GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A tsakiyar garin Ɓadamaya ne suke tafiya sun zo dai-dai bakin Genaral Hospital Ɓadawaya.
Lamiɗo ya bada umarnin cewa su shiga cikin asibitin zai kai ziyarar dubiya wa marasa lfya.

Nan take kuwa suka jujjuya akalan motocin.
Suka fara kutsa kai cikin asibitin.
Da ƙarfi Jabeer ya rumtse idanunshi tare da furta.
“Lahaulawalaqutailla billah”.
A hankali sabida wani irin masifeffen bugu da zuciyarshi tayi da ƙarfin masifa.
Wani irin taraddadi ya diro masa.
Ya ilahi shine abinda ya ambata a saman lips ɗin shi.
Dip dab dip dab dip dab dip dab haka zuciyarshi ke harbawa da bugawa a tare a tare,
addu’o’in ya fara karantowa a zuciyarshi da harshenshi, yadda suke ƙara kutsawa cikin asibitin haka bugun zuciyarshin ke ƙaruwa.

Anan cikin asibitin kuwa, A maraba da baƙi Shatu take tun zuwanta sabida, anan aka juye duk fulanin da suka samu rauni sanadin wannan faɗan,
an zubesu a wurin gwamnatin jiha kuma tayi burus da batunsu sam bata bawa likitoci damar dubasuba,
Sai ma cewa sukayi sai fulanin sun nemo polices kafin a karɓesu.
Su kuma dama ƴan agaji ne ma suka taimaka suka kawosu nan ɗin ma.

Zuwan Shatu ne da Rafi’a da ta samesu a yashe hankalinta ya tashi.
Ranta yayi matuƙar ɓaci nan ta haura gidan sama inda can jerin jadawalin officer’s ɗin DOCTOR’S suke.
Rafi’a na biye da ita tana rabka mata kira.
“Garkuwa! Garkuwa!! Ke GARKUWA!!! Ina zakije ne wai?”.
Sam bata kula Rafi’a ba sabida abin da akayiwa ƴan uwanta yayi masifar ci mata rai.

Ganin yadda take gudu-gudu da sassarfa ne yasa itama Rafi’a ta fara Binta da gudu-gudu da sassarfa.

Yayinda kuma dai-dai lokacin Lamiɗo da tawagarsa ma ke tafe suna shiga cikin gidan saman.
Lamiɗo ne a gaba sai Jabeer da Galadima dake gefenshi da Sarkin Shaɗi.
Kana su Waziri da Wambai Matawalle da Makawa Ɗurɓi Turaki Tafida da dai sauransu, kana Dogari na rike da laima wa Lamiɗo,
Ɗanzagi kuwa ya kware murya yanata.
“Gyara kimtsi sarki ya gaisheku”.
Kana sauran fadawa masu red and blue ɗin Uniform kuwa da tabka-tabkan rawuna babu kunne ko ɗaya suna biye dasu a baya da gefe gefe, suna tafe babu takalma, ga dogin bulali masu masifar tsawo da kauri suna jansu a ƙasa.

Lamiɗo, Galadima, duk shigar manyan kaya na sarakuna, masu al’farma sukayi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer shigarsa ta al’farma na limamai yayi, wannan yasa kwarjinshi ya fi nasu.
Daga nesa zakace yafi shekarunshi in ka hangoshi sabida kamala da haibarsa da suka baiyana a fili.

Laminu kuwa tuni yayi gaba yana ɗaukar shigowarsu.
Sabida aikinshi na jarida dama neman rohotone aikinshi.

Sanadin saurin da suke ɗanyi ne yakesa al’kyabbar jikinshi ɗan buɗewa tana bazuwa hakan sai ya zama kamar ƙasaitace tasa yake wannan abun a wurin mai kallonshi.

Gaba daya duk ta inda suka zo wucewa, sai ya ɗaga hannunshi duka biyu, yayi musu sallama tare da cewa.
“Ya mai jiki?”.
In sunce da sauƙi. Sai yace.
“Laah Ba’as ɗuhhuru in sha Allah”.
Duk inda suka gilma sai an bisu da ido. Especially Jabeer da babu wanda zai kalleshi bai ƙaraba

Tuni labari ya kai ga kunnen Dim din asibitin.

Lokaci ɗaya ya kikkira DOCTOR’S ɗin ta wayar salulu ya sanar musu su kimtsa komai su kula da kowa yadda ya dace.
Mai martaba Lamiɗo na cikin asibitin.

Ita kuwa Shatu tana haurawa sama.
Ido take ɗagawa ta duba sunan Office da mai Office ɗin Office na forko taga musulmine haka yasa ta kutsa kai ciki.
Zaune yake babu kowa sabida duk majinyatan sun tafi.
Wasu an duba su, wasu kuma korarsu akayi da cewa yau half day ne, sabida haka su tafi.
Da mamaki ya ɗago kanshi jin an shigo mishi Office babu sallama. Da sauri yace.
“Waye?”.
Sabida cikin shigar yan matan larabawa take.
Arabian gawd ne mai masifar kyau da taushi a jikinta wanda samanshi yake a dai-dai jikinta ƙasa shi kuma yake a buɗe, wasu irin duwatsune a jikin rigar tun daga sama har ƙasa sai wal-wali sukeyi suna ɗaukar ido.
Tayi rolling kanta da ɗan kwalin rigar fuskarta ta fito ras a ciki.
Wasu takalmi Golding color ne masu ɗan tudu dai-dai misali sai Ƴar ma dai-daiciyar hand bang mai masifar kyau shima Golding color ne, sai wayarta ƙirar iPhone 11.
Fuskarta babu kolliya sai dai duk da haka bai hanata yin kyau ba gashin girarta ya konta lib-lib. Sai dai kuma ta rufe fuskar da tattausan Niƙab sai dai bashi da duhu sosai.
To wannane ya hana Dr Salim ganin fuskanta, ita kuwa Shatu cikin tsananin ɓacin rai da zafin tozarcin da akayi wa yan uwanta tace.
“Dr Salim”.
Cikin Mamaki yace.
“Na’am”. Yatsarta tasa tana nuna mishi maraba da baƙi ta wondon shi, cikin rauni tace.
“Dr Salim na tabbatar kai musulmine, kuma nasan kasan cew manzon Allah yace shi musulmi ɗan uwan musulmine! Shin ko ka mance hakane, da ka kasa taimakawa yan uwanka musulmai da kafurai sukayi musu rauni akazo aka watsar dasu a nan kuma kuka ƙi dubasu meyasa, ko dan kawai sun kasance fulanin dajine laifinsu?”.
Cikin sanyi Dr Salim yace.
“Wallahi umarni ne ba’a bamuba daga sama”.
Cikin tafasar zuciya tace.
“Umarni wanne irin umarni kuma zaku jira bayan Allah da Manzonsa sun baku dukkan dama da umarnin taimakawa ɗan uwanku musulmi muddin kunada dama”.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Dim ɗinmu ne ya hanamu dubasu”.
Cikin kufula tace.
“Kan kafurar uwarshi! wato a cikin asibitima sai an mana ƙabilan ci, dan Allah Dr kuje ku taimakawa bayin Allancan”.

Cikin jin ƙarfin guiwa ya juya, ya fita, ya nufi can.
Ita kuma haka ta rinƙa bin duk Office ɗin da taga na musulmi ne tana shiga.

Tawagar Lamiɗo kuwa suna isa baƙin wani tamfatsetsen Office Sheykh Jabeer, ya ɗan kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Ni bari in shiga office na, ko mutun biyar in duba kafin ku gama zagayawa”.
Cikin gamsuwa da hakan Lamiɗo yace.
“To bisimilla”.
Nan ya nufi babban barandar da Nurses suke tare a wurin maza da mata.
Jamil kuma na biye dashi da System ɗinshi a hannunshi. Hakama Haroon ya biyoshi.

Nurses ɗin kuwa suna hangoshi duk suka mimmiƙe tare da cewa.
“Sir barka da zuwa”.
Barka dai yake ce musu tare da ratsawa yana wucewa.
Su kuwa sun taru a wurin ne dan tawagar Lamiɗo na wucewa su sauƙa ƙasa su duba Fulanin nan kamar yadda Dim ɗinsu ya basu umarni sabida kada Lamiɗo ya gansu a yashe a ƙasa yasan abun bazai mishi daɗi ba.
Suna ganin ya shiga Office ɗin suka juya da nufin zasu tafin sai kuma suka tsaya jiyo muryar Shatu na cewa.
“Ku tsaya ina kuma zakuje? Baku da aikin yi ko? Amman da yake ba taimako ne a zuƙatankuba kun bar bayin Allah a wulaƙance ko?”.
Cikin masifar Nurses da su ba komaiba sai iya ciwa mutane zarafi a hatsale tace.
“Ke kuma waye”.
Kallonta Shatu tayi sama da ƙasa tare da kallon rubutun dake saman aljihun rigarta ganin sunan arniyace ga kai da gashin doki ga uban faratu kamar na jaki yasa taja tsaki tare da cewa.
“Banyi da keba, da masu hijabi nake mgn”.
Yadda tayi mgnar da ƙarfi ne yasa, su Jabeer ma jiyo muryarta,
wanda shi kuwa zuwa yanzu yana jin zuciyarshi zata iya faɗowa ƙasa dan bugawar da takeyi.
Jin muryar wata nurse ɗin tana cewa.
“Wannan ma ai iskanci ne”.
Cikin taɓe fuska ya nunawa Jalal yatsa alamun ya buɗe mushi ƙofar yaga meke faruwa da suka cika mishi kunne da hayaniya.
Da sauri Haroon yabiyo bayan Jalal suka fito.

Shi kuma Sheykh Jabeer komawa yayi ya jingina da jikin kujerar shi.
Tare da rage girman idonshi ya zubawa bayan Shatu ido.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button