GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Gaba ɗaya kowa jikinsa yayi la’asar musamman matasa masu wasa da salla,
Jin ya juya yayi gyaran murya ne.
Yasa gaba ɗaya kowa ya mike ya fuskanci gabas masamar lada.

Cikin nitsuwa da tattausan harshe yake rare karatun al’ƙur’ani mai girma.
Lokacin da yake limancin sallan jumma’ar da a ƙalla yana samu halartan mutun sama da Dubu biyu.

Bayan anyi salla raka’a biyu kamar yadda yazo a nafsi, akayi addu’a aka shafa kana, mutane suka fara firfita daki-daki.

Bayan 30 minute shal cikin masallacin.
Dan gaba ɗaya kowa ya nufi wurin lamuran yau da kullum ɗinshi sai mutanen da ba’a rasaba wanda su sai dare zasu bar cikin masallacin.

Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa, ne tafe a hankali cikin irin takunsu na sarakai,
Yayinda Jikinsa mafi soyuwa a garesa ke gefen damanshi,
fadawane ke biye dasu a baya, sun zagayesu,
Sai kuma bayansu can kuma Ayarin fadawan Jalal da Jamil ne wanda suke tagwaye ƙannen Sheykh Jabeer.
shi kuwa Malam Jabeer taku yakeyi a hankali cikin rashin nuna ɗagawa a kan doron ƙasa, tafiyar yake tamkar yana tausayawa ƙasar yayinda mutane kuwa ke kallon hakan a matsayin ƙasaitace da jinin sarauta dake yawo a sasan jikinshi.

Suna tafene a tare yayinda bakin Sheykh Jabeer ke motsawa a hankali hankali, wanda sai ka lura kake gane, tasbihi yakeyi a zuciyarshi wanda hakan ya zame mishi abin ci da sha a rayuwarshi.
“Astagafirullaha wa’atubu ilaik, Astagafirullaha! Astagafirullaha!! Subahanallahi! Walhamdilillah wa lailaha’illalahu Allaahu akbar. Astagafirullaha”.
Waɗannan sune kalamen da basa rabuwa da bakinsa, dama wasu masu tarin yawa.

Ta ƙofar dake shiga masarautar daga jikin masallacin sukabi.

Masarautar Joɗa babbar masarautace mai tarin girma tarihi.

Ginin Masarautar ginine mai masifar kyau da ɗaukan hankali.

Kana shiga daga asalin babban gate ɗin fadar, zaka samu wata shimfiɗeɗɗiyar hanya mai girma irin mai guda biyun nan, gefe da gefen hanyar duk wasu irin dogin fulawowi na mijin kwanda ne masu tsawo da kyan gani,
sai kuma tsakanin titunan, shima jerin dogayen bishiyoyin ne.

Tafiya mai ɗan tsawo, zakayi kafin, ka isa wani babban Round about mai masifar kyau, wanda cikinsa ke ɗauke da babban kwarya a ƙasa, sai kuma ƙananan kware, guda uku, sai kuma ginin mutum-mutumi na kekyawar saniya fara mai ɗigo-ɗigon baƙi, wanda mace ke tsugune a gefe kamar tana tatsan nono sai kuma ɗan saurayi matashi na riƙe da sanda ya coge da ƙafa ɗaya.

Sai kuma korayen ciyawi masu masifar kyau da sanyi wanda akayi alamun manomi na ciki.

Daga nan ne hanyoyin cikin masarautar suka rabu huɗu, ɗaya yayi gefen dama ɗaya yayi gefen hagu ɗaya yayi gabas ɗaya yayi yamma wanda ta nanne ake shigowa.

In ka miƙe ta yamma daret itace titin da zai sadaka da asalin sashin Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa wanda nan sashin matanshi da hadimanshi yake da sashinshi dama faɗar duk nan take.
In kayi gefen dama kuwa wasu irin tsala-tsalan gine gine-gine masu tsananin kyau da ɗaukar hankalin wanda suna nan part-part ne masu girma da tsaruwa, an ƙawata tsakiyarsu da wani sassanyan Garden mai girman gaske.

Inda part ɗin sun kai goma, mafi kusa da sashin mai martaba sarkin Nuruddeen Aliyu Bubayero, shine sashin GARKUWAN FULANI, wato Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero.
Sai kuma na gefen daman Sheykh Jabeer shi kuma na Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero ne, da matarsa Juwairiyya.
Sai na gefen hagunshi kuma na Jalal, ne na kusa da Jalal da kuma na Jamil ne sai dai Jamil yafi zama a sashin Jalal duk da korarshi da yakeyi wasu lokutan kuma lokacin kuma yana sashin Sheykh.
Sai sashin baya kuma sashin Affan.

Daga gefen hagun Masarautar kuwa wasu tamfatsa-tamfatsan plat ne masu girma har guda huɗu, sai kuma wani babban bene dake tsakiyarsu mai tarin girma wanda nanne sashin babban ɗan sarki Habibullah da matanshi.

Sai ta gefenshi can kuma wasu manyan part- part ne kimanin guda biyar wanda duk ƙanne shi ne da iyalansu da ƙananan yaransu a ciki.
Yayinda duk manyan yaransu kuwa kowa nada part ɗin shi a gefen da part ɗin Sheykh yake a ƙalla dai Part ɗin cikin masarautar Joɗa sun kai hamsin da biyar.

Can wurin mashigar kuma wasu ƴan saffan-saffan part-part ne wanda bisa dukkan alamu duka na bayine da hadimai da matansu.

Tsayuwa fasalta cikin ko wanne sashi na masarautar bazai yiwuba, sai a hankali.

Sai dai ko wanne part yanada Garden mai ɗan girma, wannane yasa gaba ɗaya masarautar ke zagaye da korayen fulawowi da bishiyoyi masu kyau.
Fentin masarautar gaba ɗaya iri ɗaya ne, Sky blue and white, mai ɗan karen kyau, a mahaɗar sashukan kuwa wani irin tamfatsetsen sweeminpool mai girma wanda ruwansa ke sky blue.
Can bayan sashin Mai martaba da Sheykh kuwa wani ƙaton filine mai cike da dawakai, da sashin mai rainonsu, gefe ɗaya kuma raƙuma da shanaye ne da makiyaya su, kana ga tumaki, a gefen Sheykh Jabeer ne kuwa akayi wani ɗan madai-daicin gidan zu ta bayan ɗakunan shi wanda yake da tarin tsuntsaye kamarsu, Ɗawisu, jimina, mikiya, agwagin ruwa, tolo-tolo, tattabaru, kana sai Aku. Da sauran tsuntsaye carki, kurciya, hasbiya, caccagi da-dai sauransu, shiyasa sashinsa ya kasance namusamman, don Garden Park ɗin ciki yafi na sauran part ɗin duka girma da kyau, sabida shine asalin Garden ɗin tarihin masarautar Joɗa.
Daga nan mashigar masarautar kuwa akwai wani babban filin sukuwa mai girma.

Daga masallacin Masarautar kuwa akwai miƙeƙƙiyar hanya har cikin masarautar wanda za’a iso gab da fada sannan kowa zai samu hanyar sashinsa.

A tsakiyar cikin masarautar ma kuwa akwai wani masallaci mai girma.

Wannan kenan sai a hankali zaku san mutanen masarautar da sunayensu halayensu dama nasabarsa da danƙantarsu da manufarsu.

A hankali Sarki Nuruddeen da Sheykh Jabeer suke takawa.
Suna shiga cikin gidan waɗannan fadawan suka tsaya a bakin Gate ɗin.

Kana wanda suka samu a wurin suka miƙe da azama wani dogon carpet mai azabar kyau da taushi, ɗaya daga cikin fadawan ya zo ya ajiye gabansu kana ya rinƙa yin baya-baya yana worwore musu carpet ɗin.
A hankali Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa yasa hannunshi ya kamo hannun kekyawan matashin jikan nashi da kab cikin jikokinshi ya fita da ban, hannunshi yake murzawa cikin nasa hannun a hankali a hankali.
kana suna tafiya a hankali, cikin takun sarauta,
Gefen mai martaba Nuruddee bayine da dogarai a ƙallah sun kai Ashirin da biyar, gefen Sheyk Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero kuwa,
Ƴan saffan-saffan fadawane da basu kaishi shekaruba, a ƙalla sun kai goma.
Wanda wannan tsarinsa ne yace bazai iya ganin sa’an mahaifinshi ba ko sa’an Ya Jafar ɗinshi ba suna mishi bauta Babban Yayansu Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero suke kira Yah Jafar.
Kanshi ya ɗan murza ya juya a hankali da gefen ido ya kalli Kakan nashi dake magana cikin yin ƙasa da murya dan ko sarkin dogaren dake gefenshi baiji me yake cewa ba.
“Sheykh yaushe ne tafiyar taku?”.
Siraran kyawan Idonshi ya lumshi a hankali ya kuma buɗesu tare da rausayar da kanshi.
Maimartaba bai damu da jiran amsar tasaba yaci gaba da cewa.
“Munyi Magana da Aminina Sarki Jalaluddin yace min Kakarka UmmuKulsum tace tafiyar taku ta ƙara toko?”.
Shiru ya ɗanyi har saida sukayi taku uku zuwa biyar kana ya gyaɗa mishi kanshi kai a hankali irin gyaɗa kai na kamala”.
Dai-dai lokacin kuma suka iso dab ƙofar mashigar sashin Maimartaba, wanda dama duk ran jumma’a daga shabiyu yake tashi zaman fada,
sanin hutawa yake a irin wannan lokacin ne ya sashi ɗan sake hannun Sheykh Jabeer tare da cewa.
“Sirranta komai a rai yanada wuya, amman kai baya maka wuya, ya zama kamar jininki, akwai tauraro na musamman a goshinka, wanda nake fatan watan wata rana ya haska zuƙatan ahlinka dama talakawan da zaka mulka”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button