GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Tana shiga ta ɗauki ludeyi da ƙaramin akoshi kana da pilet sannan ta fito.
Tana fitowa tazo ta zauna gabansu, ta miƙa Shatu, cikin sanyin jiki tace.
“Bawa Rafi’a ta ɗiba musu, wlh jikina duka rawa yakeyi”.
Amsar pilet ɗin Rafi’a tayi ta fara ɗibawa Ummiy rabin zabuwa.
Kana ta sawa Bappa gudar da romonta,
Tana cewa.
“Garkuwa yunwace fa, ace mutun ya wuni ya kuma kwana baici komaiba ya kuwa wuni ba abinda yaci ai dole kiji jiri, gashi yawan kukan da kikeyi ne yasa miki zazzaɓi.”
Ta ƙarishe mgnar tana rufewa Bappa nashi kana tace.
“To muci”.
A tare suka saka hannunsu cikin akoshin.
Junainah ce ta fara yago tattausan farin tsokar ƙundun zabuwar cikin haɗiye min yau ta kai hannunta bakin t….!

Dan Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina, in kinsan Zaki fitarne gaya min in baki kuɗinki, dan Allah.

                     By
             *GARKUWAR FULANI*Ta kai hannun ta, kusa da bakinta kenan

Wani ƙaton gadamgare ya faɗo jikinta.
Wani irin tsalle tayi tare da rauza ihu, ta faɗa jikin Aysha tuni tayi fatali da akoshin gasassun zabbin nan ya ɓare ƙasa kirib.
A firgeci Ummiy ta yunƙuro tare da nufar inda suke, wanda hakan yasa tayi fatali da akoshin da akasawa Bappa zabbuwar da kuma take wanda aka zuba mata a plet ɗin ya ɓare cikin lallausan yashin garin.

Ita kuwa Junainah gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, fizge-fizge takeyi tana ƙwaƙumar Shatu.
Sabida ita ji takeyi kamar dai har yanzu ƙadangaren yana jikinta.
Cikin kiɗima Shatu ta ruggume ta, tare da cewa.
“Ke Junainah ki bar ihun ƙadangaren ma ya razana da ihun da kika kurma ya sauƙa ya tafi.”
Jin hakane yasa ta tashi zaune tare da zazzaro ido,
Rafi’a kuwa dariya tasa tare da cewa.
“Kai Junainah yaseen kin cucemu, kallifa yadda kikayi fatali da akoshin nan”.
Cikin sanyi Shatu tace.
“Haba wannan abu dai Allah yayi ba raban mu bane, Ni dama can haka nan in naga naman sai inji zuciyata ya tsinke ashe ba rabanmu bane, da muncima da mun harar dashi.

Ita kuwa Ummiy jan hannun Junainah tayi kana ta zauna kusa da Shatu.
A hankali ta jingina kanta da kafaɗan Shatu,
Rafi’a kuwa miƙewa tayi ta shiga kitchin ɗin su.
Abincin data dafa musu ta kawo musu.
Ta ajiye gefe, sannan ta ɗauko tsintsiyar kwakwa ta share ta kwashi naman kab ta maidashi cikin babban akoshin, ta rufe, sannan taje ta wonke hannunta kana tazo ta zauna suka fara cin abincin.

A can cikin fadar masarautar Joɗa kuwa.
Jin jiri na ɗibanshi ga duhu dake rufe mishi ganine ya sashi, tafiya a hankali tare da dafa jikin gini.
A haka har ya isa bakin Jakuzin,
A hankali ya zare al’kyabbar jikinshi, ya wurgar dashi can gefe,
kana ya tura ƙofar ya Jakuzin ya shiga,
tsayuwa yayi tsakiyarshi, hannun na rawa ya buɗe shawan ruwan ɗumi.
Wani irin numfarfashi wahala ya sauke lokacin da yaji ruwan ɗumi yana ratsa raɗi-raɗin azabobbun bulalin da yasha.
Wasu irin hawaye masu masifar zafine yaji suna tsastsafo mishi cikin jijiyoyin kekyawan idanunshi, sai dai basu kai ga damar samun zobowa ba.
Wani irin tsuma duk illahirin sashin jikinshi ya fara,
zafin ruwan yakeji har cikin ƙoƙon ranshi,
wani irin karkarwa haƙoranshi sukeyi har suna dukan juna, kat-kat.
Kanshi ya sunkuyar tare da buɗe idanunshi a hankali, ruwan dake gangarowa daga jikinshi yana bin ƙasa in da zai gangara yake kallo,
sabida zakace jinine ba ruwaba,
Sabida yana wonke mishi jinin jikinshi.
Haka ya tsaya a ƙasan ruwan ɗumin har saida yaga jinin ya daina zuba kamar da fari.
Sannan yasa hannunshi ya ɗauki daddaɗan sabulun wankan shi, ya fara murza sabulun taki wani sashi na jikinsa, wani irin wahaltaccen ƙara yayi lokacin da sabulun ya ratsa inda ya farfashe a jikinsa, cikin rauni yace.
“Wayyo Allah na! Wayyo Mamey na zan mutu, zafi zai kasheni tun kafin cikar burina.”
Ci gaba yayi da murza sabulun tare daci gaba da cewa.
“Wayyo Umaymah wayyo Ummi”.
Sai kuma ya taune lips ɗinshi kana ya rumtse idanunshi yayi ta murza sabulun tako ina yanayi ruwan ɗumi na dukanshi.
A haka yayi wonka ya wonke duk wani jini dake jikinshi yayi fes.
Al’wala yayi, kana ya fito cikin Glass ɗin sannan ya ɗauki wanni tattausan baby towel fari ƙal ya ɗaura a ƙirjinshi ya sauƙo har zuwa guiwansa.
Hannunshi yasa ya murza farin boxes dake jikinsa wanda ɗazu yake jiƙe da jini yanzu kuma yayi fari tas.
Murza boxes ɗin yayi har ƙasa, kana ya ɗaurashi kan al’kyabbar jikinshi da ya cire,
Cikin Woshing mashine yasasu,
Kana ya fara yin taku a hankali ya iso gaban drower’n glass ɗin dake cikin bathroom ɗin.
Wani tattausan gajeren wondo fari tas mai ratsin sky blue ya saka, gajeren wondon yazo mishi har guiwarsa, kuma mai ɗan faɗine,
Wata tattaunawar riga mai guntun hannu wacce itama farace da ratsin Sky blue, ya saka, kana ya zaro wata ɓakar tattausar jallabiya doguwa har ƙasa tazo mishi daya zurata,
Wani hulan taɓa kaji Hadisi ya kifa kan suman kanshi dake da ɗan damshin ruwan ɗumin.

A hankali yake taku sabida zuwa yanzu wani fitinenne zazzafan zazzaɓi yakeji.
Jiki na rawa ya fito, bisa sallayarshi dake shimfiɗe a wata ƴar kusurwa yaje ya hau.
Yana hawa kan sallayar ya fuskanci gabas, yaji zuciyarshi tayi wasai, baya tuna komai, baya kuma jin ciwon komai a jiki da zuciyarshi sabida kushi’i da tawakkali da kyutata ibada baya jin komai sai hasken farin cikin ibada.
Kabbara ya tada tare da niyar sallan la’asar daya mannata bisa laruri ya makarar dashi.

A falonshi kuwa, hankalin Haroon ya tashi yana nan tsaye bakin ƙofa yana ta magiyar ya buɗe mishi,
bai saniba shi yana can har cikin bathroom ɗin shi.
Yana nan tsaye, mai Martaba Lamiɗo da Galadima suka iso tare da Sarkin Shaɗi.
Cikin sanyi yacewa Lamiɗo.
“Ya shiga ciki kuma ya rufe ƙodar ta ciki, inata kiranshi baya amsawa.

Murmushi Lamiɗo yayi kana, yacewa Galadima.
“Muje”.
Kusan a tare suka fito falon.
Suka zauna, kana ya kira Abba, yace yazo yasa ɗanshi ya buɗe musu ƙofar.

Jin hakane yasa Abba tahowa da sauri.

A can babban falon kuma. Cikin damuwa Jamil ya labartawa Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya abinda ya faru.
Ga mamakinsu sai sukaga Jakadiyarsu tayi wani ƙayataccen dariya cikin sakekkiyar murya tace.
“Alhamdulillah wannan shine abinda muka daɗe muna jira tsowon shekaru da dama.
Kuma jinyarsa abune mai sauƙin”.
Cikin ruɗani Jalal yace.
“Ummi kuka daɗe kuna jira kuma?”.
Kai ta jinjina mishi, kana ta miƙe ta nufi kitchin dan harhaɗa aikin da akasata.

A nan Abba yazo ya samesu.
Jalal na ganinshi ya kauda kanshi.
Hakama Jamil Imran kuma bayanshi yabi suka nufi side ɗin Jabeer ɗin.

A falo ya samu iyayen nashi,
Cikin girmamawa ya rusuna yayi Lamiɗo Barka da yammaci kana ya matso kusa da baƙin ƙofar Bedroom ɗin Jabeer cikin ɗaga sauti yace.
“Muhammad! Muhammad Jabeer! Jabeer!! Jabeeey!!! Ka taso maza kazo ka buɗe min ƙofar nan ina jiran ka”.

Jabeer kuma da yanzu yake raka’ar ƙarshe, sam hankalinshi baya ga jin kiran Abbanshi domin a yanzu yana gaban Ubangijinmu ne.

Haroon kuwa wayar dake kunnenshi ya gyara riƙewa cikin shaƙiyancinsa yace.
“Uhumm Umaymah ke dai kicewa Sarki Jalaluddin da Sarki Abubakar baban Daddy na, suyiwa masarauta Joɗo gudumowar suturu. Domin yau dai ran ƴan maza ya ɓaci, nasan sai ya yayyage kab wani abu mai yaguwa a masarautarsu”.
Cikin wani irin farin cikin wannan labarin da Umaymah taji tayi kekkyawan dariya tare da cewa.
“Haroon yayan naka kakeyiwa tsiyako?”.
Cikin tura baki yace.
“Allah ko Umaymah kecema kike sawa Jabeer yana rainani wai yayana”.
Da sauri tace.
“To ba yayanka ɗin bane?”.
Cikin yamutsa fuska yace.
“Yayan kwana arba’in, shiyasa yake min kallon kobo biyu da sisi, sabida yana jin kuna ce mishi yayana, wani lokacin har cemin yaro yakeyi dan tsabar son girma da manyance, Ni mamaki da yake bani kawai sai in zuba mishi ido in naga yana min faɗa kamar wani ɗan cikinsa”.
Murmushi Umaymah tayi kana, tace.
“Gobe zuwa jibi in sha Allah ina nan zuwa Masarauta Joɗo, sabida zanzo in lallashi ɗana nasan yayi zazzafan fushi tunda yaƙi kula Dr Aliyu ma”.
Daga nan sukayi sallama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button