GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Zuwa yanzu hankalin kafuran ƙabilar ɓachama ya yi masifar tashi domin wannan shine karo na forko a rayuwar tarihin Ba’ana da ya zana mutun bulalin shaɗi har talatin da takwas baiyi ihuba bai zubda hawayeba, bai sumaba, bai faɗi ba, bai guduba.
Kai wannan abun yayi tsamari wannan wanne irin mutum ne, anya kuwa mutun ne ko al’jan.

Ya Salmanu kuwa, cikin tsanani kuka cur-cur da hawayenshi sabida yasan azabar da Sheykh Jabeer yakeji.
Juyawa yayi ya fuskanci gabas, sujjada yayi tare da fashewa da wani masifeffen kuka mai cike da rauni murya na rawa yake cewa.
“Ya Haiyu ya ƙaiyum, ya ziljalali wal ikram. Ya Allah ka ƙarawa wannan bawa naka dauriya da jarumta, ya Allah ka bashi ikon jure wannan azabar, ya ubangiji ka sanyaya mishi masifun dake jikin waɗanan bulalin, ya ubangijin taliƙai ka hana wannan mugun mushirkin bawa naka samun nasara, ya Allah ka kare musulminka kan wannan kafurin matsafin da baya salla”.
Kuka sosai ne yaci ƙarfin Ya Salmanu.

Bappa ma wani irin raunine ya rufeshi tabbas kowa zaiyi tunanin Jabeer yana jin azabar duniya.
Sai dai kasan cewarsa Jarumin namiji haka yasa babu wata alama da ya nuna na yana jin zafi ko ciwo.
Sosai kuwa hakan ya tada hankalin kafuran.

Lamido da Galadima kuwa kallon juna sukayi tare da yin murmushi irin nasu na manyan fada, murmushi ne mai manufofi.

Jalal kam kife kansa yayi a cinyar Lamiɗo ya saki kuka mai sauti.

Haroon ma hawaye yakeyi zuwa yanzu.
Hankalin duk tawagar Lamiɗo yayi masifar tashi, ganin yadda wani irin azabebben zufa ya tsinkowa Jabeer tun daga tsakiyar kanshi, zufar nan take gangarowa har kan jikinshi gaba ɗaya, saida ya jiƙe yayi jilak tamkar an kwaza mishi ruwa bokati ɗaya.
Wani irin karkarwa jikin shi, ya farayi yana tsuma yana ɓari, gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi.
wanda duk fulanin wurin suka fahimci cewa tabbas.
Zai iya cinye gasar zai kuma iya faɗuwa.

Shi kuwa Sheykh Jabeer daga can cikin naman jikinshi yake jin jikinshi na rawa tamkar mazari.
Zuciyarshi kuwa wani irin duka takeyi, wanda muddin kana kusa dashi zakaji yadda take bada sautin harbawa.

Hankalin Ba’ana yayi ƙololuwar tashi, ganin har yayi mishi bulala ta arba’in da biyar.
Baiyi ɗaya daga cikin ababen da zai hanashi cin gasar ba.
Ganin hakane ya juya a fusashe, bulalin hannunshin ya wurgar kana ya sunkuyo kam ranɗar bulalin tsafinshi, bulali biyar ya zaro, ya haɗa su ya damƙesu cikin hannunshi.
Cikin azaban ƙarfi ya ɗagosu ya yarfawa Jabeer su a tsakiyar kanshi.
Wani irin azabane ya ziyarci ƙoƙon ranshi, wanda hakan yasa yaji wani irin fitsarin azaba yana cika mishi mara.
Jinine ya tsinko ta kafaɗunshi, yana bin cikinshi,
bai gama jin azabar waɗannan ba ya kuma zarma mishi su a cinyoyinshi.
Da sauri Arɗo Bani ya miƙa tsaye daga sujjadar da yayi jin ihun mutane, suna cewa.
“Ka karya dokar gasa ba’a haɗa bulali biyuma bare biyar kasheshi zakayine.
Cikin wani irin isa ta jarumta da jinin sarauta Sheykh ya buɗe kwayar jajayen idanunshi,
Barmuji da yayi kansu da nufin kama hannun Ba’ana ne,
Ya ɗagawa hannunsa alamun daka dakatarwa alamun ya tsaya kada ya iso ya bar Ba’ana yayi komai ba komai.
Cikin tsananin mamaki duk al’ummar wurin suka zuba musu ido ganin jarumta ziraran miraran tana tsaye da sawunta.
Shi kuwa Barmuji cikin rauni yaci gaba da nufosu yana cewa.
“A a Sheykh bazan barshi ba, ai ya karya ƙaida da dokan gasa”.
Ya ƙarashe mgnar yana isowa inda suke.
Cikin tsananin takaici da firgicin ganin faɗuwa a karo na forko na rayuwarshi, Ba’ana
Ya zargawa Barmuji bulalin da ƙarfi.
Wani azabebben ihu Barmuji ya narka tare da fara tsalle yana yarfa hannunshi yana zagaya wurin hawaye na shatata mishi sabida azabar da yakeji, cikin ihun azaban bulalin da aka yarfa mishi sau ɗaya, fitsari na tsiyaya a sawunshi yace.
“Arba’in da takwas!”.
Ta gabanshi ya dawo ya shauɗa mishi na arba’in da tara, wanda yasa Jamil yin tsalle yazo gabanshi cikin kuka yace.
“Kasheshi zakayi ne?”. Cikin tsananin azabar da yakeji ne ya buɗe jajayen idanunshi ya kalli ta inda yaji muryar Jamil.
Hannunshi yasa ya ture Jamil gefenshi.
Shi kuwa Ba’ana wani irin ihu yayi tare da buga tsalle yayi sama kana ya zabga mishi bulala ta hamsin kuma ta ƙarshe.
Wani irin dogon numfashi Jabeer yaja tare da buɗe idonshi kan fuskar Lamiɗo daya iso hango dishi-dishinsa yana nufo inda suke.
Wani irin ihu da karaji Ya Salmanu ya kurma da azaban ƙarfi,
Wanda ya haɗe ya gauraye da busar sarewa da al’gaita da dukan gamgar jami, aka saki a tare.
Wani irin sowa da ihu da hargowane ya cika illahirin gaba ɗaya Rugar Bani,
Wanda mutane fulani suketa rawan farin cikin jarumtar Jabeer,
Arɗo Bani da sauran dattawan rugar kuwa gaba ɗaya sujjadar godiya sukayi wa Ubangijinmu sarki gagara misali.
Gaba ɗaya an zagaye Sheykh Jabeer.
Wanda shi kuma ya juyawa Haroon baya alamun yasa mishi suturarsa.
Da tsananin rawan jiki.
Haroon ya wore al’kyabbar, ya zura mishi ita kan jikinshi daketa zubda jini.
Yana jin Haroon ya saka mishi Al’kyabbar ya ɗago kafaɗunshi ya gyara zaman al’kyabbar.
Jiki na rawa yasa hannunshi ya kama gefe da gefen bakin al’kyabbar ya hadesu a jikinshi ya suturce kanshi ya kare kanshi.
Barmuji na shirin kamo hannunshi yayi maza.
Ya ɗaga mishi hannunshin kana ya juya ya nufi inda motoncinsu ke jere.
Jalal da na ganin haka yayi maza yayi gabanshi.
Marfin motar ya buɗe mushi tun kafin ya iso.

Cikin taron kuwa, tuni Ba’ana da matasan ƙabilar ɓachama, sun ɗauki ranɗar bulalin tsafinshi sun nufi Bonon da tarin baƙin ci dan ganin Sheykh Jabeer bai faɗi gasarba, kuma ga mutanen fulani daketa yi musu dariya da ihun rashin nasarar su.
Hakan yasa suka tafi dan sun sani a ƙa’ida sai Jabeer yayi jinya ya worke da azabar da Ba’ana ya shayar dashi kafin ya dawo ɗaukar fansa.

Cikin taron kuwa cikin kukan rauni Arɗo bani ya rusuna gaban Lamiɗo da tawagarsa murya na rawa yace.
“Sauran ɗaukar fansar da zaiyi a duk sanda ya worke a duk sanda yaga dama, fatana kuyi shirya bulalin tarihin masarautarku, domin ramuwa akan wancan taƙadirin da baya jin koda harbin bindiga baya shigarsa.
Ina yakun farin cikin nasarar da Jabeer yayi a yau, ina kuma fatan yayi nasara a ramuwar da zaiyi a wannan kuma in yayi nasarar mu zaku taya farin ciki, ko ba komai zamu rabu da wancan taƙaɗirin.”
Cikin wani irin tarin ƙuna Lamiɗo ya gyaɗa kanshi.
Kana ya juya yayi gaba Dogari na rike masa da laima ɗanzagi na cewa.
“Gyara kimtsi, a bada hanya, sarki ya barku lfy”.
Waziri da Wambai Ɗan buram Ɗurɓi Da iya duk suka mara mishi baya.

Hakama Arɗo Bani da sauran dottawan wajen sukayo musu rakiya.
Sheykh Jabeer kuwa.
Yana tafe Galadima na biye dashi a baya. Haroon kuma na gefenshi.
Suna isa yasa kai ya shiga cikin motar,
kana Haroon da Hashim suka mara mishi baya, da sauri sarkin mota ya maida ƙofar ya rufe.
Kana ya buɗewa Lamiɗo motar, gefen bayansu Jabeer ya shiga, kana Galadima ya shiga kusa dashi, sannan aka rufe motar saura duk kowa ya shiga motar da yazo ciki.
Sannan duk suka rurrufe motocin.

Kana suma Fadawa da dogarai suka shiga nasu motoci biyun.
Ɗaya tayi gaba, sauran motocin suka bisu a baya, ta Lamiɗo na tsakiyarsu, kana ɗaya ta fadawan ta biyo bayan uku da ke bin bayan ta Lamiɗo.

A haka suka ja motocin a jere a jere suka bar cikin Rugar Bani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button