GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Da sauri ya ƙarasa jikin motor. Hajia Mama na biye dashi.
Yana isa inda suke yasa tattausan hannunshi ya buɗe marfin motar.
Karo na forko da naga murmushi a fuskarshi, cikin tarin shaƙuwa da kulawa yace.
“Marhababuki ya Umaymah, ta faddal”.
Wani irin murmushi Umaymah tayi cikin tsantsar so tasa hannu ta kamo hannunshi daya nuna mata alamun ta fito.
Wani irin yalwataccen murmushi mai nuna tsantsar jin daɗi ya kumayi lokacin da yaji tasa hannunta tsakiyar kanshi.
Da sauri ya rusuna a bakin motar cikin sanyi ya manna kanshi da guiwowinta dake zuro woje,
kanshi ta shafa tare da cewa.
“Allah yayi maka al’barka ya kare mana kai da kariyarsa mai tarin yawa ya iya maka abinda idonka baya gani”.
Amin Amin, su Haroon da Jalal, Jamil, Hibba, ƙanwar Haroon, da kuma Imran, Sulaiman, Aunty Juwairiyya dake kusa da Umaymah.
suka amsa tare da murmushi a fuskokinsu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya tashi kana ya buta hanya ta fito.
Tana fitowa Hajia Mama ta ƙara so gareta cikin tarin baiyana jin daɗi ta ruggume Umaymah tare da cewa.
“Ta ɗanki kawai kikeyi, mu har mun kusa mu bushe a tsaye”.
Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“Afwan ya Aunty kin san in Jabeer na yana wuri bana ji da ganin kowa sai shi”.
Haroon ne ya taɓe baki tare da cewa.
“Uhumm ai mun saba ganin wariyar launin fata”.
Hannunta tasa ta ɗan zunguri Haroon tare da cewa.
“Kishi”.
Jamil ne ya ɗan kallesu lokacin da suka ɗunguma suka nufi Sade ɗin Jabeer cikin tura baki yace.
“Allah ko Mama kada ki bari Umaymah ta sauƙa a sade ɗin Hamma in dai ba sade ɗinmu zata sauƙaba Muda muke ƙanana sai ta sharemu saishi.
Tunda hakane ta sauƙa side ɗinkin”.
Cikin dariya Umaymah ta juyo da sauri ta kalleshi tare da cewa.
“To Jamil harda kai, wato kaima ɗan team ɗin Haroon ne ko?
To sha kuriminka Aunty bazata shiga tsakanin uwa da ɗaba, ko Hajia Mama?”.
Ta ƙarishe mgnar tana kallon Hajia Mama daketa murmushi cikin jin daɗin tace.
“Haka kuma ɗa bazai shiga tsakanin ya da ƙanwaba,
Gaba ɗaya Jabeer ya kwace mana ke”.
Murmushi mai kama da dariya sukayi gaba ɗayansu lokacin da suka shiga cikin falon.

Shi dai Jabeer sai murmushi yakeyi.
Ya Jafar kuwa in yaga Jabeer na murmushi sai shima ya ɗanyi murmushi.
Aunty Juwairiyya ce ta ɗan kalli Batul dake gaida Umaymah sakin fuska tace.
“Matar ƙani yau tun safe ban jikiba”.
Wani irin murmushin jin daɗi tayi Allah yasani in Aunty Juwairiyya tace mata matar ƙani tana jin daɗi.
Cikin happy tace.
“Yau a kitchen na wuni inayiwa Umaymah girkinsu na larabawa”.
Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa.
“Yo ai na rigaki, dama girkin bare bari kikayi mata”.
Kanta ta ɗan juya takalli Sheykh Jabeer dake zaune kusa da Umaymah, in zaiyi mata mgna sai ya juya harce zuwa larabci.
A ranta take addu’o’in Allah ya nuna mata ranar da zata zauna kusa dashi haka a matsayin abar sonshi.
Tattausan Lips ɗin shi masu kama da kunnen fure ta kalla.
sunan jazir sai sheƙi sukeyi a cikin tattausan sajenshi da gemun tamkar an shafa musu mai.
Allah ya sani randa ta samu lips ɗin nan a matsayin mallakinta, tabbas sai ta kusan haɗiyesu.

Hajia Mama da kanta da ita da Aunty Juwairiyya ne suka rinƙa kawowa Umaymah abubuwan motsa baki yaran yar uwarta na zagaye da ita, Hibba ce yar autarta ta ƴar kimanin shekaru 16 kalli Jabeer cikin cikin sanyi tace.
“Hamma Jabeer Aunty Jazrah tace in gausheka, wai yaushe zamuje”.
Kanshi ya juyo ya ɗan kalli Hibba cikin son yarinyar yace.
“Hibba auta yaushe kikeso muje”.
Da sauri tace, sai na tambayi Aunty Jazrah”.
Murmushi yayi kana ya kalli Aunty Juwairiyya yace.
“A shigar mata da kayanta, a ƙara gyara mata masauƙinta, yafi fadar Jalaluddin kyau”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer kamar ba shi yayi mgmar ba.
Ita kuwa Umaymah da Hajia Mama hararanshi suka ɗanyi tare da cewa.
“Ai babu fadar da zatafi fadar shi kam, shinefa gatanka”.
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
“A a kam Allah ne gatana, shi kuma da yake son ayi ta ɗimata”.
Juwairiyya kanta tayi mamakin sakewar Jabeer sosai
Duk wanda ya ganshi zaiga tarin farin ciki tare dashi.

Nan dai suka zauna akayi ta hira.

Saida aka kira magriba ne, duk suka miƙe sukaje sukayi al’wala.

Batul kuwa tafi kowa farin cikin, zuwan Umaymah ko ba komai ta samu ganin Jabeer yadda take so.

Bayan an idar da sallan isha’i ne suka dawo masalacin.
A nan bisa dinnin area. Suka zauna nan sukaci abinci.

Koda suka gama ne, sunata hira a falon harda Jakadiyarsu.
Jabeer ne da yanzu ya fito falonshi cikin nitsuwa yace.
“Kai dan Allah ku barta ta huta mana”.
Sai ya kuma ɗan kalli Umaymah tare da cewa.
“Umaymah muje ki gaisa da Lamiɗo, ya kirani yanzu yanata min ihu a kunne wai yaji kin iso tunda yamma kuma ban kai mishi keba”.
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
“To muje”.
Hibba ce ta tashi da nufin binsu sai kuma ta zauna, jin Jabeer nace mata.
“Zauna Hibba saida safe kuje da Jalal.”
Sai ya kuma kalli Jakadiyarsu cikin taushin murya yace.
“Ummi muje”.
Itama da sauri ta miƙa.

A tare suka fito yana gaba Umaymah na binshi,
Jakadiyarsu na bayansu.
Suna tafe cikin jin daɗi ko ina yayi lib sai sanyin korayen ciyawi da furannin da dogayen bishiyoyin gwanda da ayaba da sukayiwa ko ina ƙawanya.

Suna isa ƙofar Gimbiya Aminatu da sauri.
Sallama ya basu hanya, wanda a ƙa’ida sai ya shiga ya nemawa mutun izinin shiga kafin ka shigo.
So amman Jabeer baida hijabi da sashin kakanin nashi,
shiyasa kai tsaye suka wuce.
Shiru babban falon babu kowa.
Haka yasa suka wuce sashin Lamiɗo, a hankali yayi sallama,
Cikin murmushin Lamiɗo ya amsa sallamar tare da cewa.
“Bismillah, ku shigo”.
Kusan a tare suka kutsa kai cikin tamfatsen falon nashi.

Wani irin kallo sukayiwa juna,
Ganin…!

                            By
           *GARKUWAR FULANI**MEVYASA? ME YAYI ZAFI SHI BA WUTABA? ME RIBARKU A CIKIN FIDDA LITTAFINA WOJE KU WATSASHI WA DUBBAN MUTANE? ME FA'IDAR HAKAN? NIYARKU KO TUNANIN KI, KADA WASU SUZO SU SAYA NE? A ZATONKI DANKU DAN KU ƁATA MIN RAINE? KO KUNA ZATON ZAKU HANANI SAMUN BINDA ALLAH YA RIGADA YA ƘADDARA YA RUBUTA RABO NANE?  Nayi matuƙar mamakin al'ummar Annabi, Ni a zatona a iya hasashena, idan mace dan Allah da Manzonsa da darajar iyayen na kai ƙololuwar makurar roƙonda duk musulmi zai yi min al'farmar abinda na roƙa! Sai dai abin tsoro ashe abin ba haka bane, to wannan abun shine kadai ya bani tsoro, lallai kam tabbas muna akiruzzaman. Ai na sani kuma kuma mutanen kirki waɗanda kuka sai littafina da zuciya ɗaya kun sani dole za'a fitar da littafi. Sabida ba kaina farauba kuma ba kaina ƙarauba. Sabida haka kuyi haƙuri, dan Allah kuyi haƙuri, kuyi haƙuri da abinda wasu daga cikinku keyi. Alhamdulillah tunda na'annabi basa ƙare wa, tunda har gobe saya akeyi, wasu suna ganin gana satan a gabansu, amman sai su kauda ido suzo gareni su biya kuɗinsu a sasu a group ina godiya gareku*

Bayan Allah da Manzonsa da darajar iyayen dana haɗa mutane dasu bani da wani tsumi ko dabarar tsira daga sharrin masu zuciyar da basu san girman Allah da Manzonsa da darajar iyayensu ba. Domin duniya gaba ɗaya tana fama da gubar irin waɗannan. Iya tsaro dai kamar na bankuna, to amman me ana samun masuyin kutse a ciki har suyi sata. Manyan kampanunnuka na duniya ma suna fuskantar ɓarayj yan kutse, hakama ƴan Film suke fama da wannan matsalar, to mu ma rubuta suwaye mu da zamu tsira dasu, Roƙona anan dan Allah da Manzonsa abar maimaita mgnar a cikin groups ɗin GARKUWA. Su masu fitarwa dai na fita haƙƙinsu tunda inai musu posting sau biyu a rana kamar yadda na faɗa, su sukaji suka gani suka fitar, to wannan can musu. Ina da mutanen da nake matuƙar ganin kimarsu da darajar su a SPG shiyasa, bazan tanka musuba.

Fatan al’khairi VIP groups ƴan dari uku ina al’fahari daku, kun bawa maras ɗa kunya, shiyasa tun forko nace Ni kune VIP na, duk da nasan kuma ɗin a cikinku tabbas akwai masu fiddawar, to amman dai naku baya zama illa kamar na SPG. Ina yinku ɗari bisa ɗari.

Wlh rubutu yafi sauƙi akan mu’amalat da wasu taƙadiran da yake jarabtan marubuta da mgna dasu, ya ilahi ya mujibadda’awati, kai ina jinjina muku marubuta fama da wasu mutanen, wato da a haɗaka mgn da wasu gwara kawai a baka renon shanu garke guda na wuni ɗaya, domin shi dabba yasan abinda ake kira da makiyayinsa, amman wasu mutanen basu san darajar Allah da Manzonsa ba bare iyayensu. Allah ya kyau. Allah ka haɗamu da mutanen kirki.

Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan layin 09097853276, ko ki turo dubu ɗaya ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button