GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Sosai kuwa Shatu tasha gyara na musamman daga wurin Ummi da Mameynta.

A can ƙasar Cameroon kuwa.
Ba’ana ya gama shirin dawowarsa kab.

Wanda da azatonsa zai kaishi watanni uku sai gashi cikin wata biyu ya gama shirinsa.
Kana ya kamo hanya.

Yau Alhamis da misalin ƙarfe tara na dare yayiwa Rugar Bani diran miki…!

Ban samu nayi editing ba

                               By
              *GARKUWAR FULANI*[4/3, 8:36 PM] +234 806 559 0880: Dirar mikiya tare da tawagar shi wanda Baroon na ciki.

A bakin titi motar ta sauƙesu kana suka ƙaraso cikin Rugar tasu da ƙafa.
Dai-dai bakin mashigar Rugar Bani ɗin suka tsaya, sabida ganin uban gayan tafiyar ya tsaya.
A hankali ya lumshe idonshi, tare da shaƙan sassayan iskan garin dake kaɗawa yana ratsa jiki.
Hannunshi ya buɗe ya waresu, ya tanƙwashe kansa bisa wuyanshi cikin muryar dake nuni da gskyar abin dake binne can ƙasan zuciyarsa yace.
“Uhummmmmmm ko wani ɗan adam yanada yanki na musamman da yake cikin bugun zuciyarsa.
Ni kuwa Rugar Bani ce bugun zuciya ta.
RUGAR BANI itace mahaɗin soyayya da Mata. Allah ka sani kaine ma sannin sirrin zuciyata ina son Shatu son da ni kaina ban san adadinshi ba.
Son da bana yiwa kaina shi.
Mata itace cikon farin cikina ban taɓa son wani abu a duniya sama da Shatu ba ya Allah ka yafe min kura-kuraina na baya, ka bani ikon samun Shatu, ka tsare min imanina duk da nasan.
Ban fiye aikata aiyukan gsky ba a rayuwata.
Amman son Shatu gsky ne a cikin zuciyata kuma tuban da nayi gsky ne.
Ya Allah ka jiƙaina ka tausaya min ka cika min burina ka ƙaddara Mata ta tabbata matar aure na, in rayu da ita inuwa ɗaya.
Domin itace sanyin idaniyata in ka samar min ita rayuwata zata inƙanta.”
Ya ƙarashe mgnar cikin rauni da rawan muryar kana wasu irin tafasassun hawaye suna masu kwarya mishi.

Sheykh kuwa dake jin duk abinda Ba’ana yake faɗa bisa kiran da Baroon yayi mishi.
Da ƙarfi ya rumtse idanunshi, yana mai jin wani irin azabebben kishi mai masifar zafi da ƙuna yana caccakar zuciyarsa.

So yake ya tashi yaje suyi hira da Mamey’nshi Amman gaba ɗaya yanayi shi ya hautsine kishi ajalin maza.
Domin in mu mata kumallonmu ne tofa su maza yakan iya karsu.

A can Rugar Bani kuwa, cikin rauni Ba’ana yaci gaba da magana cikin sanyin jiki da raunin da bai taɓa riskar shi ba yace.
“Na sani na yarda akan komai ni bazan amsa sunan mai gsky ba ko mai tausayi amman akan tubana da Shatu ni mai gsky ne! Ya Allah ka mallaka min Shatu na yarda na gane babu wani sihiri ko tsafi ko boka ko dodon tsafin da zai mallaka min ita sai kai sarkin da bashi da tamka sarki buwayi gagara misali sarkin kowa na Annabi baban zara”.
Kawai sai ga hawaye shar-shar suna kwaranya daga idanunsa rusunawa yayi ya durƙusa bisa guiwowinsa ya kafa kanshi cikin sassayan yashin garin.
Ya saki wani irin raunataccen kuka.

Gaba ɗaya yaran nashi shiru sukayi cikin tarin mamaki da tsantsar gaskata soyayya ba ƙarya bace shirya kuma ta Allah ce dan tuni sun san yabar komai na tsafi saidai wasu abubuwan dake jikinsa basu karyeba kamar ɓacewa har yanzu yana iya ɓacewa.

Saida yayi kuka mai tarin yawa kana suka miƙe suka nufi cikin gari.

A tsakiyar wurin garken al’ummar Rugar Bani ɗin ya tsaya ya juya gabas da yamma kudu da arewa.
Kana a hankali yace.
“Duk da son hanaku ci gaba da nakeyi, ya rigada Allah ya lamunce muku kuna ci gaba da izininsa.”

Kai tsaye garken Bappa ya nufa bayan duk ya sallamesu sai Baroon kawai.
A hankali yasa ƙafarshi ya ratsa tsakiyar garken cikin ɗan ɗaga murya yace.
“Bappa”.
Cikin wani irin masifeffen tashin hankali da firgici Bappa ya miƙa tsaye.
Tare da cewa.
“Na’am Ba’ana”.

Giɗi da Seyo ne dake gefenshi suma suka miƙe da sauri cike da tsoron me zai faru.

A hankali ya zame ya zauna gaban Bappa kana a hankali yace.
“A nan a tsakiyar garken nan na rayu da ita tsawon shekaru goma sha biyu, na rayu da sonta kan gsky.
Koda komai ƙaryane Bappa ka yarda ina son Shatu son da bana yiwa kaina”.
Cikin sauƙe ajiyan zuciya Bappa ya zauna jiki a mace hakama su Gidi da Baroon.
Cikin nitsuwa yace.
“Ba’ana yaushe ka dawo?”.
Murya na rawa yace.
“Bappa yanzu na shigo Rugar Bani ko gidanmu ban jeba, ina so ka yarda cewa da gaske ina son Shatu”.
Yadda yayi mgnar yasa Bappa jin wani irin rauni da tausayinsa a hankali yace.
“Na yarda Ba’ana na sani kana son Shatu”.
Da sauri yace.
“Bappa ka tuna kun min al’ƙawarin aura min ita”.
Da sauri Bappa yace.
“Na tuna Ba’ana ban manceba to amman al’ƙawarin Allah ya ture namu ya rigada Allah ya tsara Shatu ba matarka bace.”
Cikin sauri ya miƙe yana cewa.
“A’a a’a bana son jin haka”.
Yana faɗin haka yana yarfa hannun a haka ya nufi cikin gari Baroon na biye dashi a baya.

Shiru Bappa da su Giɗi sukayi cikin tarin rauni.

Shi kuwa Ba’ana a tsakiyar gidansu ya zauna gaban Bukar da Bugulu mahaifiyarshi.
Cike da mamaki suke kallonsa jin yadda yake kuka babu sassauci.
Cikin tsananin tausayi da so irin na iyaye da yaransu.
Sukayi kanshi cikin kula Bugulu tace.
“Ba’ana yau ranar farin cikine a garemu ba ranar kuka ba.
Kada kayi kuka muna cikin farin cikin ganin juna”.
Ba mgn sai kuka.
Da sauri Bukar ya jawoshi jikinshi tare da cewa.
“Gaya min me ya saka kuka haka?”.
Cike da rauni yace.
“Karo na forko dai a rayuwata Baba zan roƙeku in kuna da hali ku aura min Shatu ku dawo da ita gareni”.
Ganin tsananin tashin hankali da yake cikine yasa sukace.
“To kwantar da hankalinka ina shine kawai burinka zamu dawo maka da farin cikin ka”.
Da sauri yace.
“Allah Baba?”.
Kai ya gyaɗa mishi cikin tausayinsa.
Shi kuwa jin hakane ya zame ya kwanta ya ɗaura kansa bisa cinyar babanshi yana sauƙe numfashin kuka shima Baroon gefe ya zauna.

Sheykh kuwa cikin tsananin tashin hankali na kishi ya rumtse idanunshi da ƙarfi.
Kana ya taune lip ɗinsa na ƙasa.

Shatu ce zaune ita da Mamey har cikin ɗakinta Afreen na hannun Ummi.
A hankali Mamey tace.
“Shatu”.
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli Mamey tare da cewa.
“Na’am Mamey na”.
Gyara zama tayi tare da cewa.
“Shatu batun mijinki ne, nake son kisa baki a lamuransa”.
A hankali tace.
“Mamey waɗannen lamuran ne?”.

“Shin kina son Mijinki ya mulki masarautar Joɗa?”.
Ta jefa mata tambayar kai tsaye.
Da sauri Shatu ta zubawa Ummey nata ido ta karanci yanayinta na ƴan wasu daƙiƙu kana a hankali tace.
“Mamey in dai kuna so ya mulka to nima zanso, hakan sai dai ina tsoro kada a sabautamu”.
Da sauri Abba dake shigowa yace.
“A’a Shatu in sha Allah babu komai babu abinda zai faru sai al’khairi.
Burinmu ya mulki masarautar Joɗa ne dan ya gyara ta zama Tsarkakkiyar masarauta mai wadatar sunna da ƙarancin al’adun bidi’a”.
A hankali ta gyaɗa kanta tare da cewa.
“Shi kenan Abba Allah ya sanya al’khairi yasa hakan ya zama ci gaba ga Musulunci da musulmai”.
Amin Amin sukace.
Kana ta ɗan yunƙura zata tashi.
Ganin Abba ya shigo yana amsar Afreen tare da cewa.
“Ƴar lukuta”.
Murmushi tayi kana ta kalli Mamey dake cewa.
“Ki fara nuna mishi amfanin ya mulki masarautar bisa hikima ta yadda zaki sa mishi abin a ransa ba tare da yaji dole akayi mishi ba”.
Da sauri tace.
“Toh Ummeyna”.
Har ta isa bakin ƙofar kuma sai ta tsaya jin Mameyn na cewa.
“Umurnine fa Shatu ki fara daga yau”.
Ajiyan zuciya mai sauƙi ta sauƙe tare da cewa.
“In sha Allah kuwa Mamey”.
Tana fita Ummi na biye da ita a baya.

A bakin ƙofar shigowa suka haɗu da Sheykh shida Affan.
Wuce sukayi kana su kuma suka fita.

Kai tsaye har bedroom ɗin suka wuce.
Suna hira ta tsakanin iyaye da yaransu.
Da sauri Sheykh ya ɗan ɗago ya kalli Mameynshi tare da sakin murmushi jin tana cewa.
“Jabeer wannan gemun haka ka ɗan rageshi mana ga saje ga gemu”.
A hankali yace.
“Mamey bai min kyau bane?”.
Da sauri tace.
“A’a wlh yayi maka kyau sosai ma fiye da zaton mai zato sai dai yasa kayi kwarjini da yawa ni kaina sai inji kana min kwarjini”.
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
“Uwa mai daɗi Allah ya bar mana ke Mameynmu”.
Dariya Abba da Affan sukayi tare zubawa Sheykh ɗin ido jin yana cewa.
“Toh gemu da saje ku kiyayi kanku da sa Mameyn Jabeer ganin kwarjini mai yawa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button