GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shi kuwa Jamil waya yakeyi da Khairat sabuwar budurwarshi.

A can baya kuwa Affan ne liƙe da waya a kunne yana mgna da Yusuf.

A motar Sheykh kuwa, shiru kakeji kowa da sabgar da yakeyi.
Shi zaune yake da kyau ya buɗe system ɗinshi yana wani aiki a ciki.

Hankalinshi duk yana kanta.
Ita kuwa Aysha wani irin farin ciki mai zaman kashi takeyi.
Shiyasa hankalinta kab yana kan rugagen Fulani da suke wucewa.
Murmushi mai baiyana shauƙinta da begen irin wuraren takeyi, yana tuno mata Rugar Bani, da sauran inda suka zauna.

Kana tana farin cikin bin wannan tafiyar ne ko zataga wani abin da ya shafi su Ya Gaini.

Ɗan juya kwayar idonshi yayi ya kalli inda take.
Hankalinta duk yana kan window.
Taɓe baki yayi kana ya maida idonshi kan fuskar na’urar tashi.

Wani babban rugar Jafun suka fara isa.

Rugar a cike take maƙil da maza da mata matasa da sofaffi

Bisa alumun sun san da wannan ziyar shiyasa basu fita kiwo ba.
Bayan sunyi parking ne.
Fadawan suka fara fitowa.
Sukazo sukayi buɗe wa sauran motocinsu.
Galadima ne ya fara fita kana gaba ɗaya su Jamil Jalal dasu Affan suka fito.

Ita kuwa Aysha da sauri ta yunƙura zata fita kasan cewar ta gefen da take aka buɗe.
Hannunshi yasa ya riƙo nata.
Da sauri ta juyo ta kalleshi cikin sanyi tace.
“Ba fita zamuyi ba?”.
Ido ya zubawa fuskarta yana kallon yadda take mgn da alamun tsiwa da tura baki.
Uhum wato yanzu ta worke tsiwar zata dawo.
Ya raya a ransa,
a zahiri kuma kai ya jujjuya mata, tare da ronƙofowa, kan cinyoyinta.
Hannunshi ya miƙa ya jawo marfin ya rufe.

Su Galadima kuwa kan zuwa sukayi suka zagaye motar tashi, suna jiran fitowarshi.

A hankali ya buɗe marfin dake kusa dashi.
Kana yasa ƙafarshi ta dama, ya fita.
Meda ƙofar yayi ya rufe ganin tana shirin fitowa.

Buɗe al’kyabbar jikinshi yayi kana ya gyara zamanta.
Bayanshi Galadima ya koma.
Sannan Jalal da abokanshi suka koma gefe-gefenshi.
Sauran ayari kuma suka rufa mishi baya.

Su kuwa can cikin taron fulanin da sauri Arɗo Maru ya miƙe da sauran ƙananan Arɗo na gefenshi,
kasan cewar shine Arɗon araɗabe na yankin gaba ɗaya.
Da sauri suka nufosu cikin mutumtaka da fara’a suka iso.
Hannu ya bawa Sheykh tare da nuna mishi hanyar shiga inda sukayi musu shimfiɗa can cikin manyan rufuna.
“Bismillah GARKUWAn mu, gatanmu a idon gwamnatin jiha data ƙasa, bismillah gacan wurin zama”.
Kanshi ya jinjina kana yabi bayanshi sauransu suka biyo bayanshi.

Bayan suna zauna ne, duk Arɗo’s ɗin suka zagayeshi ta gaba su Galadima da sauran tawagar kuma suna baya.
Kana dogorai kuma na tsaye.
Arɗon araɗabe kuwa, yana gabanshi.

Gyara zamanshi yayi ya fuskanci Arɗon araɗabe cikin tattausan lafazi yayi ɗan murmushi tare da cewa.
“Kuna lfy ko? ba wata matsalar ko?”.
Murmushi Arɗon araɗabe yayi tare da cewa.
“Lfy lau Alhamdulillah”.
Kanshi ya ɗan ɗago ya kallesu baki ɗayansu kana yace.
“Masha Allah. To Allah ya taimaka”.

Amin Amin sukace cike da jin daɗi, shi kuwa fuskantarsu yayi dukansu tare da cewa.
“Na kawo wannan ziyarar ne dan samar da Kekkyawar alaƙa da kauda fitina tsakanin makiyaya da manoma da sauran al’,lummar gari.
Ina al’fahari da dukanku biyu uku makiyaya manoma jama’ar gari.
Bana son wani sashin ya cutar da wani sashin.
Ina neman al’farma daku zauna lfy da manoma banda yi musu ɓarna akan haƙinsu.
su wahala su noma kusa dabobbin ku suci su taka kunsa ya tabbata baku da gskya duniya zata ɗaukemu masu tada zaune tsaye.
Amman ina kuka bari manoma suka tattara kayan amfaninsu sai ku nemi izinisu ku shiga kuyi kiwo a gona kinsu”.

Cikin gamsuwa da bayaninshi suka haɗa baki wurin cewa.
“In Sha Allahu zamu kiyaye,
bazaka samemu a layin masu tsokana ba mu nan Jafuna”.
Kanshi ya gyaɗa cikin gamsuwa kana yace.
“Muddin manomi ya neme ku da fitina ko wasu sauran gama gari kada ku tanka musu.
Ga number wayata zan baku koda yaushe kuka kira zata shiga.
Zan sanar da ƙungiyar MI YETTI ALLAH itace ƙungiyar dake kula da matsalolin makiyaya da manoma.
Sannan duk inda kuke akwai mambobinmu a garuruwan dake kusa daku zasu shiga lamarin.
Duk wanda aka samu da rashin gsky zai fuskaci Hukunci.
Kana Ƙungiyar TABITAL POOLAKU tana tare daku a cikin dukkan al’amuran ku.
Kiyaye shigar banza kamar dai yadda na ganku yanzu cikin manyan suturu shine abinda yafi dacewa damu a matsayinmu na musulmai”.

Cikin murmushin Arɗon araɗabe yace.
“Zamu kiyaye, kuma dama mu Jafunawa bamu ɗaya daga cikin ƙabilun dake yawo a daji da kiwo masu yaɗa barna.
Mu Jafunawa ko suturarmu ta banbanta data sauran makiyaya”.

Hannu ya bashi bayan ya basu number miƙewa sukayi tare.
Da musu godiya
Kana suka rakasu har wurin motocinsu, nan Galadima ya miƙa musu kyautan kuɗin taimakon da Sheykh ya ware musu.
Nan suka shiga suka tafi a jere kamar dai yadda sukazo.

Tafiya mai ɗan nisa sukayi kana suka dawo kan hanya.

Jihar Jigawa suka nufa,

Dan yana so a ƙalla dai a yau ya zauna da Arɗaɓen jihohi uku

Kamar yadda ya tattauna da Rugar forko hakama ta biyu.
Sun amshesu a mutunce.
Daga nan suka nufi jihar (Tsinako) Katsina.

Daji suka nausa karfe biyar dai-dai suka isa Rugar da Arɗon araɗabe nasu yake.

Dai-dai lokacin kuma gaba ɗaya makiyayan sunata dawowa kiwo.
Bayan sun fitone, suka nufi inda suke.

Cike da mamaki Sheykh da tawagarsa duk ke kallon mutanen wannan Rugar.
Gaba ɗayansu maza garin kitsone a kawunansu reras har kafaɗunsu.
Ga wasu irin guntayen wondunan yadin atampa na mata,
kana rigunan tashi kabi shanu a jikinsu.
Kowa ka gani da sanda a wuyanshi.

Ba yabo ba Fallasa suka marab cesu.
Bayan sun gaisa ne yayi musu jawabin abinda ya kawosu.
Ɗaya daga cikin Arɗo’s ɗin ne yace.
“To wannan shiga dai itace muka samu wurin iyaye da kakanni babu kuma abinda take mana mu ba a takure mikeba kamar yadda kace.
Sannan batun manoma kuma infa suka tsokanemu mu bazamu jira wata hukumar.
MI YETTI ALLAH da TABITAL POOLAKU ba.
Zamu rama”.
Murmushi Jalal yayi tare da cewa.
“In kunfi ƙarfin kungiyar ku ta mi YETTI ALLAH da TABITAL POOLAKU.
Tabbas bazakufi ƙarfi mu mu rundunar tawagar sojojin ƙasar ba.
Ku iye harshenku tabbatar da zaman lfy ne ya kawomu nan ba musuba kuma umarnine.”
Cike da mamaki Ya Hashim da Laminu da Sulaiman harma da Jamil suka zubawa Jalal ido.
Mgnarshi ta nuna cewa, shi sojane mai ƙarfin iko kenan.
Rigar dake jikinshi ta sama ya cire.
Sai ga rigar sojojin ƙasar Nigeria ta baiyana a jikinshi a saman kafaɗunshi.
Taurari biyu da kuma alamar Shaho colonel ne kenan.

Suma sauran abokanshi biyu rigunansu na sama suka cire.
Ganin hakane yasa waɗannan makiyayan sukayi ƙasa da kawunansu.

Shi kuwa Sheykh.
Gyara zamanshi tare da cewa.
“Zama lfy yafi zama ɗan sarki, inji bahaushe to, tabbas mu zauna lfy shine ci gabanmu.”
Sai kuma ya kalli Galadima dake gefenshi yace.
“Waɗannan mutanen a dasawa Rugarsu ayar tambaya.
Ku tashi mu tafi, in naji wani kuskure ko tsokana daga gareku tabbas zaku fuskanci fushin ƙungiyar mu, zamu kuma miƙaku hannun hukumar ƙasa.
In kuwa wasune suka tsokaneku ga number ta ku gaya min haƙiƙa zamubi kadunku bazan lamunci a cutar daku ba.”

Da sauri Arɗon Arɗaɓen ya biyo bayansu da sauran wasu dattawansu.
Haƙuri suka bashi tare da al’warin zaman lfy.
Kana bazasu bari ayi husumaba.

Da haka dai sukayi sallama suka tafi.
Madadin su kwana cikin jihar Tsinako indama sukeda cikekken ikon a masarautarsu Haroon ga uwa mai daraja Umaymah sai suka wuce jihar Noka bayan sunyi sallan mangriba da isha’i.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button