GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Gaban dreesing mirror ta koma wasu turaruka masu ƙamshi guda biyu ta fesa.
Kana ta zato wani ƙaton hijabinta Black blue mai ɗan karen kyau da sheƙi, ta zurashi har ƙasa ko idon sawunta bazaka iya ganiba.

Sallayarta ta ɗauka kana ta fito da ɗan sauri ta nufi Side ɗinsa.

Ganin baya falone yasa ta wuce bedroom da sallama a bakinta.
“Wa laikissalam”.
Ya amsa mata lokacin da ta turo ƙofar ta shigo.
A gogon hannunshi ya kalla tare da cewa.
“Iso muyi lokacin na tafiya.”

To tace tare da ƙarasowa tsakiyar ɗakin.
Sallayan dake hannunta ya kalla tare da taɓe fuska kana yace.
“Duk sallayan dake ɗakin nan bazasu isheki bane sai kinzo da naki?”.
Girgiza kai tayi alamun a a.
Hannunshi yasa ya amshi sallayar, kana ya juya ya fuskanci gabas.
Ita kuma ta ɗan matso gefenshi ta tsaya daga bayanshi kaɗan. Ganin ta kimtsa ta nitsu yasashi tada kabbara.

Masarautar Joɗa kuwa, an dai kira salla amman ba’a samu mutane da yawa ba sabida laruran ruwan sama.

Bayan sun idar da sallan ne, sukayi addu’o’in kana sukayi nafila raka’a biyu, sannan suka zauna.
Tasbihi ya ɗanyi kana ya gyara zamansa da kyau, Al’ƙur’ani dake kan durowar dake gaban wurin da yake sallan ya dauko,
juyowa yayi ya fuskanceta kana ya miƙa mata.
Kallonshi tayi tare da amsar ƙura’an ɗin.
“Ki karanta inji yadda kira’arki take”.
Ya faɗa idonshi na kanta.

Shiru ta ɗanyi tare da kauda idonta daga kan nashi.
Cikin sanyi ta miƙo mishi ƙura’an ɗin”.
Ba tare da ya amsaba yace.
“Bazakiyi ba, inji ki samu lada ba?”.
Kai ta jujjuya kana a hankali tace.
“Zanyi”.
Cikin kauda kanshi daga kanta yace.
“To bismillah”.
Miƙo mishi ƙura’an ɗin ta kumayi tare da cewa.
“Ka riƙe min sai inyi kana duba min haddana yayi ko da gyara”.
Wani irin sassanyan numfashin da bai shiryawa bane ya subce mishi.
Cikin nitsuwa yace.
“Ba sai na duba mikiba, kada ki damu kiyi inaji in kin ɓata zan gane ba sai ina duba surar ba”.
Cikin sanyi ta ɗan ɗago idanunta ta kalleshi kana ta ruggume ƙura’an ɗin a ƙirjinta.
Lumshe idonta tayi tare da cewa.
“Wacce sura zan karanta?”.
Kanshi ya jingina da jikin gado kana ya zubawa fuskarta dake zagaye da hijabin ido a hankali yace.
“Surar da kikafi jin daɗin haddarsa”.
Cikin nitsuwa tace.
“Suratul Noor”.
Kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
“Bismillah”.
Kai ta rausayar ba tare da ta buɗe idonta ba, ta gyara zamanta kana a hankali tayi gyaran murya tare da cewa.
“Aaoozubillahi minashaiɗani rajen.
Mismillahi rahmaniraheem.
(Suratu anzalnaha wa farad’nahah wa’anzalnaaa fihahhhhhhhhhhh Aayati baiyinati la’allakum tazakarun.”
Ida nunshi ya lumshe a hankali tare da sauƙe numfashi jin yadda ta bada taƙib a wurin fihahhhhhh, kana ta rufe ƙarshen ayar da bawa Wawun iya damarsa.
A hankali ya buɗe idanunshi ya zubawa lips ɗinta su, sabida jin taci gaba da aya ta biyu.

Karatun takeyi cikin sanin ƙaidarsa da bawa ko wanne harafi haƙƙinsa tsakanin ɗauri da wasalin sama dana ƙasa da kuma wurin ja mai shida da huɗu da uku.

Sosai yake jin sautin zazzaƙar muryarta na ratsa mishi kunnuwa har zuwa ƙahon zuciyarshi.

Kanshi ya jingina da gado yana jin yadda take fitar da Tajwid da kyau da fidda Qalqala, iglab, idgham, ikhfa’a Ghunna.

A hankali ya ɗan ɗago kanshi lokacin da ta iso aya ta 31 gyaran murya ya ɗan yi,
wanda yasa ta buɗe lumsassun idanunta da sauri.
Kallon alamun tambaya ta mishi.
Kanshi ya jujjuya tare da mata alamun taci gaba.

Nannauyan numfashi ta sauƙe tare daci gaba.

Kai ya sake ɗagowa lokacin da tazo aya ta 61 still yayi gyaran murya.
Ci gaba tayi da karatun dan ta fahimci alama yake mata.
Kasan cewar suratul Noor ayoyi 64 gareta.
Aya uku ta kara kan na 61 da ya mata gyaran murya tazo ƙarshen ayar.
Da sauri ta buɗe idonta jin yace.
“Sadakallahul azeem”.
Kanshi ya jinjina tare dayin murmushi.
Ita kuwa cikin sanyi tace.
“Ɓata nawa nayi?, Yah Sheykh a gyara min?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Baki ɓataba kinyi ƙoƙari sosai”.
Cikin sauri tace.
“To kuma naji kayi gyaran murya”.
Gyara zamanshi yayi ya fuskanceta da kyau kana yace.
“A aya ta nawa da ta nawa nayi gyaran murya?”.
Hannunta tasa ta tallaɓe fuskarta tare da cewa.
“Aya ta 31 da 61”.
Hannunsa yasa ya ɗan shafa gemunsa kana yace.
“Ayoyin sun kasance ɗaya daga cikin dogin ayoyin da aka ƙiyasta tsawonsu dake cikin al’ƙur’ani mai girma”.
Kai ta jinjina alamun gamsuwa kana tace.
“Ayyah, wato shiyasa lokacin da nake haddarsa aya ta 31 saida na kusan sati a kanta, bappa yayi ta faɗa wai nasa wasa a gaba”.
Kanshi ya jinjina kana yace.
“Sosai ma kam gskyar Bappa kinyi wasa”.
Cikin sanyi tace.
“Kai a kwana nawa ka haddaceshi?.”
Murmushi yayi tare da cewa.
“A kwana bakwai sati ɗaya na haddace suratul Noor”.
Cikin ware ido tace.
“Kai ai ƙwaƙwalwarka ta musamman ce Yah Sheykh.”
Miƙe tsaye yayi yana cewa.
“Ko?”.
Eh tace tana kallon dunduniyar ƙafarshi.
Wayarshi ya ɗauka, ɗan daddan nawa yayi kana ya kara a kunne jim kaɗan ya fara mgna.
“Ayyah Ummi zanci gashinki”.
Murmushi Ummi dake zaune bisa sallaya tayi tare da cewa.
“Kaza ko zabuwa?”.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Aysha kana yace.
“Zabuwa, Ummi ta gasu da kyau”.
Cikin sakin fuska tace.
“To Sheykh bari inyi sallan isha’i”.
To yace kana ya katse kiran.
Ya dawo ya zauna.

Ummi kuwa
har ta zauna sai kuma ta tashi.
Ta nufi kitchen a cewarta kafin tayi sallan zabuwar ta sulala.

A gudanta haka ta wonketa fese.
Kana tasa a tukunta, sannan tasa al’basa, kanamfari citta tafarnuwa kaɗan sai kurry, sannan tasa Maggi da gishiri kaɗan, sannan ta ɗaura a wuta kana ta wonke hannunta ta koma ɗakinta.

Ruwa kuwa har yanzu tsugashi akeyi kamar ba gobe.

Tana gab da shiga falon ne ta jiyo muryar Jalal.
“Ummi”.
Da sauri ta juyo tare da cewa.
“Yauwa Jalal ɗaukar muku abinci tun ɗazu ku nake tunawa”.
Kanshi ya sunkuyar yana kallon yadda yake ɗigan ruwa.
Dinning table suka nufa.
Foodflaks ɗin ya ɗauka tare da plate kana ya juya ya fita da sassarfa.
Yana fita Ummi ta meda ƙofar ta rufe kana ta koma ɗakinta.

A can ɗakin Sheykh kuwa.
Kallonta yayi tare da cewa.
“Bappa ya baki tabsir a kan surar ne?”.
Da sauri tace a a.
A gogon hannunshi ya kalla kana yace.
“Kina son ki san abinda Allah madaukakin sarki yake cewa a Suratul Noor ɗin?”.
Da sauri tace.
“Eh sosai ma.”
“To tashi muyi sallan isha’i sai in fassara miki ita ko a taƙaice”.
To tace kana ta miƙe.

Bayan sun idar da sallan isha’i sukayi addu’o’in kana ta miƙe tayi shafa’i da wutri”.
Sannan ta zauna tana tasbihi.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta kana ya meda kai yaci gaba da Addu’o’in.

Ummi kuwa tuni ta fita tazo kitchen.
Gashin tukunya mai masifar daɗi da ƙamshi tayiwa zabuwar.
Bayan ta kwashe robon, ta sake sata ta hasata da kyau.
Gaba ɗaya gidan ya cika da ƙamshi mai tada yunwa.
A wani kekyawan Foodflaks tasa dangwaleliyar zabuwar kana tasa, romon mai cike da ɗan-ɗano da kayan ƙamshi a ƙaramar kula.
Sassayan madarar shanu, ta haɗa da zuma ta gaureya kana tasa a flaks ɗin riƙe sanyi. Kamar yadda tasa yana son zabuwa da madara da zumar.
Plate, cup, spoon, fork, knife, ta jera bisa plate ɗin kana ta kife ɗaya a kai.
Sannan ta jerasu a tray.
Sannan ta fito tazo ta ajiyesu kan dinning table, ita kuma ta ɗebi tuwo da miyar kasenta taci tayi haniƙan kana ta koma cikin ɗakinta ta ɗauki wayarta, ta kirashi ta shaida mishi ta gama yana kan dinning table.
“Sannu Ummi ngd matuƙa Ubangiji ya biyaki da mafi kyawun sakamako”.
Yace cikin girmamata.
Amin Amin tace kana ta katse kiran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button