GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

“Wonkan tsarkin”.
Ta bashi amsa ido a rufe.
shafa fuskarta yayi tare da cewa.
“Niyan wonkan me zakiyi”.

Idonta ta ƙara rumtsew wasu hawayen suka zubo a hankali tace.
“Wonkan Janaba”.
murmushi yayi mai faɗi kana yace.
“Eyeh Gud gerl, kin girma yanzu kin zama big gerl ai, tunda har wonkan Janaba ya hau kanki, sannu ko Aish Allah ya miki al’barka”.

Tafin hannunta tasa ta kare fuskarta.
Shi kuwa miƙewa yayi tare da cewa.
“Bari inje in ɗauko miki wasu kayan, ko in baki aron al’kyabbata?”.
A hankali tace.
“A a ɗauko min”.

To yace kana ya fita.

Ba kowa a falon, dan haka da sauri ya wuce falonta har bedroom.
drower’nta ya buɗe,
hannunsa yasa ya zaro wani abu da ya gani Royal blue shi kalan yabi.
Sai kuma ya samu ashe doguwar rigace ta shaddar wagambari mai masifar kyau.
daga ita bai kuma ɗaukan komaiba ya juya ya fita.

A babban falon ya samu Ummi tsaye,
cike da tsananin kunya ya sunkuyar da kanshi kana a hankali yace.
“Um Uhmm Barka da safiya Ummi”.
Ganin alamun kunya yasata kauda kanta kana tace.
“Barka dai Muhammad”.
Ci gaba da tafiya yayi.

Da ido ta rakashi, tana murmushin jin daɗin. Muhammad ɗinta ya zama cikekken magidanci,
daga yawau zasu fara hango nasarorinsu. Tabbas akwai kwan da zai fashe nan kusa a tsakiyar masararutar Joɗa.

Shi kuwa yana shiga bathroom ya sameta zaune bakin bathtub ɗin ta ɗaura towel a jikinta.

A hankali yasa hannunshin ya kamo nata ya tsaida ita, kana cikin sanyi yace.
“Wanne irin wonka kikayi?”.
A hankali tace.
“Da al’wala a haɗe”.

Na’am yace kana ya zira mata rigar.

Saida ya dai-dai-ta mata rigar kana ta kwance towel ɗin ta ɗaura ɗan kwalinta.

Sannan ya nuna mata hanyar fita da hannunshi.

A hankali ta ɗago ƙafarta ta taka, ido ta ɗan rumtse tare da cije laɓɓanta, kana ta ɗan ware ƙafafuwanta tare dacewa.
“Wash”.
Ido ya ƙurawa yadda take tafiyar.
Kanshi ya jinjina sannan a hankali ya biyota cikin kauda kai yace.
“Y.M.D.G ko dai kin ƙarune?”.
Shiru batayi mgna ba, sabida sosai takejin zafin.
Buɗe mata ƙofar yayi ta fita.
Da sauri yabi bayanta suka fito.

Sallaya ya shimfiɗa mata, tare da miƙo mata hijabinta, hannun ta miƙa zata amsa tana mai ɗan kallonshi.
yana kallonta yace.
“Kiyi salla sai in dubaki inaga ko na buɗa ƙofar da yawa.
Gwara in gani da wurin in na buɗata ne in ɗinketa”.
Hawayenda ya zubo mata sanadin rumtse idanunta ne, ta share da hijabin kana ta juya ta fuskanci al’ƙibila.

Shi kuwa Sheykh bakin gadon ya dawo, da nufin gyarawa yana janye blanket ɗin yayi maza ya maidashi tare da cewa.
“Subahanallahi har haka ta zubda jini”.
Gaba ɗaya tausayinta ya rufeshi wani irin abu na musamman yakeyi a kanta yana ratsa dukkan jikinshi da zuciyarsa.

Ita kuwa Aysha tana idarwa ta zauna tana sharce hawayenta dake silalowa tana mamakin wasu zantukan Yan Sheykh yana abu ko a jikinsa kamar bashi yayi wannan abun ba.

Tana shafa addu’a yace.
“Taso zo muje kici abinci in dubaki, tafiyar kin nan batayi minba, akwai matsala”.
A hankali ta yunƙura ta tashi dan tabbas yunwa ke son hallakata.

Da sauri ya isa gareta sabida ganin ta dafe kai ta rumtse idanunta tayi baya alamun zata faɗi.

Ruggumeta yayi a jikinsa tare da tallabe kanta.
Luuu yaga idanunta na tafiya alamun suma zatayi.
Murya can ƙasa tace.
“Yah Sheykh duhu nake gani, jiri nakeji kaina ciwoooo”.
Da sauri ya tallabota jikinshi.
Kan gadon babu inda zai ajiyeta dan haka ya wuce falo da ita.
Bisa 3 str ya kwantar da ita dai-dai lokacin kuma taja wani dogon numfashi ta fara wani irin karkarwa da rawan sanyi alamun tana gab da sume mishi.

Cikin ɗan ɗaga murya yake kiranta yana ɗan marin kumatunta.
“A’ish! A’ish!! A’ish!!! Tashi! Ummi! Ummi!!”. Ya ƙare kiran Ummi da ƙarfi dan gigice
Ummi dake bakin ƙofar falon zata shigo musu da breakfast ɗin su ne, tayi sallama tare da shigowa da sauri, bisa santa table ta ajiye tray’n tare da isowa inda suke a kiɗime tace.
“A subahanallahi Sheykh sata a jikinka, sata a jikinka”.
Da sauri ya jawota jikinshi ya ruggumeta gam-gam.
Ita kuwa Ummi gefe ta tsaya tana cewa.
“Subahanallahi”.
Kar-kar haka jikinta ke rawa har nashina na rawa.

Da sauri Ummi ta juya falon.
Wayarta ta ɗauka da sauri ta kira Dr Kubra tace suna buƙatar taimakon gaggawa.
To Dr Kubra tace kana ta fara shirin tahowa.

Ita kuwa Ummi falonshin ta koma.

Cikin mamaki ta iso kusa dasu.
Ganin jikin Aysha ya dena karkarwan ta kuma buɗe idonta.
a hankali ya sauƙe numfashi kana ya medata kan kujerar ya ajiyeta, sannan ya gyara zamanshi a hankali yace.
“A’ish”.
Kauda kanta tayi daga kallonshi ta kalli Ummi.
Cikin sanyi da disashewar muryar tace.
“Ummi yunwa nakeji, kaina ciwo jiri nakeji’.
Da sauri Ummi ta ɗauki cup kunun kanwan nan mai haɗin mazarƙwaila da citta kanamfari.
Ta zuba a kofin da yakeda da girma saida ta cikashi.
Kana ta matso kusa da ita,
kofin ta miƙa mata, amsa tayi da sauri takai bakinta.
Kafa kanta tayi ta fara sha, tanayi tana ɗan cire kofin dan zafin kunun.
Shi kuwa Sheykh matsawa gefe yayi, ya fara daddanan wayarsa idonshi kuma na kanta, kunyar Ummi ya sashi ɗan matsawa.

Ita kuwa Ummi sannu take yiwa Aysha. Da sauri ta juyo ta kalli Sheykh jin yana ce mata.
“Ummi Abba yace ki kaiwa Lamiɗo beshit”.
Cikin kauda kai tace to.

Ta lura kunyar ta kusa tasashi ya maida kanshi cikin wayar da yake dannawan.

Kai tsaye bedroom ɗin ta nufa.
Cike da farin ciki take kallon shimfiɗan.
Ture blanket ɗin tayi ta haɗe beshit ɗin kana, ta shimfiɗa blanket ɗin, sannan ta fito.

A falon ta wucesu yana sunkuye kamar yadda ta barshi yana danna wayarsa,
Ita kuwa Aysha kunun take sha, tana mai jin daɗin shi a bakinta.

Kai tsaye Side ɗin Sarki Nuruddeen ta wuce.
Har cikin ɗakin Gimbiya Aminatu ta wuce.

Durƙusawa gaban Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
“Allah hokke sabbugo Ga tabbacin tantanin Aysha uwar gidan Sheykh.”
Wani sihirtaccen Murmushi Gimbiya Aminatu tayi kana ta tashi zaune daga kishingidar da take, cike da farin ciki tace.
“Alhamdulillah mafarki mu nata dabbata kamar yadda muke dako, yau Allah ya nuna mana dare mai cike da ruwan sama da walƙiya da rugugin tsawa.
Kana ga tabbacin kyakkyawan budurcin bafullatanar daji, zantu kan malam Musa na baiyana ɗaya bayan ɗaya.”
Sai kuma ta kalli zanin gadon da jinin ya ɓatashi sosai.
Cikin ƙasaita tace.
“Maza a haɗa tukuicin budurci, domin ta bawa Jabeer kyauta mai tsada a bata tukuici mai girma.”
To Ummi tace kana ta miƙe ta fita ta nufi ɗakin tukuicin.

A can Side ɗinsa kuwa, bayan ta shanye kunun sai ta koma ta konta bisa kujerar tayi lib, wani irin zufane yake tsastsafo mata tako ina na jikinta limshe ido tayi tana jin raɗaɗin jikinta.

Shi kuwa Sheykh da alamun wani abu mai mahimmanci yakeyi a wayarsa.
Koda ya ɗago kai yaga ta lumshe idonta sai yayi zaton ko bacci tayi.

Gimbiya Aminatu da Lamiɗo da Galadima ne zaune a falon Lamiɗo,
Ummi na zaune a gabanta da wasu manyan ƙore da daro irin nada.
Cikin girmamawa ta jawo ƙwaryar dake kusa da ita,
A hankali ta fiddo wasu manyan al’kyabba irin na matan sarakuna guda uku.
sai kuma ta fiddo wasu kekyawawan yan kunne da sarƙa mai masifar kyau, na gold.

Wasu aworworo ta fiddo na asalin azurfan masarautar Joɗa, wanda yake da sirruka,
domin matuƙar mutun mayene in ya leshesu zaiyi bayani da kansa.

murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
“Tun bayan Ayshancan ba, sake danƙawa wata mace sarƙar tamɓarin Masarautar Joɗa ba, gashi da ita dashi duk basu tsira ba.
Ina fargabar a sake baiyana wani a ahlinta.
kada tarihi ya maimaita kanshi.
Murmushi Lamiɗo yayi kana yace.
“In Sha Allah babu komai fashe al’kyairin Allah, Magauta sunyi tasu nasarar sun gama, yanzu lokacin masu gaskiya ne”.
Shiru Abba yayi yana jin kalaman iyayen nashi, suna masu uzzuro mishi ciwon dake zuciyarshi.
Galadima kuwa kwalin babban ashanan da Ummi ta buɗe wanda yake cike tab da ƴaƴan ashana ya kalla tare da yin murmushi.
Wannan itace babbar shaidar mace in ta kawo budurcinta gidan mijinta a masarautar Joɗa.
Shine asa kwalin ashanan a cikashi tab da yayansa, in kuma bata kawo budurcinta ba, sai a zazzage ya’yan ashanar asa fonko haka ba ɗa ko ɗaya a ciki.
Kuma za’abi sashi-sashi na Masarautar a nuna kowa shaida to indai anga fonko babu ɗa a ciki to shaidar ta zubda budurcinta a woje.
Ci gaba da ɗaga kayayyakin Ummi tayi.
tana nuna musu.
Ɗaya daro ta jawo shi kuwa, silke ne da sirdi a ciki sai linzamin doki, kana sai takalman hawa doki kala biyu na mace dana miji,
sai kuma ɗaya kwaryan cike yake da gero sai citta da kanamfari sai kwalin sugar irin mai ƴaƴan nan.
Kai ta ɗan ɗago ta kallesu tare da cewa.
“Ga haɗin kayan da dawakai biyu mace da namiji ɗaya macen na Aysha ɗaya namijin na Sheykh.
Sai kuma kyautar zabbi ashirin na jinyar Aysha daga Masarautar Joɗa.”
Cikin jin daɗi Gimbiya Aminatu tace.
“Masha Allah. Allah ya sanya al’khairi, kira yan rakiyarki su rakaki ku nunawa kowa dake Masarautar Joɗa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button