GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Nan suka rinƙa zuwa suna gaidata da gaya mata sunansu. Kana Hibba ta irga dubu biyar, ta ɗaura kan kala bibbiyu sun ta basu.
Ummi kuwa jakan gabanta ta buɗe tana basu takalma.
Aunty Juwairiyya kuwa jakar hijabai ta buɗe tana basu.
Suna godiya suna tafiya.
Haka sukayi tayi har kusan awa biyu kafin suka gama, duk kayan sun ƙare sai kuɗin ne ya rage.

Ganin lokacin salla yayi ne, suka tafi.

Bayan sun idar da salla ne, suka fito.
Nan a falon Shatu suka zauna.
Suna ɗan hira sabida yau aikinsu baida yawa, kuma Saratu nacan na rage musu.

A hankali wayar Ummi ta fara suwa, alamun ana kiranta.
Da sauri ta kalli Hibba tare da cewa.
“Hibba ɗauko min wayata a ɗaki”.

Miƙewa tayi tare da cewa to.
Jim kaɗan ta fito da wayar da sauri ta miƙa wa Ummi wayar a kunne tare da cewa.
“Amshi Ummi kiyi mgna na amsa kiran Hamma Jabeer ne, kin sanshi baya kira biyu.”
Cikin sauri da tarin jin daɗi Ummi tace.
“Assalamu alaikum”.
Shi kuwa Sheykh Jabeer a can saudia yana tsaye ne a gaban dreesing mirror yana gyara igiyoyin al’kyabbar jikinshi.
Tare da saƙala wayar a kunnenshi ya matseta da kafaɗarshi.
Alamun sauri yake yana shirin tafiya haramine.

Cikin sanyi yace.
“Wa alaikissalam. Barka da gida Ummi”.
Fuska a sake tace.
“Barka dai Sheykh, ya ibada?”.

“Alhamdulillah Ummi, yasu Jalal”.

“Suna lfy, kuma basa wasa da ibada, yanzu Jamil ya dena zuwa hirama wata ƙil kuma ya ɓata da Khadijah naji yanzu wata Maryam yake kira, Jalal ne dai yake ɗan fita shima ba sosai ba”.
Gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
“To Alhamdulillah, eh shi Jalal ba matsala fitanshi, nasan dashi.
Ya Hibba kuma tana azumi ko batayi?”.
Cikin murmushin da kallon inda Hibba take tace.
“A a Hibba ai an girma yanzu ta rage rakinma”.

Ɗan karamin mataji ya ɗauka yana kontar da sajenshi yace.
“To Ummi na gaisheku, na kira Aunty Juwairiyya kam nani jikin ya Jafar da sauƙi sosai mun gaisa da Hajia Mama, har take cemin Affan ɗina zai dawo a salla”.
Da sauri tace.
“Uhum Sheykh”.
Ajiye kum ɗin yayi tare da cewa.
“Na’am Ummi”.
Cikin sanyi tace.
“Ga Shatu”.
Shiru yayi baiyi magana ba, kuma bai katse kiranba,
jin haka yasa ta kuma cewa.
“Sheykh”.

“Na’am Ummi”.
Ya kuma cewa.
A hankali tace.
“Ga Shatu”.
Still baiyi mgn ba, hakanne yasa a hankali ta mannawa Shatu wayar a kunne ta.
Kana ta sa hannunta ta kamo hannun Hibba suka fita babban falon.

Shi kuwa Sheykh Jabeer shiru yayi tsaye gaban dreesing mirror, yana kallon gemunshi.
A hankali yake jiyo sautin sauƙar numfashin can ƙasa-ƙasa, ɗis ɗas haka yaji ƙasan zuciyarshi na harbawa.

Ita kuwa shiru tayi tanajin sautin tasbihi da yakeyi can ƙasan-ƙasan maƙoshinsa,
Lips ɗin shi na motsawa a hankali suna fidda sautin can ƙasa.
Jin shirun yayi yawane yasa a hankali ta buɗe bakinta tare da cewa.
“Assalamu alaikum”.
Sai kuma tayi shiru ta kasa kunnen dan jiran amsarshi.
Gyara zamanta tayi tare da ƙara riƙe wayar, numfashi ta sauƙe a hankali.
Hakan yasa yaji sautin iskar.
Har ta cire tsammanin zai amsa sai kuma taji muryarshi can ƙasa yana cewa.
“Wa alaikissalam. Ashe kin iya sallama?”.
Ya jefo mata tambayar a gajarce.
Cikin juya ido tace.
“Ba’a koya min da wuri bane!.”
Shine mgnar da tayi niyar gaya mishi, sai kuma tayi mgnar a zuci, ta danne abun.
Sabida tana son ta nemi al’farman addu’o’in a kaba, aka yayunta da suka bace, shiyasa cikin sanyi tace.
“Eh, Ummi ta koya min”.
Shiru yayi kamar bai jitaba,
ita kuwa a hankali tace.
“Ina kwana”.
Kanshi ya ɗan kalla a madubi tare da cewa.
“To Kifin rijiya su nan yanzu wunine”.
Cikin sanyi da sassauta Muryar son isar da buƙatar ta tace.
“To ina wuni”.

“Alhamdulillah”.
Ya bata amsa.

Miƙewa tsaye tayi ta nufi bedroom ɗinta.
Tare da cewa.

“Ya ibada?”.

“Alhamdulillah”. ya kuma cewa.
“Har ya kai hannunshi zai janye wayar sai kuma ya tsaya jin tana cewa.
“Uhmm, Ayyah Yah Sheykh..”.
Sai kuma tayi shiru. Cikin saurin jin an kira salla murya a nitse yace.
“Uhumm Ayyah, me ɗin?”.

Da sauri tace.
“Dama.. dama!!…”.
Gajeren tsaki yaja tare da cewa.
“Sauri nakeyi zan tafi masallaci, kada kisa na rasa damata”.
Cikin rauni da muryar dake nuna cewa tana zubda ƙwalla tace.
“Ayyah dan Allah da Manzonsa.
In kaje kayi min addu’a a harami mana”.
Juyowa yayi yana kallon Haroon da Ya Hashim da suka shigo yanzu alamun kiranshi zasuyi.
Cikin wata iriyar murya a hankali yace.
“Addu’ar me zan miki?”.
Murya na rawa tace.
“Allah ya dawo min dasu Yayana lfy, ya kare minsu a duk inda suke, ya baiyana sucikin gaggawa”.
Cikin rashin fahimtar zancen nata yace.
“To zan miki saboda Allah da Manzonsa da kikace”.
Cikin jin daɗi tace.
“Ngd matuƙa Allah ya biya maka buƙatunka.”
Wani irin sassanyan numfashi ya sauƙe tare da lumshe ido a hankali yace.
“Amin ya rabbil izzati, kema kuma kiyita addu’a ki dage da ambaton Allah zai cika mana dukkan burinmu”.
Yana faɗin haka ya katse kiran.

Ita kuma murmushi tayi tare da share hawayenta.
Cikin sanyi tace.
“Ya Allah ka dubemu da idon rahama”.
Hibba dake shigowane tace.
“Amin Amin.”

Daga nan suka fito falo suka kama sabgoginsu.

A kwana a tashi asarar mai rai.
Yau da gobe kayan Allah.
Kamar yau aka kama azumi gashi yau an kai azumi na ashirin da tara.
Wanda ake tsammanin tsalla gobe ko jibi.

Irinsu Hibba duk sunfi fatan wata ta dawo yau.

Gaba ɗaya wunin yau aiki Ummi da Shatu da Saratu suka wuni yi, wanda aikin salla ne.
Zabbin da Jalal ya kawo bisa umarnin Hammansun.
Da kuma kajin da Lamiɗo yasa aka rabawa al’ummar masarautar Joɗa.
Ko wani Side in dai akwai mace kaji goma ake kaiwa.
Da tarin kayan miya komi da komi, wanda shi cikin lambun masarautar ake cirewa.
Kajin kuma daga gidan Gidan gonar MJ aka kawo, kana zabbin da aka kawo manyan sashin Masarautar Joɗa ma daga gidan gonar MJ aka kwasosu. Haka ƙoyayen kaji.
Duk an rarraba ko ina.
kuma duk saida aka yanka su aka gyarasu aka rarrabusu, dan haka aiki kawai aka fara babu kama hannun yaro.
Hadimai da bayi sunata aiki.

Duk sauran ɗinku nan suma sun dawo.

Kasan cewar kusan a kitchen ɗin suka wuni ne, yasa Shatu ta ɗauki zabbi uku tun da azahar tayi musu gyara na musamman.
Hibba kuwa tana Side ɗin Aunty Juwairiyya anayi mata zanen lalle.

Akan sai dare za’ayiwa Shatu shiyasa taketa kimtsa aiyu kanta da wuri.
Dama sunje da sassafe an wonke musu kai an gyara musu.

Ummi kuwa tayi lallenta na gargajiya tana kwance a falo.
Hakane yasa Shatu ta kira Gimbiya Aminatu.
Cikin wasa tace.
“Gimbiya a ƙaro min mai taya aiki yau Ummi na tasa lalle, Hibba ma tana can ana zana mata, nida Sara ce kaɗai a kitchen.”
Dariya Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
“To Sayyadar Sheykh bari Larai tazo”.
Cikin jin daɗi tace.
“To Gimbiyar Lamiɗo”.
Dariya sukayi duka kana sukayi sallama.

Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
“Tace zata turo Larai, Ummi ta iya aiki ko?”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
“Sosai ma kuwa”.
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana ta miƙa wa Ummi wayarta tare da cewa.
“Ummi sai mun nitsu ki bani number Gimbiya Aminatu”.
To tace kana ta koma kitchen ɗin.

Wanke zabbin tayi fes tare da ɗan matsa lemun tsami kaɗan a ciki.
Kana ƙara lallaɓeshi.
A tukunyar ƙirar ƙasar Cameroon ta zubasu.
Kana tasa al’basa, Curry, Maggi, kanamfari, citta, tafarnuwa kaɗan, da gishiri ɗan ƙanƙani.
Ta rufe tukunyar da zabbin uku suka cikashi.

Bisa gas ta ɗaurashi kana tasa wutan dai-dai.

Saratu kuwa sa sauran tayi a babbar tukunta tasa kayan ƙamshi da ɗanɗano.
Sannan ta ɗaura.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button