GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Hajia Mama na biye da ita.
Ita kuwa Salma tana ganin fitansu ta ruggume mijinta.

Koda suka koma Side ɗin Hajia Mama bata daɗe a nanba ta nufi sashin Gimbiya Aminatu.

To bata fito nan ɗinba sai shabiyu saura.
Koda ta dawo Haroon da Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya kawai ta samu a falon.
Sai kuma Jalal da Hibba da suke dinning area suna zaune bisa kujerun Dinning table ɗin.
Sun sa plet a tsakiyarsu da kofunan tea a hannunsu, alamun sai yanzu sukeyin breakfast.

Cikin kula Aunty Juwairiyya tacewa Ƙanwar mahaifinta ɗin.
“Umaymah muje kuci abinci rana tayi fa”.
Murmushi tayi tare da son danne ɓacin ranta tace.
“Alhamdulillah Juwairiyya Ni kuma da nakeda Hajia Mama ga Gimbiya Aminatu, ai naci nayi nak.”
Cikin sauri Jakadiyarsu ta e.
“Ga kuma Matar Barrister Kamal ma ta aiko miki abin kari.
Gimbiya Saudatu ma ta aiko miki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“A ajiye minshi sai anjima, kinga Juwairiyya kada ki shiga kitchen yau kizo mu wuni hira abinmu, abinci tako ina zaizo”.
Cikin sanyi Juwairiyya tace.
“Uhummm Umaymah ke har zaki iya cin abinci waɗanan mutane ai Gimbiya Saudatu ba abin wuya bane tasa mana guba muci duk mu mutu.
Sai dai muci na gidan Barrister”.
Kai Jakadiyarsu ta jinjina alamun eh.

Cikin ɗan ɗaga murya Umaymah tace.
“Haroon!.”
Da sauri ya amsa tare da tahowa inda take.
Gefenta ya zauna tare da cewa.
“Umaymah gani”.
Ba tare da ta kalleshiba tace.
“Ina Jazlaan?”.
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Y shiga Garden”.
Kai ta ɗan jinjina mishi tare da zubawa Jalal ido.
Ita Hibba sai murmushi takeyi shi kuma fuskarshi kamar boss.

A hankali ta miƙa ta nufi falon Jabeer ɗin.

Da sauri ta kalli Haroon tare da cewa.
“Ina zakaje”.
Baki ya ɗan tura tare da cewa.
“Umaymah inda zakije mana”.
Cikin tsokana tace
“Sirri zanyi da ɗan”.
Tana faɗin haka ta juya ta nufi can. Shima Haroon yana biye da ita a baya.

A hankali take taku har ta isa inda yake.
Gefenshi ta zauna tare da zuba mishi ido.
Cikin kula tace.
“Jazlaan”.
Cikim nitsuwa ya buɗe idonshi tare da kallon inda tarin tsuntsayen nan suke,
Lokaci ɗaya idanunshi suka kaɗa sukayi jazir.
lips ɗinshi ya fara motsawa da nufin yin mgna amman ya gagara,
sai wani irin kuka mai ƙarfi da yake son ƙawance mishi daga can ƙasan zuciyarsa.
Hakan yasa lips ɗinshi karkarwa tamkar mai jin sanyi.
Umaymah kuwa. Tuni hawaye sun wonke mata fuskarta tana mai kallon tsuntsayen.

Ganin Haroon yasa tayi mishi alamun ya kawo mata ruwa.
Ba musu ya juya ba tare da yayi mgn ba jim kaɗan ya dawo da goran ruwa da glass cup. Ruwan ya tsiyaya a kofin ya miƙa Umaymah.
Cikin sanyin murya tace.
“Ga ruwan sanyi kasha, nasan zakaji sanyin ƙunan da kakeji a ranka”.
Ta ƙare shi mgnar tana miƙa mishi cup ɗin.
Amsa yayi yayinda gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi alamun tsananin tarin baƙin ciki duniya.

Da kyar ya iya shan rabin kofin.
Nan ta gyara zamanta tare da kamo hannunshi ta fara tausar zuciyarshi kan abinda tasan shine babban matsalarshi.

A garin Bani kuwa zuwa yanzu hankali ƙabilar ɓachama yayi matsifar tashi, tsoro mai tsanani ya rufesu.
Tsoron da yasa da yawansu suka rinƙa guduwa suna koma cikin babban birnin Ɓadamaya,
Wasu kuma su tafi wasu jihohin.
Sabida sun gama tsinkewa da goron gaiyata da fulani keta raɓawa babu dare babu rana birni da ƙauye duk inda suka san fulani na nan sai da suka aika musu goro
Wannan ne yasa mafiya yawan kafuran aran na kare.

Inda hakan ya fusata Habban Ɓacama.
Har ta kaishi ga cewa, duk ba ɓacamen da yasan tsoron fulanine ya sashi guduwa to kada ya kuskura ya sake dawo mishi garinshi garin Shikan.
To wannan abun shiyasa wasu suka fasa guduwa, wasu da basuyi nisaba suka dawo.

To kuma kwatsam sai gashi yau an aiko an karɓin sandar sarautar Shikan dake hannunshi
Wannan abun yasa da yawa mutanen cikin Shikan Maza da mata hausa fulani da Ɓacamawa da sauran ƙabilu suka kuma rinƙa fecewa sabida, suna ganin yanzu dai shi kanshi Sarki Shikan bashi da madafa bashi da ƙarfi tunda an karɓe sandar sarautar shi.

To hakane yasa, ya rinka bin ƙauyuka Especially mutanen Bonon da kewaye ya rinƙa zugasu da ingiza su cewa, nanfa garinsu ne ya zasuyi su gudu kan Fulani.
Kuma ma suda sukeda dodon tsafinsu Bonon ai shi kadai ya ishi fulanin.
Da haka yasa duk ƙabilun Ɓacamawa na ƙauyukan basu guduba.
Sunata shirin faɗa yayinda cikin garin Shikan kuma yayi shal ko ina shiru babu mutane.

Cikin garin Bani kuwa, iya tsoronsu da suka gani a cikin kafuran ya sasu jin daɗi tunda gashi har suna guduwa subar garin da suke musu gadara da gori a kanshi da cika bakin sai sun kori Fulani a garuruwansu.
To tabbas sunada nasara akan fansar da zasu ɗauka, zasu ramane dan nemawa kansu enci.
Sun san iya sau ɗaya in sun nunawa arnatakun nan zasu iya gwabzawa dasu zasu barsu su sarara.

Haka yasa suke jin ƙarfin guiwar yin abun.

Ba’ana kuwa yanata ƙara shirya kanshi, sabida ramuwar gasar da za’ayi.

Ya Salmanu kuwa yanzu ya fara jajir cewa, yana fakewa da jarumtar Jabeer yana gasawa Ba’ana maganganu.

Sosai ya ƙara shigewa Shatu a mako ɗayan nan.
Kuma tana jin daɗin hakan.
Ta sake sosai.
Zuwa yanzu kuma jikin Ummey yayi sauƙi garawau sai dai har yau bata taɓa yin mgna ba ta zama tamkar kurma.

Da dare bayan sallan isha’i,
tana zsune ita da ya Salmanu suna hira cikin nitsuwa tace.
“Ya Salmanu gobene zamuje asibiti mu dubo su Junaidu da sauran marasa lfy dake cikin Genaral Hospital Ɓadawaya, dan naji ƙishin-kishin ɗin wai har yanzu babu likitan daya dubasu.”
Cikin gamsuwa da hakan yace.
“Eh hakan yana da kyau, kuje in sha Allah muma jibi asabar zamuyi gamgami muje, danma goben jumma’a ne da munje tare”.
Sai kuma ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Da yaushe zakuje?”.
Cikin sanyi tace.
“Da safe zamuje, in anyi sallan azahar zan dawo, amman Rafi’a zata wuce makaranta”.
yace.
“To ke sai yaushe zaki koma?”.
“Sai Ummey ta ɗan ƙara samun sauƙi. Ni da na so mu kaita asibiti kan batun rashin mgnar tata.
Gyara zaman shi yayi tare da cewa.
“Wannan ba matsala bace, wlh firgici da tsoro ne yasata hakan”.
Haka dai sukaci gaba da hirarsu.

Washe gari ranar jumma’a, misalin karfe sha biyu dai-dai suka fito zasu tafi asibitin.

A bakin lambun garinsu sukayi kiciɓis da Ba’ana nan ya tsaidata dole suka zauna.

A can cikin masarautar Joɗa kuwa,
Lamiɗo, Galadima, Sarkin Shaɗi, da Jabeer ne tafe a hankali suka shiga cikin Garden ɗin nan.
Ta gefen Lamiɗo, suna shiga suka nufi inda katon curin dake wurin shekara da shekaru.
Shi dai Jabeer binsu yakeyi baiyi magana ba,
Koda suka isa wurin zama sukayi dabas a ƙasa.
Dole shima ya zauna, cikin sanyi Lamiɗo yace.
“Assalamu alaikum Jaimi”.
Da mamaki Jabeer ya kalleshi,
Hiraminshi ya gyara tare da cewa.
“To yau kuma”.
Da sauri Galadima yasa hannunshi ya rufe mishi bakinshi.
Hannunshi yasa ya janye hannun Galadima tare da cewa.
“Yo ai ba sai ka rufe min bakiba, in kace nayi shiruma zanyi, sai dai ina naga abin saɓon Allah ko tsireni za’ayi sai na faɗa”.
Dafe kai Galadima yayi tare da tsuke fuskarsa.
Ganin haka ya taɓe baki tare da ɗaga kafaɗunshi ya ɗan buɗasu alamar, ban damuba.

Sarkin Shaɗi kuwa bai kallesu bama.

Wani irin zabura Jabeer yayi cikin tsananin firgici da kaɗuwa lokacin da yaga wani irin h ….!

                           By
            *GARKUWAR FULANI*Ganin wani irin hayaƙi fari tas yana fitowa, tako wacce ƙofa na jikin curin.

Da sauri Galadima yasa hannunshi ya kamo hannun Jabeer yaja da ƙarfi.
Alamun ya nitsu ya zauna, cikin mamaki ya zubawa tarin hayaƙin dake bulbulowa daga ƙofofin ramin shirgegen curin.
Su kuwa ga ɗayansu hankali konce suke zaune.
Ido ya zuba musu tare da cewa.
“Me hakan?”.
Da sauri Lamiɗo ya girgiza mishi kai hakanne ya sashi jan gajeren tsaki tare da cewa.
“Nifa ba son wannan soki burusun naku da surkunlenku nakeyi ba. Me gamina da ku da tsare-tsaren naku. Fisabilillahi me wannan?”.
Cikin faɗa Lamiɗo ya sa hannu zai bugi bakinshi da sauri ya kauce.
Cikin hatsala Lamiɗo yace.
“Wannan bakin naka da baya mutuwa, komai sai kayi inkarin a kai tabbas sai na kashe bakin nan”.
Wani kallo yayi mishi tare da cewa.
“Uhumm ai babu mai kashe bakin Muhammad Jabeer sai Allah”.
Ganin zaija suma suyi surutune ya sasu kauda idonsu kanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button