GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A haka Salmanu da abokinshi, sukazo suka sameshi zaune. Bayan sun gaisane Sule ya ɗan matso kusa da Arɗo a hankali yace.
“Allah rene, duk wuri an taru mu ake jira, shi Ba’ana tun da asuba yana can, yanzu Iro yazo yake ce mana gacan fili ya cika, mu kaɗai ake jira, har wasu nata maganganun wai Salmanu ya ji tsoron Ba’ana ya gudu”.
Murmushin da yafi kuka ciwo Arɗo Bani yayi dafa tsakiyar kan Salmanun yayi kana yace.
“Kuje Salmanu, Allah ya bada sa’a Ubangiji yaga niyarmu na son tseretar da wannan yarinyar daga fadawa auren wannan mushurkin, taƙadiri in Shatu matarkace Allah ya baka sa’a in kuwa ba matarka bace, Allah ya baiyono mata wanda zai zame mata GARKUWA daga faɗawa auren wannan azzalumin”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu kana su sukayi gaba.
Shi kuwa Arɗo, saida ya jira su Malam Liman Bappa kenan dasu Ahaji Horu, da Ahaji Umaru da Garbati.
Koda sukazo ba ɓata lokaci suka nufi, farfajiyar wurin da aka tanada dan shaɗi.

Filin ya cika ya batse tako ina mutane zuwa sukeyi arna da musulmai fulani da hausawa da ƙabulun, Ɓachamawa, domin duk yankin nahiyarsu an san babu taƙadiri sama da Ba’ana sabida tunda ake gasar Shaɗi da kuma gasar kokuwa yayin nunan sabon gero ba’a taɓa cin nasara kanshiba, muddin ya shiga gasa tofa shine da nasara.
Har ta kai da in dai ya ɗaga hannun to babu mai ɗagawa.
To sanadinshi aka hana Shaɗi a Rugar Bani, tsawon shekaru biyu sai gashi yau an dawo dashi.

Wannan dalilin ne yasa gaba ɗaya Rugar Bani ta cika maƙil da mutane maza da mata manya da yara,
Ga mai busar sarewa kuma yana tsakiyar taro inda akabar filin da za’a gobza yanata rere kirari wa Ba’ana.

Isowar su Arɗo yasa aka basu hanya har suka iso gaba inda aka tanada musu, kujerun zama. Na bencin katako.
Daga nan manyan Dattawan duk suka Zazzauna.
Bisa ƙa’idar gasar Shaɗi wanda ya fara cewa yana son yarinya shi zai fara duka, in wanda yace yana sonta daga baya ya ƙetare bai zubda hawayeba baiyi kukaba, to sai asa kwanaki sai yaje yayi jinya ya worke daga zabgar da yasha, sai ya dawo ya ɗauki fansa, to in ya zana wannan yayi kuka shike nan yayi nasara in kuma wannan ma baiyi kukaba za’a sakeyi har sau uku to nan in babu wanda yayi kuka cikinsu sai yarinya ta zaɓi wanda takeso, don anada yaƙinin duk wanda ta zaɓa, zai iya kare kanshi tunda ƙarfinsu yazo ɗaya.

Bayan an gama dai-dai-ta komai, Salmanu ya cire rigarsa kamar yadda ƙa’idar gasar take, ya rage dagashi sai gajeren wondon.
Shi ma Ba’ana ya cire rigarshi ya zama dagashi sai gajeren modo, irin masu zuwa har guiwa ɗinnne.

To dole a ƙa’ida Ba’ana ne zai fara duka, amman da yake ya shiryawa abun sai yace, shi ya amince a fara dashi, kuma shima yau zai rama Ba sai an ware kwanakin zuwa jinya ba.

Nan kuwa take al’kalin gasa Barmuji yace an amince.
Daga nan aka zaro bulalin shaɗi na cikin tanɗun masarautar Arɗo Yabani wanda an ƙara tsumasu suma.

A hankali Barmuji ya miƙa wa Salmanu, bulalin,
kana ya ɗaga hannunshi ya dawo dashi ta bayan Ba’ana.
Shi kuwa Ba’ana tsayuwa yayi ƙam tare da ɗan ware sawunshi,
Busar sarewar da mai busan yayine alamun a fara,
Ai kuwa cikin kuzari da jaruma Salmanu ya ɗan ja da baya,
kana ya tattaro ƙarfin shi ga ba daya, ya ɗaga kitsetsten bulalan nan, ya taƙarƙara ya zabgawa Ba’ana shi a tsikar bayanshi,
Wanda a take taron matasan dake wurin suka kurma ihu mai karaji,
Yayinda shi kuwa Ba’ana, ƙim ya tsaya kamar ba shiba, domin ko idonshi bai ƙebtaba.
Sake taƙarƙarewa Salmanun yayi ya kuma zabga mishi bulalar a inda ya kima mishi na farin.
Still ihu, taron matasa sukasa, tarin ƙabilar ɓachama kuma dake wurin sai rurrufe idanunsu sukayi da ƙarfi sabida wai bazasu iya jurar ganin ana zabgar jakadan suba.
Mai irge kuwa da iya ƙarfinshi yake kware baki yana cewa.
“Ɗaya! Biyu! Uku! Huɗu! Biyar! Shida! Bakwai!!!”.
Haka yaketa irga duk bulalar da aka kaiwa Ba’ana amman wannan tagadirin mutumin ko a jikinshi kamar dutse ake zanawa ba shiba.

Ƙa’idar bulalin shaɗi Hamtsine akeyi.
Haka Salmanu yake ware iya ƙarfinsa yana zabgar Ba’ana, yana tsaye ƙiƙama. In wannan bulalan ya lauye, sai a bashi wani bulalan.
Har akaje arba’in da takwas ko gezau.
Gaba ɗaya hankalin mutanen kirki ya gama tashi, domin sun sadakar da nasara ta kubcewa, Salmanu.
Shi kuwa Salmanu tattaro sauran ƙarfinshi kab yayi,
ya narka mishi bulala ta 49-50″.
Amman shirunshi.
Ihun da kafuran ƙabilar ɓachama suka sakine ya tabbar an gama, nan take suka shigo filin da gudu ruggumeshi suketayi suna shafa bayanshi, da yayi shati-shati.

Shi kuwa Salmanu gaban Arɗo yaje ya zauna, nan aka basu ruwa sukasha gaba ɗayansu.
Hutun 30 minutes sukayi aka koma fagen fama.

Da ƙarfi mai busan sarewa ya busa alamun a fara,
wani irin kafurin murmushi Ba’ana yayi tare da gyara riƙon da yayiwa bulalar tashi.
Cikin tsananin mugunta ya ɗan koma da baya, kana ya ɗago bubalar da masifan karfi ya zabgawa Salmanu ita a tsakiyar fatan bayanshi.

Wani irin gan tsarewa Salmanu yayi, sabida wani irin masifeffen azaba mai girgiza zuciya da yaki yana ratsa dukkan sasasan jikinshi.
Bai gama dawowa daga gigi da azabar bulalar forkoba, yaji ta biyu,
Rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi, gaba ɗaya inda bulalar ya taɓashe, harbin kunama yakeji yana ratsashi.
Wani irin numfarfashi yaka lokacin da aka zabga mishi bulala ta goma.

Gaba ɗaya hankalin mutane ya tashi domin kowa yaganshi yasan yana jin azaba.
Bulala ta ashirin da biyar da akayi mishine ya sashi buɗe idanunshi da suka koma jajazir dan azaban da yakeji.
Su kuwa kafuran nan sai ihun farin ciki sukeyi.
Shi kuwa Barmuji zagayawa yayi gaban Salmanu wai yaga ko idonshi ya kawo ruwa,
babu ruwa kam sai azabar da yakeyi tamkar idanun zasu faɗo ƙasa, ci gaba da irgens yayi.
“Ashirin da uku! Ashirin da huɗu!!”.
Wani irin tsalle Ba’ana ya buga da iya ƙarfinshi ya tsulawa Salmanu bulala ta ashirin da biyar.
Wani irin duhune ya rufe ganin Salmanu, saiga wasu zafafan hawayen azaba sun kwaranyo masa, ihu ya kuma zurma jin zafin bulalar ta isa kan mazantakanshi.

Gaba ɗaya su Bappa dama matasan kowa rufe ido yayi sabisa dukan da akewa Salmanu dukane na son ɗaukan rai.

Aysha kuwa tana gidansu kamar kullum tajiyo ihun Ya Salmanu kamar yadda kullum ihun wanda ake gasar dasu ke shaida mata sun faɗi.

Cikin kuka konta bisa cinyar Ummey tare da cewa.
“Shike nan Ummey zai kashe ya Salmanu”.
Tuni itama Ummey da Inna hawayen suke zubdawa.

A can gidan Arɗo Yabani kuwa inna laure Maman Salmanu, kuka takeyi tamkar zata shiɗe domin yaranta mata sun zo sun gaya mata halin da yake ciki.

A can wurin gasar Shaɗi kuwa, ganin tuƙuru Ba’ana so yake ya kashe Salmanu ne yasa,
matasan Fulani sukayi kanshi dan dukanshi yake harda tattakashi kuma tuni ya wuce balali hamsin ɗin ƙa’idar gasar.

Koda matasan Fulani suka shiga dan crton ran Salmanu kawai sai ga ƙabilar ɓachamawan nan, sun fara zaro makamai sun rufa duk wani ba fulatani da duka da saran wuƙa.

Lokaci ɗaya wurin ya hargitse gaba ɗaya.
Aka kaure da faɗa saida.

Ganin wurin ya hargitse ne yasa,
Gaini yayi saurin kiran hukuma mafi kusa ya sanar musu.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka iso.
Hakane yasa duk ƙabilun Ɓachamawa suka gudu.
Allah ya takaita faɗan baiyi nisa ba, a take ɗaya daga cikin police ɗin wanda yake abokin Salmanu ne ya kwashesu suka tafi asibi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button