GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ita kuwa Shatu cikin zafi ta kalli arniyar nan da tace mata wannan ma ai iskanci ne tace.
“A kul kada ki kuskura ki sake kira min iskanci a gabana, ke kika sanshi ba niba, ke kika taso cikinsa”.
Sai kuma ta juya harce cikin fillanci tace.
“Shegu masu wari”.
Sai kuma ta juyo ta fuskancesu da kyau, Haroon kuwa da Jalal ido suka zuba mata cikin mamaki.
Shima Jabeer idon ya zuba mata so yake yaji meyasata ihun nan.
Ita kuwa Shatu cikin sanyi ta fuskanci musulman ciki murya a ɗan tashe tace.
“Kada dai ku manta nace daku nakeyi masu hijabi sabida nasan kun san ma’anar Al’muslim akul muslim. Kun kuma san girma da daraja da kuma wanda ya faɗi hakan”.
Cikin gamsuwa duk suka ɗaga mata kai, rai a ƙuntace tace.
“To meyasa kuka bar waɗanan can bayin Allah’n a tozarce a yashe a maraba da baƙi koda dreesing na raunuka su bakuyi musuba, menene laifinsu, kawai dan sun kasance fulanin daji, shiyasa DOCTOR’S da Nurse’s kab bazaku jiƙansu ba”.
Cikin sanyi ɗaya daga cikinsu tace.
“Ayyah yanzuma can zamu tafi. Sabida sai yanzu Dim ya bamu umarni”.
Wani dogon tsaki taja tare da cewa.
“Daga baya kenan yau kwanansu goma cib babu wanda daya dubasu, sai da suka gama jigata”.
Tsaki arnan ciki sukaja tare da juyawa suka tafi.

A hankali Jalal ya juyo ya kalli Hammanshi da yake cewa.
“Rufe min ƙofa wannan ta cika min kunne da ihu”.
Da sauri yace to.
Haroon kuwa murmushi yayi tare da juyowa zai shiga ciki kafin Jalal ya rufe ƙofar.
Da sauri ta juyo jin takun mutun a bayanta,
Cikin muryar umarni tace wa Jalal.
“Kai mai kamar larabawa tsaya kada ka rufe ƙofar, Office ɗin na arne ne ko musulmi?”.
Cikin dariya Haroon yace.
“Na musulmi ne”.
Taku ta fara tare da nufo cikin Office ɗin.
Wani irin sunkuyawa Jabeer yayi ya kifa ƙirjinshi kan babban Glass table dake gabanshi, sabida ji yakeyi tamkar kan zuciyarshi take taku. Ji yakeyi zuciyarshi zata fashe tsabar yadda take bugawa da azaban ƙarfi yadda take ƙara matsoshi haka bugawa zuciyarshi ke ƙara tsananta.
Cikin mamaki ta zubawa Office ɗin ido. Office ne mai matukar girma da kyau da tsaruwa, kai bakace Dr Office bane in ba ɗan wannan gadon da labulanshi da sauran kayan aiyukansu ka ganiba.
Duk da sai sati-sati yake zuwa nan Office ɗin tsab-tsab sai wani irin sanyi da ƙamshi yakeyi, cikin taɓe fuska tace.
“Me hakan shima DOCTOR baida lfy ne? Kodai tsabar wulaƙanci ne?”.
Murmushi mai kama da dariya Haroon yayi sabida yasan babu abinda Jabeer ya tsana yake kuma tsoro kamar a tsaya a kanshi ana mgna da ƙarfi, yo shi ko a hankali kake mgna sai yace kana mishi ihu a kai bare kuma wannan da take tsaye a kusa dashi kuma tana mgna da ƙarfi cewa zaiyi haushi takeyi.”
Shi kuwa Sheykh Jabeer hannunshi yasa yana dafe ƙahon zuciyarshi da yakejin yana tsalle.

Rafi’a kuwa tsaye tayi a bakin ƙofar tana kallon ikon Allah.

Sauran Nurses ɗin kuwa suma, tuni sun tafi, maraba da baƙin.

Ita ko Shatu a hankali ta ƙara motsowa gaban table ɗin hannunta tasa ta bug…

????????????????tsawon shekaru labarin littafin GARKUWA yana kimtse a kaina da zuciyata. Ni kaina in na tunoshi sai nayi murmushi nayi shauƙi sarƙaƙiyarsa kan hanani baccin dare inyi ta nazartan lmrin lbrin GARKUWA, nakanji murmushi da daɗi in na tuna lbrin nakan zubda hawaye wasu lokutan wasu lokutan nakanji jikina yayi sanyi da rayuwar duniya, labarin Garkuwa bazaka ganeshi ba, sai in ka karantashi duk iya lbrin mai labartawa bazai labarta maka yadda komai yakeba, Uhummm Allah ya nuna mana ƙarshensa, salon soyayyar Sheykh ta musamman ce..

Masoyan Parvina kuna sani dariya.

Masoyan Shatu kuna burgeni.
Ina masoyan Boleru jinjinan girma gareku.

Masoyan Sheykh ina sonku,
Sheykh yana gaidaku.

Masoyan Jalal yace ku dena kallonshi.

Masoyan Umaymah tace ku tayata da addu’a Allah ya yaye musu matsalarsu.

Wai Ya Ba’ana baida masoya ne?
Allah sarki Ba’ana ina sonshi dan al’khairin da yayiwa Aysha a baya. To wai wane al’khairi yayi mata ne?

Littafin GARKUWA na kuɗine in kina buƙatan Normal group turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276. In kuma special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin dubu ɗaya rak ta asusun na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Masu turo katin mtn numbers ɗin zaki turo ba hotonba.

                            By
              *GARKUWAR FULANI*

Ta ɗan buga table ɗin, tare da cewa.
“Malam ka tashi kaje ka taimakawa yan uwanka musulmai! in kuma baka da lfy ne ka nemi bokaye irinka su duba lfyarka”.
Zuwa yanzu gaba ɗaya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne yakeji yana jujjuya mishi sabida yadda ta konkotsa glass table ɗin da kanshi ke kife a kai. Ga kuma sautin muryarta da yake jinshi har tsakiyar kanshi.
Da sauri ya ɗago kanshi tare da ware matsakaita kyawawan idanunshi na zaiba.
Cikin sauri Haroon ya matsoshi ganin idanunshi sun cika tab da ƙwalla sai sheƙi sukeyi alamun suna iya zubda ƙollan a ko wanne lokacin.
Cikin harɗewar murya ta larabci yacewa Haroon.
“Please ka fitar da ita a nan, ta matsa kaina zata fasa min dodon kunne”.

Ita kuwa Shatu cikin tarin mamaki da al’ajabi ta zaro manyan idanunta tare da cewa.
“Laaah!”. Sai kuma ta fara ɗan ja da baya tare da cewa.
“Afwan baka da lfy ne!?.” Wani irin fitinenne murmushi Haroon yayi tare da cewa.
“Eh baya jin daɗi ne, ɗan fita zamu kira wasu bokayen suzo su dubashi”.
Cikin sauri tace.
“Subahanallahi bokaye kuma?”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Yesss ba haka kikace ba, ya nemi bokaye ƴan uwanshi su dubashi”.
Kanta ta ɗan dafe tare da cewa.
“No kada ka munana min zato, ina nufin likita bokan turai ka gane ko?”.
Da sauri taja da baya ganin Jabeer ya miƙa tsaye da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tsayuwanta kusa dashi barazana ce ga zuciyarshi tabbas zata iya faso ƙirjinshi ta fito.
Ganin yadda ya haɗe fuska ya nuna mata hanyar fitane, yasa ta juya ta fita.

Shi kuwa Jabeer komawa yayi ya zauna tare da sauƙe wasu tagwayen ajiyan zuciya a jere a jere.
A hankali yake jin bugun zuciyarshin na ɗan dai-dai-ta kamar dai yadda yaji kafin ta shigo.

Sai kuma ya fara jin zuciyarshi na tsinkewa ras-ras kamar dai tana tsoron kada wani abu yayi nesa da itane.
“Ya ilahi ya mujibadda’awati ya hayyu ya ƙayyum”.
Sune kalaman da Jabeer yaketa maimatawa a saman lips ɗinshi.

Haroon kuwa wani irin kallo yakeyi ma Jabeer mai cike da nazari.

Jalal ma kallonshin yake cike da tarin mamaki duk da sun san baya son akeyin mgn da ƙarfi a kanshi, to amman idonshi bai taɓa ciko da hawaye ba, sai yau.

Ita kuwa Shatu, ido ta zubawa Rafi’a da ta tsareta da ido, cikin yin ƙasa da murya tace.
“Rafi’a dama, wannan shugaban tuzuran ƙasar nan, yana aiki anan asibitin gwamnatin jihar nema?”.
Kamo hannunta Rafi’a tayi tajata sukayi gaba.
Haroon kuwa dariya yayi sabida, duk da rage muryarta da tayi sunji abinda tace, sabida wurin da suke ɗin yanada amsa kuwar amo.

Cikin yin ƙasa da murya sosai Rafi’a tace.
“Garkuwa ki nitsufa ki rufa mana asiri, kin ko san waye wannan?!”.
Shiru sukayi dukansu lokacin da suka juyo wata kekyawar mata tana bawa wasu ƴan mata Nurses a ƙalla sun kai goma lbri.
Ido Rafi’a da Shatu suka zubama wannan matar cewa.
“Shi wannan Dr Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, ba kamar sauran mutane bane, shi mutunne da Allah yayi masa wasu baiwa da nasabobi masu tarin yawa”.
Wata ƴar kekyawar cikinsu ne ta ɗan lumshe ido tare da cewa.
“Allah ya sani Aunty ina sonshi, ina son wa’azin shi, muryarshi kawai in naji yana zuba larabci sai inji bani da sauran damuwa a duniya, sai dai shi kuma yana nan kamar dutse!”.
Da sauri Matar nan tace.
“Ai bazai yiwuba, wlh bazai taɓa kulakiba, duk nacinki da korkosarki, shiyasa wasu ke raɗe-raɗin shi waliyi ne!”.
Numfashin ta sauƙe tare da ci gaba da cewa.
“Duk matsayinki, kyanki, mulki, sarauta, gata, ilimi!. ko da meye kike taƙama dashi a duniya ya fiki abin”.
Kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa.
“Kawai dan shi jikan sarkine sai yafi mu komi?”.
Kanta ta jinjina tare da gyara zaman ta cikin sanyi tace.
“Ba haka bane. Bari kuji kaɗan daga cikin nasabarsa.
Kunga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani.
Yana ɗaya daga cikin manyan malam da Afirka gaba ɗaya take ji dashi.
Sabida a ƙiyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jiki da tarin ilimin addini kamarshi.
Tun yanada shekaru takwas a duniya ya haddaci al’ƙur’ani mai girma.
Sannan ya fara karatun littafai shine matashin da yakeda haddar hadisai zunzurutunsu a kanshi sama da dubu ashirin.
Kunji wannan darajeta da tasa ko manyan mutane suke girmama shi.
Sannan shi jinin Masarautar Joɗa ne ta wurin mahaifinshi.
Ta wurin mahaifiyarshi kuwa shi jinin sarki Jalaluddin ne, masarautar sarkin Musulmai.
Kana ta wurin kakarshi data haifi mamanshi. Asalin balarabiyar saudiya ce, wacce zuriyarta ne limamen Harami.
Kunga nasaba kan nasaba kenan.
In kyau ne na halitta, babu irin kyan da bai ganiba,
In kuwa kuɗine, ku leka ƙasan gidan saman nan zakuga ayarin motocin da sukayi mishi rakiya, to ko kakan nashi Lamiɗo motar da yake hawa bata kai ta Jabeer ba.
Uwa uba shi mutun ne da ya ƙoshi da sunna, baya son bidi’a.
Shi mutun ne wanda ya samu kekyawan zato a wurin mutanen duniya ake mishi shaidar salihi, mumini, mai tausayi.”
Da sauri suka ƙatseta da cewa.
“To Aunty meya hanashi yin aure har yanzu?”.
Cikin maida numfashi tace.
“Allahu alamu, sai dai ance kamar shi bana miji bane!”.
Cikin sauri wata tace.
“Kai mgnar. Duniya dan Allah kiji zancen ƴan shashi faɗi. Bita da ƙulli har an samo sharrin da aka liƙa mishi bawan Allah.”
Rafi’a kuwa kai ta jinjinawa Shatu alamun kinji ko, ita kuwa Shatu zuru tayi kamar makahon daya tsinka garaya”.
Cikin sauri wacce tace tana sonshin tace.
“Wlh ni dai ko shi bana miji bane zan iya zama dashi a hakan in da zai yarda muyi aure”.
A hankali Shatu ta gyara riƙon da tayiwa wayarta tana ɗaukar su video.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button