GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Bayan kusan mitinu goma, sai ga hayaƙin nan ya bar fitowa,
Sai wani irin huci.
Da sauri Jabeer yace.
“Nifa zan tafi, inma kun mance in tuna muku yau jumma’a ace, inada abinda yafi wannan abun naku mahimmanci a rayuwata ta duniya da ƙiyama, yanzu gashi har kusan sha biyu.”
Murmushi sukayi baki ɗayansu ba tare da sunce mishi komaiba.
Sabida dama sun san za’ayi haka kam.
Sabida kowa ya sani shi Jabeer yana barranta da duk irin waɗannan ababen gado na sarauta shiyasa sarautar kanta shi bata ɗaɗashi da ƙasa ba.

Da sauri ya buɗe siraran idanunshi da kyau.
Sabida ganin wani irin ƙaton maciji ya sako kanshi cikin babban ramin da yafi girma.

Da sauri yace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun!.”
Sai kuma ya zubawa maciyar nan idanu.
Tana fitowa cikin ramin ta, zuɗuɗuɗuɗuɗu. Haka yake zaro jikinshi.
Haƙiƙa dole duk wanda bai taɓa ganin macijinba bai kuma san da zamanshi ba, dole ya razana.
Dan ma shi zuciyarshi na cike da tsoron Allah so irin wadannan ababen ba kasafai suke firgitashiba.
tashinsa fahimtar ko wani ɗan abin sihirin za’ayi mishi ne.
Wani dagon numfashi yaja mai ƙarfi ya sauƙe ganin. Yadda macijiyarna taketa keta fitowa taƙi ƙarewa.
Su dai su Lamiɗo shiru sukayi a zaune.
Saida ta gama fitowane, ya rage iya bindinta sai gashi ta fito bindinta na kananmaɗe da wasu irin kitsastsun bulalin da ka gansu kasan tsoffine.
A hankali ya turo bindinshi gaban Lamiɗo,
Ya ajiyesu, sai kuma ya sumkuyo da kanshi ya zaro harshensa ya rinƙa lasar bulalin nan saida suka fito ras kamar an wonkesu.
Kana ta juya ta nufi cikin curin zuɗuɗuɗuɗuɗu ta koma,
Kamar forko sai ga hayaƙin.

Wani nannauyan numfashi Jabeer ya sauƙe tare da cewa.
“Uhum inda ranka kasha kallo. Oh ni Muhammad Jabeer an ɗauramin jakar tsaba za’a jazamin kaji su bini su tsastsageni.
Du wai wadannan abubuwan na menene wai dan Allah”.
Ya ƙarishe mgnar yana kallonsu baki ɗayansu,
fuskarshi cike da alamun fargaban gudun saɓawa ubamgijinshi.

Su kuwa saida hayaƙin ya gama ɓacewa baki ɗaya sannan Lamiɗo ya fara miƙewa kana suma duk suka miƙa.
Sarkin Shaɗi ruggume da bulalin.

Juyawa sukayi zasu nufi hanyar da zata ɓullo ta falon Lamiɗo,
da sauri ya ɗan motsosu tare da cewa.
“Dan Allah shi wannan abun me amfanin zamanshi a nan? Wurinda Kum san duk baƙin da suke zuwa tako wani sashi na duniya ganin abin tarihin masarautar Joɗa muna kawosu nan.
Yanzu in wata ran yunwa ta koroshi ya fito ya cutar da mutane fa me zakuce?”.
Cikin ƙosawa da mgnar Galadima ya gyara riƙon da yayiwa sandarsa cikin sanyi yace.
“Bata tare da yunwa, macijiyar da duk wata sai an ajiye mata motar ƙwai a cikashi da kiret-kiret na ƙwai shine abincinsa”.
Da sauri Galadima ya nufi hanyar fita.
Lamiɗo kuwa tuni sun tafi.

Ganin sun tafi sun barshi a nan a tsayene. Yasashi sauƙe numfashin tare da juyawa ya nufi, ƙofar da zata sadashi da falonshi.

A hankali yake taku, cikin kasala da mutuwar jiki, da mgnar zuci.
“Wai ya zanyine? Wanna wacce irinyar masifeffiyar rayuwace? Yaushe zamu samu Allah ya gama tsarkake mana wannan masarautar Joɗa ya rabata da wadannan tsarabe-tsaraben gargaji.
Wannan wacce iriyar fitinace?”.
Dogon numfashi yaja lokacin da ya shigo falonshi,
babu kowa, can babban falo ma babu kowa bisa dukkan alamu duk sunje shirin sallan jumma’a ne.

A hankali ya kutsa kai cikin bedroom ɗin shi.
Kai tsaye bathroom ya wuce.
Jallabiyar jikinshi da hirami da vest ɗin ya cire,
Cillasu yayi cikin injin wonki.
A hankali yake taku kanshi a sunkuye dagashi sai boxes Sky blue.
A hankali ya shiga cikin wurin wonkan.
Kamar yadda ya saba haka yayi wonkan jumma’a anshi.

Bayan ya fitone ya nufi drower’n glass ɗin dake cikin bathroom ɗin.
Wani tattausan Baby towel ya ɗauka bisa saman kafaɗunshi ya ɗauri ya fara gogewa, yana tsane ruwan jikinshi.
Kana a hankali ya ɗauki wanni babban towel ɗin ya ɗaura daga saman ƙirjinshi.
Wanda ya sauƙo har guiwa shi, a hankali yasa hannun ta ciki ya fara murza boxes ɗin yayi ƙasa, dashi yana zuwa sharabanshi ya riƙe shi ya zare ƙafa ɗaya, kana ya zare ɗayar ma.
Lallaɓeshi yayi ya matse kana ya shanyashi kan ƙarfin silver da yake na shanya.
Farar jallabiya ya zura a jikinshi, kana ya kwance towel ɗin. Dashi ya goge suman kanshi.

Cikin hamzari ya fito bedroom,
Kai tsaye gaban dreesing mirror ya nufa, mai ya shafa a dukkan sashin jikinshi. Kana ya taje tattausan suman kanshi tare da shafa mishi manshi, wani Duaol jannah mai masifar daɗi ya shafawa jikinsa, kana ya ɗauki wani ƙaramin kum ya tace tattausan sajenshi ya kontar dashi lib-lib hakama gemunshi.

Saida ya gama komai na gaban Mirror kana ya nufi babban drower’nshi da sauri-sauri yakeyin komai.
Wani tattausan jallabiya mai masifar kyau da taushi fari ƙal ya zaro.
Kana ya ɗan yi sama da kanshi ya kalli cikin tsep ɗin ƙarshe na drower’n inda al’kyabbanshi suke jere a kimtse tamkar shagon saidasu.
Hannu yasa ya zaro wata sabuwa dal tana cikin ledanta tana haɗe da hiramin ta da komai.
Rufe wannan wurin yayi kana, ya buɗe wani sashin inda ƙananan kayan shi ke jere, boxes and singlet ya zaro farara ƙal suma sabbi ne.
Da sauri ya rufe drower’n kana yazo ya ajiyesu bakin gadonshi.
Ba tare da ya cire jallabiyar jikinshi ba, ya saka boxes ɗinshi saida ya dai-dai-ta zamanta a jikinshi da kyau ya kimtsa komai nashi yadda zaiji daɗi tafiya, kana ya zare jallabiyar ya ajiyeta bakin gadon
Singlet ɗin ya yasa, sannan ya ɗauki farar tattausar jallabiya mai dogon hannun ya saka, jallabiyar daya cire ya ɗauka ya gaban ƙaton drower’n nashi ya nufa, wani side ɗin ya buɗe nan ya saƙalata.
Kana ya dawo bakin gadon.
Ledan al’kyabbar ya farka da ƙarfi da kuma sauri sabida ganin tuni ƙarfe ɗaya da rabi tayi, yasan yanzu masallacin ya cika maƙil da mutane.
Ɗan gajeren tsaki yaja, tare da ci gaba da warware al’kyabbar.
Yana gamawa ya zurata a jikinshi, al’kyabbar baƙace, sai gefen bakinta da akayiwa kolliya da wani zare mai masifar kyau Golding color irin mai sheƙi da ɗaukar ido, hakama, kan kafaɗunsa har zuwa hannunta anja zirin irin wannan kolliyar.
da sauri ya dai-dai-ta zamanta a jikinshi, kana
Ya juya ya nufi, gaban dreesing mirror da hiraminshi a hannunshi,
Yana isa ya ajiye baƙin abin, kana ya ware farin hiramin shima da kolliyar Golding color a jikinshi, ya ninkeshi kamar yadda muke ninke dankwali, bayan ya gama ne.
Ya ɗaurashi a kanshi ya dai-dai-ta zamanshi kana, ya ɗauki baƙin abin wanda shima an zagayeshi da Golding color ya sakashi a akanshi, ya fito ras tamkar a Saudia.
Allah ya sani yana masifar son wannan shigar da jin daɗinta a jikinshi babu takura babu matsi gashi ka suturtu da kyau mayu masu kallon tsiya irinsu Jazrahda Batool duk basa iya ganin komai a jikinshi ba.

Da sauri ya nufi wurin aje takalma shi wanda yake na glass ne marfin ya buɗe kana, ya ɗauki wasu takalma irin nasu na sarauta Golding color ne kuma half cover ne, zura jajayen sawunshi yayi a ciki, kana ya koma gaban mirror, wani kolba turaren OudKareem mai masifar ƙamshi mai sanyi, ya fesa a duk sashin jikinsa.
Kana yasa hannunshi ya ɗauki carbinshi. Farin galashi ɗan siriri ya manna a idonshi.
Kana ya juyo da sauri zai fita, sai kuma ya tsaya cike da mamakin ganin. Haroon tsaye ya zuba mishi ido.
Ya buɗi baki zaiyi faɗa sai kuma yayi shiru jin Haroon na cewa.
“Kada kace zakayi faɗa Lamiɗo ne yace inzo in kiraka, lokaci na tafiya fa.”
Bai kulashi ba kawai yayi gaba, da sauri Haroon ya bishi tare da cewa.
“Wannan baza ƙamshi haka sai kace wurin amarya zakaje, gsky kayi kyau sosai masha Allah”.
Bai kula Haroon ba sabida addu’o’in da yakeyi.
Amman duk da haka saida ya bawa Haroon amsa a zuciyarshi, yake cewa.
“Akwai wani wuri da yafi cancanta da ɗan adam yayi shiga ta tsabta da kyan shiga da ƙamshi sama da masallacin ne? Innal masajida lillafa, duk duniya da babu wurin da Allah ya keɓanta yace dakinshine sai masallatai. Nan zamu gana dashi. Domin idan mu bama ganinshi ai shi yana ganin mu”.
Murmushi Haroon yayi, dan Jabeer bai san mgnar da yakeyi a zuci ta fito filiba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button