GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A can cikin makarantar kuwa,
Kasan cewar duk ɗaliban jami’ar sun san babban Doctor zai shigo yasa gaba ɗaya harabar asibitin dake cikin jama’ar cika da taron tsala-tsalan ƴan mata ƴaƴan manya, duk mai matsalar lfy tana fatan ya dubata sabida ƙwarewarsa.

A hankali wasu ƴan mata biyu suke taku a farfajiyar shiga asibitin, bisa alamu duka ɗayar bata da lfy dan ɗayar na rike da hannunta, kuma a hankali suke tafiya.

Cikin tausayawa ɗayar ta kalli wacce ta riƙewa hannun a hankali tace.
“Garkuwa ki daure kiyi sauri mu isa, wallahi zamu samu layi da yawa, kuma wannan Sheykh ɗin kasaitarsa nada tarin yawa, yanada doka da ƙa’idoji da tsari, yanada tsauri kan tsare kima da darajar addininshi, daga shigar jikinki in kinyi kuskure kaɗan na shigar kima wallahi bazai dubaki ba.
Shiyasa ahlul kitabi dake cikin makarantar nan suke masifar shakkarsa,
kinga gashi azahar ta kusa, kuma wallahi ko sarkin garin nanne yazo ya dubashi in dai lokacin salla yayi to tashi zaiyi ya fita ya barshi, gashi shiru-shiru da ido yake hukunta mutun”.

A hankali wacce aka kira da GARKUWA tasa hannu ta gyara niƙab ɗin dake fuskantar, wacce ta dace da wata kekyawar arabian gawn dake jikinta
wanda dama shigartace haka kullum sabida gudun kada wani ya ganta ya tsaida ita dan tasan duk namiji daya nuna yana sonta har lahira ake kasheshi wanda kuma duk Rugarsu akeda yaƙinin Ba’ana ne dan mutunne mai masifar baƙin kishi, yasha sanar mata a kanta zai kashe kowa ba damuwarsa bane da fari duk wanda ya nuna yana sonta da bulalin shaɗi yake korarshi, to yanzu duk wanda yace yana sonta sai dai a wayi gari ya rasu.
Cikin sanyin muryar dake nuna azabar da takeji, murya na rawa tace.
“Rafi’a, bazan iyaba marata ciwo kamar zata ɓalle, ki sakeni kije ki amsar mana foldana kafin in ƙaraso”.
Jin haka yasa Rafi’a cewa.
“Zaki iya tahowa ke ɗaya?”.
Kanta ta gyaɗa mata a hankali.
Hakan yasa cikin sanyi ta saketa kana ta wuce cikin Hospital ɗin da sauri.

Dai-dai lokacin kuma motar Dr Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ta kutso kanta cikin farfajiyar.
Bayan Ado ya dai-dai ta parking ne a cikin rumfar adana motor da aka rubuta Dr Jabeer a samanta.
Ado ne ya fito da sauri ya buɗewa, Sheykh marfin motar, a hankali ya zuro ƙafafunshi ya fito.
Cikin nitsuwa ya fara taku yana ratsowa cikin farfajiyar Hospital ɗin.
Kasan cewar ta gabas ya fito Aysha kuwa ta yamma ta fito sai ya zama suna fuskantar juna.
Yayinda sai sun haɗu wuri ɗaya zasuyi kwana sun fuskanci kudu inda nanne mashigar cikin asibitin.

A hankali suke takowa suna fuskantar juna.
Sosai ya zuba mata ido sabida ya lura gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi alamun tsananin ciwo takeji gashi a hankali take taku.
Ita kuwa Aysha, tafiya takeyi da kyer sabida azaban ciwo da mararta keyi.
Kanta a sunkuye take tafiya, hakan yasa bata san da mutunba a gabanta.

Da sauri Sheykh ya tsaya sabida wani irin bugawa da ƙirjinsa ya fara. Ganin ta tunkaroshi gadan-gadan, kuma daga yanayin tafiyarta tamkar zata faɗi ƙasa.
Ganin tayi wani irin sunkuyawa tasa hannunta duka biyu ta damƙe mararta da takeji tamkar caccakarsa akeyi da allura.

Gefe ya ɗan tsaya yana kallon ikon Allah, ita kuwa GARKUWA rumtse idanunta tayi da karfi, wata fitinenniyar zuface ke tsastsafowa tako ina,
a hankali ta fara buɗe idanunta jin kartan da mararta keyi ɗin yana ɗan lafawa,
a hankali ta zubawa kyawawan sawunshi idanu, cikin sauri ta ɗago kanta, ganinta tsaye gab kusa da namijin da bata saniba ne yasata ja da baya da sauri tare da miƙe tsawonta cikin firgici murya na ɗan rawa tace.
“I’m very sorry”.
Bai kulata ba, sai kauda kanshi da yayi gefe.
Ita kuwa Garkuwa cikin sanyi tace.
“Dan Allah kayi haƙuri”.
Kai ya ɗan gyaɗa mata alamar Uhumm.
Ita kuwa cikin sanyi tace.
“Uhumm kaima Doctor Sheykh ɗin kazo ganin ne?”.
Da mamaki ya ɗan kalleta da gefen idonshi, sai kuma ya ɗan juyo kanshi kaɗan jin muryarta a sanyaye taci gaba da cewa.
“Muyi sauri mu shiga ance yanada shegiyar ƙasaita da isa, wai ko sarkine yake dubawa in dai lokacin salla yayi tashi yakeyi ya fita”.
Cikin tarin mmki ya ɗan waro kyawan idanunshi tare da cewa.
“Umh”.
Ita kuwa Garkuwa, hannu tasa ta matse mararta tare da cewa.
“Muyi sauri mu shiga, kaga kuwa kayi sa’a kayi shigar mutunci dan ance shi baya son ganin musulmi da lalatacciyar shiga, ancema in mace tayi shigar banza baya dubata, kaji shishshigin mutunfa ko meye ruwansa da rayuwar wasu ai kowa yayi mai kyau dan kansa ko?”.
Rolling Ball eyes nashi yayi tare da gyaɗa mata kanshi.
Kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya.
Ita kuwa Garkuwa cikin yin ƙasa da murya tace.
“Uhum shidama akace shine shugaban tuzuran ƙasar nan, yana zaune baiyi aureba, ai zama ba aurema ba kyau tunda dai yanada damar yi ko?”.
Ɗan tsagaita takunshi yayi tare da cewa.
“Hummh”.
A hankali ta bishi a baya cikin yanayin muryar mara lfy tace.
“Dan Allah ka tsaya in rigaka shiga kar yace sai ya dubaka kafin ya dubani”.
Dai-dai lokacin kuma suka kutsa kansu cikin asibitin.
Da sauri Garkuwa ta zazzaro idanunta baki ɗaya, tare da dafe ƙirjinta ganin gaba ɗaya Nurses ɗin dake ƙoƙarin fitowa sunyi maza suka koma baya, tare da rusunawa suka haɗa baki wurin cewa.
“Barka da hantsi Sheykh”.
Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, har ya shiga cikin wani ɗan corridor ya shiga wanda zai sadashi da tamfatsetsen Office dinshi ba tare daya ratsa ta cikin Reception ɗin su ba.

Ita kuwa Garkuwa gaba ɗaya tsorone ya rufeta,
Gefen Rafi’a taje ta zauna wanda a take kuma mararta taci gaba da murɗawa da kartawa.

Da ƙarfi ta damƙi hannun Rafi’a.
Cikin tausayawa Rafi’a tace.
“Sannu, in sha Allah bazamu jimaba za’a kiraki, dan na nemi al’farman sauran sun yarda Khadija Nasir Shugaba ce aka shigar, ƴar gwamnan, ba lfy”.
Kai kawai ta iya gyaɗa mata, sai taune lips ɗinta da takeyi.

Shi kuwa Sheykh yana shiga Office dinshi, ya fara aikin daya kawoshi cikin ikon Allah kuwa Khadija ta samu sauƙi tunda ya dubata aka bata magunguna.

Mutun biyar ya duba, na shida kuwa, Aysha ce.

Koda aka kira sunanta jiki a mace ta miƙe ta nufi inda take ganin ana shiga.
Nurse namiji na gabanta.
A haka suka shiga,
Ajiyan zuciya taja a hankali sabida tsaruwa da kyau da tsabta da ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta, su sukasa ta son bin Office ɗin da kallo amman ina ciwo bazai bartaba.

A hankali ta iso gaban table ɗin baƙin Glass dake gabanshi.
Ɗaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table ɗin ta zauna.
Ƙasa tayi da kanta cikin tarin ciwo da fargaba.
Shiru tayi zaune bisa kujerar tayi ƙasa da kanta.
Shikuwa Sheykh ko kanshi bai ɗago ya kalli inda takeba wanda wannan al’adarsace da wuya ya kalli mutun, mafiya yawan lokuta yafi kallon mutun ta cikin gilashi table ɗinshi,
shiru Office ɗin sai sautin A/C da yake busawa, shima kanshi Nos ɗin sai ya gaza abin cewa,
Ita kuwa Aysha pat-pat haka zuciyarta ke duka, gashi tana jiyo mararta na fara kartawa.
Kusan tsawon 1 minute suna a haka, cikin dakiya da rauni ta ɗan nago kanta ta kalleshi,
Ga mamakinta sai taga asalima hankalinshi baya kanta, yana dai murza yatsunshi da alamun tasbihi yakeyi.
Shi kuwa Sheykh duk abinda takeyi yana ganinta ta kan glass ɗin,
Cikin sanyin murya tace.
“(Jam ɓanɗuna). Ina kwana”.
Shiru bai kulataba har sawon wasu daƙiƙun har ta fara zaton ko bai jita bane.
Da sauri ta ɗago kanta jin yayi mata magana, cikin wata sahihiyar murya a takaice yace.
“Suna?”.
Cikin fargaba ta tace.
“AYSHA ALIYU GARKUWA….!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button