GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Kai tsaye Side ɗin Yah Sheykh ta nufa tana danna mishi kira.

Baya cikin ɗakin ganin hakane yasa ta juyo da sauri.

A corridor’n shigowa falonshi sukayi kiciɓis da ƙarfi ta faɗa jikinshi tare da ruggumeshi gam-gam cikin kiɗima jiki na rawa tace.
“Yah Sheykh, Jahan ya sake zuwa har cikin ɗakinan.
Yah Sheykh har kan gadona ya hau”.
Tallaɓe kanta yayi cikin mamakin tashin hankali da take cike, danne murmushin sa yayi tare da cewa.
“Me ya miki?”.
Sai kuma ya janyeta a jikinshi tare da juya wa da sauri ya nufi sashinta.
Da gudu ta biyo bayanshi tana cewa.
“Yana ciki muje wlh yana ciki”.
Shiru tayi ganin babushi babu dalilinshi.
Cikin tashin hankali tace.
“Wlh yazo har nan har kan gadona.
Da ina ta kiranka yace min wai Matar Liman kiyi a hankali ba jinki zaiba dan yana can masallaci”.
Gaba ɗaya dariyar mugunta ke cinsa.
Sanin in yayi dariyar zata iya fahimtar wani abune yasashi zuba mata ido.
Sosai ta gigice, hannunta ya kamo suka nufo babban falon.
Suna fitowa Ummi da Saratu na shigowa.
Da sauri Saratu ta nufi kitchen.

Ummi kuwa ta nufi kansu.
Cikin kaɗuwa tace.
“Sheykh meya faru?”.

Yana riƙe da hannunta yace.
“Ummi wai cewa tayi yauma Jahan yazo har cikin ɗakinta.

Ni kuma tun kwanaki da take cewa, yazoma na bincika akace min baya ƙasar nanma gaba ɗaya.

Ya fita UK kuma ance zai kai wata shida kafin ya dawo.
To waye Jahan ɗin da take gani, taketa ihu duk jama’ar masarautar Joɗa naji in ba aljanunta ba.”

Cikin damuwa Ummi tace.
“To wake firgitata har hakane”.

Cikin riƙo hannunta gam ganin yadda taketa fizge-fizgen tana rantsewa wlh ƙarya akeyi yana garin.
A hankali yace.
“Kawai fa Ummi al’janunta ne ke zuwa da wani sabon salo.
Kuma zanci musu mutumci, bazasu medamin gida sansanin ihu da kururuwa ba”.

Cikin sanyi Ummi tace.
“Babu maijin ihunta fa Sheykh, kai dai ka ƙara bincike da kyau akan al’amarin.”

Sai ta kuma kalli Aysha da har yanzu a gigice take.
“Ki nitsu ko Aysha gani gashi ga Saratu.
Babu wanda zai shigo nan zamu ganshi”.
Cikin sanyi ta gyaɗa kai.

Jan hannunta yayi suka nufi falonshi.

Ummi kuwa wurin Saratu taje suka fara aikinsu.

Shi kuwa yana riƙe da hannunta ya zauna bisa kujera kana ya zaunar da ita.
System ɗinshi dake hannunshi ya ɗaura kan stoll ɗin dake gabanshi.

Tare da buɗe wa, ɗan juyowa yayi ya kalleta.
jin har yanzu jikinta rawa yakeyi, a hankali yace.
“Ke wai me ya miki”.

Cikin rawan murya na tsoro tace.
“Abunda kakeyi min”.
Da sauri ya juyo ya fuskanceta tare da zaro idanunshi woje cikin ɗan ɗaga sauti da haɗe fuska yace.
“Me nakeyi miki da yayi miki?”.
Ya ƙarashe mgnar a fakaice.
Cikin takaici tace.
“Hannunshi yasa a rigata”.

Jawota yayi jikinshi tare da miƙewa tsaye.
Cikin faɗa da zafi rai a ɓace na fatar baki yace.
“Zancen banza kenan.
Ko iskarki ce, ta isa in haɗa muhalli da itane, bare wani can Jahan da ba’a san asalin menene shiba menene addininshi ba.
Ke wacce iriyar yarinyace, da zaki tsaya har ya kalli abinda Muhammad Jabeer ya kalla har ya taɓa min kayana.
Lallai ya nemawarwa kansa masifa da yayi gigin kai hannunshi inda hannuna ya kuskura ya taɓa.”
Juyawa yayi a fusace ya nufi.
Bedroom wayarshi ya ɗauka tare, da kiran Jamil wanda ma’akacine a ma’akatar su Jahan.
Cikin kausasa murya yace.
“Ka binciko min waye Jahan ina yake suwa yakewa aiki nanda rabin sa’a ina son amsoshi na”.

Da sauri Jamil yace to.

Ita kuwa Aysha a inda ya tashi ta kwanta.

Bayan wani ɗan lokacin.
Jamil ya kira Hamma Jabeer ɗin ya shaida mishi cewa da tabbas Jahan baya nan.
Baya ƙasarma gaba ɗaya tsawon watanni biyu.
Kuma babu wani Jahan da ya sani.”

Jin hakane yasa Sheykh, yin wani sihirtaccen murmushi da kyau.
Ko Jamil bai san komai kan Jahan ba.
Murmushi yayi tuno yadda yake cewa al’janin Aysha ke zuwa da salon iskanci.

Ranar dai a gida ya wuni, yana fakewa yaita murmushi lokaci zuwa lokaci.

Ita kuwa Aysha wurin Ummi ta koma.

Sai da Yamma Sheykh da Galadima sukaje suka samu Lamiɗo sukayi mishi dukkan bayanin tafiyar da sukayi da nasarorin da suka samu a ciki, da alamar matsalar da suka tarar, nan sukayi tattaunawa tamu sannan kan al’amarin.

Aysha kuwa sai washe gari Ummi ta mata jagora taje, Sashi Gimbiya Aminatu.

A can ta samu, Aunty Juwairiyya da Mamin Affan.

Nan suka zauna sunata hira.

Sai yamma ko wacce ta nufi Side ɗinta.

Yau sallan layya saura kwana uku.

Mutane nata shiryawa shirin ƙaramar salla.

Yau tunda safe da Sheykh ya fita bai dawoba sai dare.

Washe gari da Safe, Junaidun ya kira Aysha bayan sun sha hira yake cemata.
“Adda Shatu, jiya Dr Sheykh yazo Rugar Bani, wurinsu Arɗo Bani da Babanmu.

Sunata godiya dai sunce ince miki ki ƙara yi mishi godiya kan hidimar da yayi mana.”
Cikin mamaki tace.
“Au dama shine likitan da ya maidaku asibitinshi ya kula daku?”.

Da sauri yace.
“Eh amman nima ban san shine kuma mijinki ba sai.
Yau da yazo.
Ni nayi zaton wurinmu yazo sai naga su Baba da Arɗo Bani sunata murnar zuwanshi, sai na gane bafa wurinmu yazo ba”.
Uhum tace tare da cewa.
“To ba matsala in sha Allah zan masa godiya”.

Daga nan sukayi sallama.

Konciya tayi tana nazartan takun Yan Sheykh sai dai duk nisan da zurfin tunaninta kafin taje wuri a tunani ko bincike tuni ya wuce ta.
Abu ɗaya ta fahimta, yana bin diddigi akan abubuwa da dama shi mutumum ne bauɗaɗde mai algibata tako ina ka buga zaka sameshi.

A ranar bata ganshi ba.
Hakama washe gari.

Sai da asuba Ummi ta tasheta akan ta kai mishi.
Abun yin sahur sabida gobe za’a tashi da azumin arfa.

A tsaye ta sameshi a falo da waya a hannunshi.

Bisa alamu da Aunty Hafsat yake mgn.
Gabanshi ta ratsa ta ajiye mishi tray’n a kan stoll dake gabashin.

Ba tare da ya kalletaba ya kamo hannunta ya riƙe lokacin da zata juya ta fita.

Sai kuma yaci gaba da wayar.
“Aunty Hafsat wai har bikin ya isone?”.
A can ɗaya gefen murmushi tayi tare da cewa.
“Sosai ma kuwa Sheykh saura wata ɗaya da kwanaki ne zulhajji na ƙarewa da kwana biyar na sabuwar wata za’a fara bikin”.

A hankali yace.
“To kuma shine zakuzo tun bayan salla da mako ɗaya, yanzu ita Ramatu da wa zata bar mijinta ta taho wata kusan biyu”.
Hannunta dake cikin nashin hannun ya ɗan ƙara matsewa.
Tare da janta jikinshi.
sai kuma ya ɗan gyara tsayuwarshi tare da cewa.
“A a Aunty Hafsat ku bari in bikin saura mako ɗaya ko biyu sai kuzo”.

Da sauri tace.
“Sai dai biyun”.

Uhum yace. Ita kuwa cewa tayi ina.
“Ya Ɗiyata Aysha kuma yar uwata aborso a rayuwarmu”.
Murmushi yayi a hankali tare da lumshe idonsa yanaji wasu zafafan hawaye na tashin hankali na tsastsafo mishi yace.
“Gata”.
Yana faɗin haka ya liƙa mata wayar a kunnenta.

Da sauri ta ɗago ta kalleshi.
Tsareta da ido yayi. Jin muryar Aunty Hafsat ne yasata ɗan murmushi tare da cewa.
“Aunty Barka da asuba”.
Cikin tarin so tace.
“Barka dai Aysha yasu. Jalal da Jamil ya kewan Hibba”.

Cikin murmushi tace. “Suna lfy Aunty ina kewar Hibba kam sosai ma”.

“Kada ki damu mun kusan haɗuwa ai muma zamu zo ai. Ya Jazlaan yana lfy ko”.
Cikin jin daɗi tace.
“Allah ya kawoku lfy Aunty”.

Amin Amin tace.
Kana tace.
“Ya Jazlaan yana lfy ba wata damuwar ko”.
Ɗago kanta tayi ta kalleshi,
Kwaɓe mata fuska yayi tare da mata alamun bata amsa.
Cikin sanyi tace.
“Uhum Alhamdulillah”.

“Masha Allah. To sai anjima ko kada in hanaku yin sahur”.

Ɗaga nan sukayi sallama.

Shi kuwa a hankali ya zauna tare da zaunar da ita gefe.
Kana yace.
“Kinyi niyar yin azumin arfanne?”.
Kai ta gyaɗa mishi alamar eh.
Kauda kanshi yayi tare da cewa.
“To kin nemi izinine?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button