanin dake zaune tsakiyar al’ummar wannan rugar bayan sun dawo daga jana’izar mutun ɗaya da ƙabilun ɓachama suka kashe musu cikin sunkuru, a daren jiya wanda ya kasance ɗane ga Arɗon Yabani shugaban Rugar tasu kenan.
Hannu yasa ya share zafafan hawayenshi dake kwaranya daga ida nunshi cikin ɗaga sauti yaci gaba da cewa.
“Fulani basa ɗaukar mataki domin yaƙi ko zalumci sai dai dan kare kawunansu. Kuma kun sani duniya duk ta sani FULANI BA ƳAN TA’ADDA BANE! Ba ƴan bindiga daɗi bane, makiyayene masu ƙare rayuwarsu dan samawa mazauna cikin birane jin daɗin rayuwa, muyi kiwo mu kai musu suci naman susha madarar shanu kana muyi noma mu ciyar dasu.
Meyasa su mutanen birane basa ɗaukar matsalarmu tasu matsalar ana kashemu tamkar kiyashi kuma babu masu kulawa”.
Tsagaitawa ya ɗanyi tare da shashsheƙa cikin bada umarni a matsayinsa na shugaban Rugar uban wanda aka kashe kuma yace.
“Na roƙeku da Allah kada wanda ya ɗauki makami domin ramuwa duk da munga yankan rago akayiwa Hashimu amman bamu san wayeba kuma bamu da hujja, dan haka kada wanda yace zai ɗauki makami.
Muyi rubutu mu aikawa maimartaba sarkin Ɓadamaya, domin Al’ƙalami yafi tokobi, mu kai kukanmu gareshi, tunda shi sarkin wannan yanki na Shikan mun kai mishi kukanmu a karo na barka tai bai kulaba, kuyi hakuri mu miƙa lamarinmu ga sarakuna mu, inada yaƙinin zasuyi mana adalci”.
Shiru mutanen da aƙala sun kai ɗari da ashirin sukayi.
Yayinda kowa ya keta zubda hawaye.
Sai ɗaya daga cikine da ya kasance baƙin jakada Ɓachama ruwa biyu uwarshi ƙabilar ɓachama, wacce ubanshi bakura babarbaren borno wanda shike saida kanwa a rugartasu ya auro Uwar Ba’ana. yana naɗa komai a wayarshi,
domin miƙawa shugaban mayaƙan ƙabilar ɓachama, komai ya gani, domin shi ɗin ya kasance, makashinsu ne kuma taburmarsu ne, domin dama bahaushe yace sai da ɗan gari akanci gari da yaƙi!…

A cikin babban birnin Ɓadamaya kuwa. Land of beauty Garin Modibbo Joɗa,
Mai tutar fulɓe garinda duk arawacin ƙasar Kautal mune kaɗai muka rage da tutar Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo.
Wanda ya dasashi ya kafashi da hannunshi masarautar fulbe mai ƙarfi Masarautar Joɗa…

Cikin birnin matsarautar Joɗa.

A cikin babban birnin Ɓadamaya.
Wasu irin tsala-tsalan motocine wanda a ƙalla sun kai Goma suke jere suna fitowa daga harabar shaharerriyar makarantar Jami’a ta dake cikin babban birnin Ɓadamaya wato J.U.B Joɗa University Ɓadamaya

Yayinda suke tafiya a jere a jere cikin tsananin gudu tamkar zasu tashi sama kana ga jiniya daya karaɗe illahirin sashin wurin wanda dole yaja hankali duk wanda ke wurin gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama da titin.
Motoci huɗune a gaba, wanda suka kasance masu kyau.
Sai wata Rolls Royce, mai kuɗi kimanin naira million 4, 959,630. Motace mai tsananin sheƙi da azabar kyau motar sabuwace dal, sai sheƙi da ɗaukar ido takeyi komai na motar farine ƙal sai glass ɗinta daya kasance tin tek mai duhu.
Wani kekyawan matashine mai cikar haiba da kamala da kima, uwa uba kwarjininsa mai cika idon mutane, farine ƙal wanda da ka ganshi kasan tabbas bafulatani ne, kuma zaka gane ya haɗa jini da larabawa.
Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin yadin Super Nour a jikinsa wanda a ƙalla zai kai tamanin ɗ kuɗinshi, ya ɗaura baƙar al’kebbarsa ta jinin larabawan saudia Al’kebbar baƙace mai faɗi, kana yasa farin hirami a kanshi da zagayen baƙin saman hiramin.
Fuskarshi nan ta fito ras sajenshi mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, kana gashin girarsa ya komta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido, wani irin tsabtaceccen gemune da bazai wuce kamu ɗaya ba ne yayi lib a haɓarsa.
Zaune yake cikin motar ya jingina bayanshi da sit ɗin, ya lumshe fararen idanunshi,
A hankali yake motsa tattausan jajayen laɓɓansa yana tasbihi.
“Subahanallahi wal’hamdulillah wa la’ilahaillah Allah Akbar, Astagafillaha wa’atubu ilaik”.
Yanaji a jikinshi kudun da akeyi yayi yawa, to amman dolene ayi irin wannan gudun domin lokaci na gab da ƙurewa, dan sosai sallan jumma’ar ya gabato, yasan yanzu masallacin ya fara cika, wannan dalilin yasa bai hana drevernshi gudunba, kuma bai hana fadawanshi sakin jiniyarba, dan ta hanyar jiniyarce zaisa a basu hanya su samu su isa kan lokacin daya dace.
Bawai ya bari ayi jiniyar da gudun dan nuna isa da ɗagawa bane, sai dan son isa masallacin Masarautar Joɗa da yake limanci kuma yake gabatar da Hudubar jummar matuƙar yana ƙasar tiyatar da yayiwa watace ya sa lokaci yaso ƙure mishi.
Motoci, biyar kuma na bayanshi wanda uku daga ciki na ɗaliban J U B da ya fitone, wanda yana aiki cikin Hospital ɗin makarantar, bayan kuma asibitinshi da kuma Genaral Hospital Ɓadawaya da yake zuwa sau ɗaya cikin ko wanne sati.
motoci biyun bayanshin kuma, Jalal ne da abokanshi.
Shiyasa motocin suka taho a jere-a jere dan shi bai fiye yarda ya fita da mota sama da biyarba, suma ba kullum ba, wani lokacinma yakan fita shi ɗaya.

A haka dai har suka fara ratsowa cikin Ɓadamaya, a dai-dai mashigar laleko ne,
Cunkoson ababen hawan ya yawaita, yayinda suka danno kai wurin yasa da yawa suka fara komawa gefen titi suna kauce musu dan basu hanya dan jiniyar dake musu nunin akwai uzurin gaggawa ga kuma fadawa a motocin.

Wani mai keke Napep ne ya gangara gefen titi har kusa da wani mai saida su Oranges Banana da dai sauransu.
Dogon tsaki mai Napep ɗin yaja tare da cewa.
“Wannan ai mulkin mallaka ne da izza duk an tsaidamu sabida wani can zai wuce ai duk nan muma saurin mukeyi munada babban uzuri, saurin da duk mutanen wurin nan keyi duk an katse mana hamzarinmu na son isa masallaci kan lokaci muji huɗubar jumman wannan rana”.
Mazan dake cike a bayan napep ɗin ne suka haɗa baki wurin cewa.
“Wallahi kuwa, gashi motocin nasu nada yawa.
zasu sa mu rasa jin hudubar wannan fasihin Malamin”.
Wani mai motane dayake gefensu ya amshi zancen da cewa.
“Kuma gaba ɗaya mutanen nan wurin masalacin zasu tafi, sabida duk mai son jin huɗuba mai ratsa jiki da zuciya baya ƙaunar ko furuci ɗaya na wannan malamin ya wuce shi domin Allah ya rigada ya mishi baiwar lafazi mai shiga zuciya”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button