GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

(Toh sokuwa kada kiji mijinki yace wai in bakya so zan fasa, kice zakice bakya so.
Yaseen farfaganda ce kawai, da son kwantar miki da hankali da irin su nuna miki kin isa dasu ɗinanne, kada kiyi zaton zasu tozar taki.
To da kinyi wautar cewa eh. Ni bana so ban aminceba kada kayi aure.
To kallon sokuwa zai fara yi miki yoh to ke uwarsace da zaki hanashi yin auren da Allah ya bashi damar yayi.
Ke kuwa amrya uwar kaɗi firi ki shigo rana tsaka ki nunawa uwar gida kin fita sanin mijinta.
Wawuya to wayayyu basa haka, wai ke irin ke ake so ɗinnan irin anai miki zaƙin bakin nan, to wlh kada ki kuskura kiyi zaton uwar gidanshi bata gabanshi maza bakin gangane duk ta inda yafi zaƙi ta nan suke bugawa.
Domin dolene ya miki wannan zaƙin bakin.
Sabida ai duk ɗan siyasa dole yayi kamfen yayin neman a zabesh to, hakama neman aure, kisa a ranki yana son matarsa.
Kema mada kisa a ranki amryafa ana sonta sannan uwar gida kiyi haƙuri domin amarya ko ta buzuzuce za’ayi mata marmari, in kinga yana rawa da ƙafa ɗaya tattara ki watsarsu, basu lokaci zai dawo har kataryarki ya nemeki.

Cikin tsananin zafin kishi Shatu tayi ajiyan zuciya data samu ya danne mata malolon da takejin yana gab da kasheta tace.
“A’a Yah Sheykh na amince Allah ya bamu zaman lfy”.
Cikin tarin jin daɗi da gamsuwa da wayewarta yace.
“Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati, Shatu my happiness my everything my life Mar’atussaliha”.
Ya fara jero mata sunaye, wani sunanma ranar ta taɓa jinshi.
Da sauri ta miƙe ta fita.
Tana cewa.
“Laa na manta na ɗaura tukunya”.
Ta faɗi hakan tana fita dan kada ya gane halin da take cikin ( Sabida in mijinki ya gane miki kinada mahaukacin kishi to kallon zarerriya zai rinƙa miki, hattara mata).
Tana fitowa bedroom ɗinta ta wuce.
Tana shiga ta meda ƙofar ta rufe, kana ta faɗa bisa gado ta saki wani irin masifeffen kuka mai cike da kishin mijinta abin sonta.
Da sauri Junainah dake Bathroom ɗin ta tanayiwa Khausar wonka ta fito.
Gefenta ta zauna jiki na rawa tace.
“Innalillahi Adda Shatu meya sameki meya faru?”.
Kawai sai ta mirgina ta ɗaura kanta bisa cinyar Junainah ta saki kuka mai rauni tare da cewa.
“Ba komai Junainah na tuno su Yah Lado da Inna ne”.
Cikin rashin gamsuwa Junainah tace.
“Adda Shatu wai yaushe kika fara ɗaukana a matsayin ƙanwar Hamma Jabeer? Kin mance tare muka tashi muka rayu bani da wani ɗan uwa ko ƴar uwa sama dake, gaya min gsky meya sameki?”.
Cikin yin ƙasa da murya tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
“Yah Sheykh zai ƙara aure Junainah na kasa hana kaina kuka!”.
Murmushi Junainah tayi tare da cewa.
“Shine zaki ɓoye min, to sa a ranki ni nan Junainah ko Ishman Aunty Rahma ya auro ni mai tayaki kishine.
Kuma wlh auren a dole yazo mishi kana kada kiyi kokonton soyayyarshu gareki.
Allah dole Abba ya sashi amsar auren Mamey ma har kuka tayi ita da Ummi wai kuna zamanku lfy kada a birkita muku zama sai dai naji sunce itama Aunty Jazrah Bata faɗa”.
Cikin jin daɗi tace.
“Toh dan Allah kada ki cewa su Mamey nayi kuka hankalinsu zai tashi.”
Cikin gamsuwa da hakan tace.
“Toh”.
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
“Wai yaushe kika dawo?”.
Cikin lumshe ido tace.
“Yah Junaidu ne ya ɗaukoni wai rana tayi kada in sha rana ya kodar masa sani”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Kana sukaci gaba da hira.

Haka dai aka fara shirin auren Jabeer da Jazrah, Junainah da Junaidu aure haiƙan ƙadaran.

Alhamdulillah anyi aure lfy an watse lfy, amare sun tare.
Kowa ya kama gidansa.

Bayan shekaru goma sha ɗaya.

Abubuwan da yawa sun faru cikin shekarun.

Yusuf ɗan Affan ya auri Afreen sai dai basa ƙasar suna India.

Jabeer ƙarami kuwa yana karatu a jami’ar Madina
Bappa yana nashi karatun a India.
Habibullah kuwa yana karatu a nan cikin jami’ar Ɓadamaya.

Jazrah ma ta haifi yara uku Aliyu takwaran Dr Aliyu, sai Ruƙaya da Aminatu takwarar Gimbiya Aminatu wacce itama ta rasu.
Shatu kuwa ta ƙara biyu Khadijah takwarar Umaymah sai autanta Sultan.

Rayuwa fa ta miƙa komai yana tafiya.

Hajia Mama ta rasu babinta ya ƙare a masarautar Joɗa.

Yau kimanin mako biyu kenan da tafiyar Shatu Cameroon.
Sai yau da hantsi jirginsu ya dawo.

Habib ne ya ɗaukota da Jabeer ƙarami wanda yazo hutu.
Sai Bappa wanda tare suka zo da Afreen da ƴan tagwayenta.
Mu’azzatu da mu’azzam dan da tagwaye tayi haihuwar farinta.

Suna zaune a falon Jazrah Aminatu na goye da Mu’azzam wanda takwaran Yah Sheykh ne.
Tanata juyi tana cewa.
“Sorry Mu’azzam Adda Afreen kizo ki bashi nono mana”.
Tura baki tayi tare da naɗewa bisa kujera, taci gaba da bawa Jazrah labarin littafin
Ba Kason ɗauka bane na Aysha Aliyu Garkuwa.
Da sauri Jazrah da yanzu take jin hausa ras tace.
“Afreen kamar muryar Mamanku nakeji fa”.
Da sauri suka miƙa baki ɗayansu suka nufi.
Side ɗin Shatu.
Da gudu Afreen ta iso ta bayanta ta ruggume ta tare da cewa.
“Oyoyo Mommy”.
Cikin sarkuri ta juyo don bayan ta tafi Cameroon Suka zo.
Cikin jin daɗi tace.
“Oyoyo Adda Afreen”.
Jabeer ƙarami ne ya ɗan harareta tare da cewa.
“Toh ki barta ta shiga ciki mana, kin tsare mana ita a woje.”
Ya ƙare mgnar yana amsar.
Mu’azzatu dake hannun Jazrah tare da cewa.
“Aunty yunwa nakeji fa”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Toh Yah J Jabeer ɗan Jabeer”.
Murmushi sukayi duka kana kab suka wuce falon Shatu.

Bayan sun gaggaisa ne, sunci sun sha, Shatu ta wuce ɗakinta.
Tayi wonka tare da al’wala tana fitowa tayi salla kana ta kimtsa cikin wani tattausan yadi Royal blue mai ɗan karen kyau riga da zani.
Ta cancaɗa daurinta ras.
Ta fesa turare, da shafe humra mai sanyin ƙamshi,
Da sauri ta jawo wayarta jin text ya shigo mata a waya.
Murmushi tayi ganin Habibi Da’iman. Sheykh kenan.
Buɗe saƙon tayi.
“Alhamdulillah barka da isa lfy Gimbiya Aysha, hasken Masarautar Joɗa, kina shigowa ƙamshinki har fada yazo ya gaidani.
Yanzu zamuyi salla, Please dan Allah ki gama da yaranki da jikokinki kafin in dawo in sameki a ɗakina, kinji ko Aish na”.
Cikin jin daɗi ta maida mishi amsa
“Uhummmm toh Yah Sheykh me zaka bani?”.
Murmushi yayi tare da rubuta mata.
“Kayan daɗin ki”.
Murmushi tayi tana mai lumshe ido.

Ai kuwa ana idar da salla ya nufo gida.
Kai tsaye ta ƙofar falon Shatu ya shiga.
Su Jabeer, Bappa, Habib, Aliyu, Sultan autanshi na biye dashi a baya.

A falon suka samu Afreen, da yaranta da Amina da Khausar Ruƙayya da Khadija suna cin abinci.
Suna ganinshi suka gaisa.
Kan Mu’azzatu dake hannun Jazrah da yanzu ta fito ɗakin Shatu dan mata sannu da hanya da kyau.
Shafa kanta yayi tare da cewa.
“Jika wahal da kaka ko?”.
Murmushi Jazrah tayi tare da cewa.
“Gata ƴar lukuta”.
Cikin jin daɗi yace.
“Haka Mamanta take tana ƙarama.
Kamar yau ina tunowa haka Abbanmu ke kiranta ƴar luku”.
Murmushi Afreen tayi cike da jin daɗi.
Jabeer kuwa baki ya taɓe tare da cewa.
“Abeey nifa”.
Cikin son ɗan nashi Yarima Jabeer kenan motsusu yayi tare da cewa.
“Kai ai na musamman ne”.
Duk suma sauran sai suka zuba mishi ido.
Ɗaya bayan ɗaya ya yabasu.
To Sheykh kuwa da tsuntsaye ma sai ya yabawa ko wacce taji bata kishin ƴar uwarta ko ganin tafi ƴar uwarta bare yaranshi.

A haka dai ya wuce ya tafi Side ɗinsa.

Ita kuwa Jazrah ta wuce Part ɗinta dan tasan.
Shatu ce dashi yanzu.

Ita kuwa Shatu a hankali ta fito tana mai baza ƙamshi.
Ganin kab yaranta suna sabgogin gabansu ne yasa ta shafa kan Mu’azzam dake zaune kusa da ƙofar ta wuce Side ɗin Yah Sheykh da ɗan sauri jin yana ɗan kiran Jabeer tare da cewa.
“Kira min Mommynku.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button