GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shi kuwa Sheykh ƙara tsuke fuskarsa yayi ganin Batool cikin sauri ya gaida Mama, ta amsa fuska a sake tare da sanya masa al’barka.

Kana ya nufi hanyar fita, da sauri Jafar yabi bayanshi.

Umaymah kuwa da Ummi da Juwairiyya da Batool nan suka zauna suna ɗan hirarsu.

Jalal kuwa da Jamil a tare suka fita, shi kuwa Haroon falon Jabeer ya koma.

Yana shiga ya kira Jannart bayan sun gaisa take tambayarshi yaushe zai je masarautarsu nan yake ce mata.
Yana nan tafe a satin nan.

Shi kuwa Sheykh Jabeer yana fita kai tsaye Valli Hospital ya nufa.

Asibitinshi mai zaman kanshi.
Asibitin da duk nahiyar Ɓadamaya babu kamarshi.
Asibitin da in kana cikinsa zakayi zaton a ƙasashen turawa kake.

Haka lamarin yaci gaba da tafiya.
Babu mai yiwa Sheykh Jabeer batun Aysha.
Itama Aysha gani take kamar ziyara tazo ba aureba.
Tunda ita dai da idonta bata taɓa ganin mijinba, sai dai taji sunanshi.

Sosai ta shaƙu da Hibba da Umaymah, hakama Gimbiya Aminatu da Ummi.

Lokuta da dama takan shiga Bathroom tai ta kuka sabida begen ƴan uwanta.

Yau kwananta uku cur a gidan.
Idonta ma baiga ranaba.

Umaymah kuwa a sashin Jabeer yana fita.
Wata tirela ta iso har bakin Side ɗin shi.
Nan aka fara sauƙo da kayayyakin ɗaki na amare.
Ana shigarwa ciki. Kana masu aiki na ɗaure komai suna kimtsashi.

Sai kusan la’asar suka gama komai kafin.
Suka tafi kana su Umaymah suka taho.

Suna shiga asalin babban falon, Aunty Juwairiyya da Hibba suka haɗa baki wurin cewa.
“Wow masha Allah, Kai Umaymah ƙara so da sauri kiga falon nan yadda ya zama fadar masarauta”.
Da sauri Umaymah da Ummi suka ƙara so.
Masha Allah! Masha Allah!! Masha Allah!!! Shine abinda kawai Umaymah keta mai-mai tawa, sabida kyau da tsaruwan falon yayi masifar kyau.

Kasan cewar falon irin ƙaton nanne mai faɗi da tsawo.
Wasu irin kujeru ne Daimond set masu masifar kyau da tsada, a shirya a cikin tamfatsen falon.masu Golding color mai ɗan karen sheƙi sai surkin Brown color mai sheƙin gaske da ratsin ruwan madara..
Kana haka ma kalan labuyen falon masu tsawo da faɗi da taushin gaske.sai wani table na glass mai Golding color da aka ajiye a tsakiyar falon bisa wani tattausan carpet mai azabar kyau.
Sai wani babban Tv dake liƙe a jikin bongon, kana gefen dama kuwa wani babban majigine manne wanda yake baiyana rubutun Kur’ani reras daki daki.

Can gefen kuwa steps ɗin hawa Dinning area ne,
wanda aka canza Dinning table and chairs ɗin,
Aka zuba wasu masu masifar kyau da tsadan gaske.

Ba’a wani cika falon da tarkace ba, amman yayi matuƙar kyau.

Tafiya kaɗan zakayi ta gefen hakun zaka ratsa cikin wani madaidaicin falo.
Yayinda na Jabeer yake hannun dama.
falon ɗakin da Umaymah ke tsauƙa in tazo kenan.
2 bedroom ne wannan falon yake dashi ko wanne da bathroom a ciki.
Kana sai Dinning area matsakaici daga nan gefen Dinning area kuma akwai ɗan ƙaramin corridor wanda zai sadaka da kitchen da store.
wasu irin datsa-datsan kujeru masu masifar kyau da ɗaukar hankali aka kimtsa a falon wanda komai na ciki.
Peach and white coffee ne mai ɗan karen kyau.
Hakama Dinning table and chairs ɗin.
Still labulayen ma hakane.

Sai kuma cikin bedroom ɗin wanda duk girmansu ɗaya, haka yasa aka shirya wasu tagwayen gadaje masu masifar kyau suma Golding color ne mai sheƙi da ɗaukar ido.

Saɓanin side ɗin Jabeer komai Sky blue and white ne, wanda hakan yasa kana shiga sashinsa sai kayi zaton a sararin samaniya kake rayuwa.

Komai yayi kyau.
Especially kitchen ɗin dake matsakaicin falon.

Domin wancan kitchen ɗin dake babban falon ba’a taɓa shi ba, hakama Side ɗin Sheykh.

Sai kuma sama wanda shi a rufe yakema, sam babu kowa a ciki.

Sosai fa su Umaymah suka yaba da kyan shirin da akayiwa wurin.

Nan suka zauna a falon.
Umaymah ce ta kalli Jakadiya cikin sauƙe numfashin tace.
“Alhamdulillah, gobe kuma zakiyi musu jagora shida matarshi su zaga ta gaida ahlin masarautar Joɗa, ta gansu su ganta su san juna, gudun kada a haɗu a wani wurin ba’a san junaba”.
Wani gwauron numfashin Ummi ta sauke tare da cewa.
“A nan gizo ke tsakar ko ta ya zamu samu, Sheykh yayi wannan al’adar yadda ya dace ake kuma yinta, kinsanshi mutunne mai kunya, koda yana son abunma bare ba wani son abun yakeyi ba”.
Cikin yarda da kai Umaymah tace.
“Kada ki damu yana ɗaya daga cikin dalilin da yasani, na zauna sai naga kamun ludeyin zaman nasu.”

Haka dai suketa tattaunawa,
Suna nan zaune Gimbiya Saudatu ta shigo tare da hadimanta, kana da Laminu da Baba Basiru da Baba Nasiru.
Cikin isa da ƙasaita ta nufi kujerar da duk canjin da akayiwa falon ba’a canzashi ba sabida kujerace ta masarautar Jalaluddin, cikin isa take taku yayinda ta bawa ƙofar shiga baya.
Cikin gatsali ta kalli Umaymah data tsareta da ido. Kallon uku saura tayi mata kana tace.
“Duk mutun muna fuki abin tsorone. Amman munafurcin balaraben Mutun yafi na kowa muni da bada tsoro.
In banda salon munafurci ayi aure yau kwana uku a gaza fito da amarya a nunata ga mutanen masarauta, bare a fanshi idonta.”
Ta ƙarishe mgnar tana kai mazaunanta bisa, Kujerar.
Sai kuma tayi maza ta miƙa, jin muryar Jabeer da yanzu ya shigo, ko mgnar ta, ta ƙarshe baijiba.
Cikin isa da ƙasaita da rashin tsoronta, da kuma tsare fuska alamun Ni bani da lokacin ki, kuma ni ba sa’an yinki bane ya nuna mata hanyar fita da yatsarshi tare da yamutsa fuska cike da ƙarfin zuciya ya kalleta ita da ƙannen Mahaifin nashi yace.
“Fice min daga gida, bacci na dawo zanyi so banda lokacin jin ihunku na kar…!

               By
        *GARKUWAR FULANI*

“Muhammad!”. Ya kira babban sunanshi tare da jawo hannunshi, ya zaunar dashi bisa kujerar da ya tashi a kai.
Cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoron abinda suke shirin aikatawa, ya kalli Mahaifin nashi, kana ya juyo ya kalli Lamiɗo da Galadima gefen damanshi ya juyo ya kalli Jadda cikin rauni ya kuma kalli mahaifin nashi tare dayin ƙasa da murya yace.
“Abba kada ka bari su ɗaura auren nan, dan Allah kace musu su bari, kada su ɗaura”.
Ya ƙarishe mgnar cikin tashin hankali da ɓacin rai da tarin rauni a fuskarshi.
Cikin zuba mishi ido Abbanshi yace.
“Meyasa? Sabida me za’a bari!? Meyasa baka so!?.”
Kanshi ya jujjuya tare da haɗe hannayenshi wuri ɗaya ya fuskanci mahaifin nashi cikin sanyi yace.
“Ni dai bana so. Abba dan Allah kada ka bari suyi.
Bana son garin nan bare mutanen cikinsa, kuma bawai haka banza naƙi auren nan ba, Abba inada matsala, Please Abba na tuba dan Allah kace su bari. In yaso a ɗaura da wani amman banda ni kam”.
Lamiɗo ne ya kamo hannunshi cikin isa yace.
“Auren’ nanfa, kamar ma an ɗaurashi an gama, domin babu wani abu ko wani mahaluƙin da ya isa ya hana wannan ɗaurin auren, gwarama ka kontar da hankalinka. Tunda ka iya jure bulalin aiko tabbas dole ka aureta, babu shakka dole sai ka aureta, bazai yiwu a dakeka a kantaba sannan ka barmusu itaba.”
Cikin jin haushin wannan fitinenne tsohon ya kwace hannunshi daya riƙe tare da cewa.
“Haka kenan kullum zanyi ta wahala a bisa wasu dalilanka da bana addiniba, me ruwanka da dukan da akayi min, ba dai kai-kasa dole aka dakeni ba”.
A hankali Galadima yace.
“Eh da kuma bakayi kukaba, baka guduba, yau kuma kasa yayi kuka ya gudu ai dole ka aure matar da a kanta aka haɗaku gasar, tunda mu dai ba sakarkaru bane, bare ace bamu san dokar gasar Shaɗi ba.”
Wayyo Jabeer ji yakeyi tamkar ya mammake tsoffin nan dan tarin baƙin ciki. Rai a ɓace yace.
“Bakufa fini sanin kainaba, tunda nace muku bana son aure, bazan kuma yi aureba, to ku barni mana, rayuwata ce ko taku, ko dole ne duk wata matsalata da sirrin rayuwata sai kun sani! Nace muku bana son wannan garin na tsani garin bana son mutanen garin karankatab ɗinsu.
Bani babu su, in kuma kukayi gangancin cusa min wata muguwar yarsu, tabbas! lallai ilaihin! A kanta zan rama sauran bulali ashirin da wancan ƙaton gardin ya min, hamsin, ni a talatin ya gudu”.
Kai Jadda ya girgiza tare da cewa.
“Ka rama mana kaida matarka, ka rama ka kuma jinyace ta”.
Shiru sukayi sabida jin muryar Dr Aliyu da kuma Galadima da Arɗo Bani da Bappa suna tabbar wa juna lfyar yaransu, cikin Mamaki ya kalli Galadima dake cewa.
“Muma ɗanmu lfyarshi lau, Namiji ne”.
Cikin sanyi Jabeer yace.
“Ji maƙaryacin tsoho, wai lafiyata lau, ko yaushe ya zama likita ya gwadani. Harda wani karkacewa yana zuba ƙarya ko farin gemunshi bai martaba-ba”.
Jin Abbanshi ya daki gefen ƙafarshi ne yasashi yin shiru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button