GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Zareta daga jikinshi yayi kana ya miƙe yana cewa.
“Zaki bazu yarinya bari ki shiga tarkon Muhammad zaki bazu iya bazuwa”.
Ya ƙarashe mgnar yana wuce bedroom ɗin yana shiga bathroom ya wuce al’wala yayi kana ya fito.
Wayarshi ya zaro a al’jihunsa, kirar arshi mai sauti yasa mata kana ya ajiye mata gefen kanta, sannan ya fita ya tafi masalacin.

Bayan sunyi sallan mangriba basu fitoba saida sukayi isha’i, kana suka dawo gida.

A falon ya samu Umaymah, Ummi, Mamma, Aunty Rahma, Safiyyah Jannart.
Itama Aysha tana zaune,
yana ganinsu a cike ya ɗan tsaya kana ya kalli Umaymah dake cewa.
“Jazlaan ya jikin nata dai”.
Matsowa yayi yasa hannunsa ya ɗauki wayarshi dake kusa da ita kana yace.
“Uhumm ta worke ai”.
“Alhamdulillah Allah ya ƙara lfy”.
sukace a tare,
A hankali Aysha tace. “Amin”.
Safiyya, Jannart, Aunty Rahma, ne suka fita.
Hakane yasa ya rage Umaymah, Ummi Mamma.
Kanshi ya ɗan juya ya kalli Ummi dake cewa.
“Wannan abun fa sai an tsaya mata zata rabu dashi Sheykh”.
Yana lallatsa wayarshi yace.
“Dama ai Ni na sani tun jiya data fara cewa, taga Jahan a a Jahan yazo nasan ba wani Jahan ababaɗenta ne kawai ke mata gizo. Amman ba komai zan juyo kansu ya faɗa yana ɗan guntun murmushi, domin yasan Umaymah dai tasan waye Jahan”.
Ita kuwa Aysha.
Tura baki tayi tana kallonshi kamar tayi kuka. Allah ya sani bata son yana cewa tana da al’jani”.
Murmushi Umaymah tayi ganin yadda tayi kana a hankali tace.
“Kada ki damu, yana raba wasuma da nasu bare ke, in sha Allah zasu bar jikinki juyowa ɗaya zaiyi kansu bazasu sake waiwayarki ba ɗiyata. Kirkiji komai mu mun sani matsalar a masarautarsu ce, da Juwairiyya ma lfya lau muka kaita gidan Jafar bata shekaraba makarai suka shige ta”.
Da sauri yace.
“Amman dai ita wannan da abunta tazo Umaymah ba a masarautarmu ta sameshi ba”.
Mamma ce tace.
“Kada ka kare wancan masarautar taku, mu tayi mana illa mafi muni a rayuwa.”
Kanshi ya jinjina tare da lumshe idonsa kana yace.
“To ya zanyi Mamma tunda jigo nane asalinane, kuma ba kowa na ciki keda mugun dafiba, kada kuyi mana kuɗin goro, Nima inai musu uzuri duk da dai nasan duk duniya babu wanda sukayiwa illa sama dani, sai dai nasan zanen ƙaddaratace suka bi”.
Kai Ummi ta jinjina kana suka miƙe tsaye.
Umaymah ce ta nuna mishi Foodflaks dake tsakiyar falon tace.
“Kuci abinci ka kula da ita,sai da safe”.
Ta ƙare mgnar suna fita.
Cikin jin kunya yace.
“Allah ya bamu al’khairi”.
Amin sukace kana suka tafi.

Washe gari da asuba, a hankali ta buɗe idonta jin muryarshi yana karatu.
Ganin ya bata baya baya ganinta ne, yasa ta yunƙura a hankali, ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa.
Kana ta miƙe ta nufi Bathroom, ruwan ɗumi ta haɗa cikin bathtub ɗin sabida alamun hadari da sassayan iskan dake busowa.
Wonka sabulu tayi, kana tayi na tsarki sabida al’adarta ta ɗauke.

Towel ɗin dake bisa masaƙalin ta ɗauka ta tsane jikinta, kana ta meda kayan jikin nata.sannan ta fito.
Gefenshi ta ɗan ratsa sannan tace.
“Zanyi salla kuma ba hijabi”.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta,
kana yaci gaba da karatun.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ni ban san ina mukeba, kuma ba hijabi”.
Miƙewa tsaye yayi jin masallacin Masarautar suna ƙoƙarin tada kabbara.

Al’kyabbar ajikinshi ya zare, kana ya dawo ta bayanta.
Hannunshi yasa ya ɗago hannunta ya zura mata hannun al’kyabbar, kana ya ɗago ɗayan ma ya zura mata.
Sannan ya saketa.
Har ƙasa ta zo mata,
kasan cewar irin al’kyabba mai duhu da kaurin nanne yasa tayiwa jikinta ƙawanya.

Gabanta ya dawo, jallabiyace a jikinshi fara ƙal.
Hiramin kanshi ya cire, kana ya ɗaura mata shi a kanta tare da dai-dai-ta zamanshi ya rufe komai na kanta sai fuskarta kawai.
Ido kawai ta zuba mishi tana mai shaƙar ƙamshin jikinshi.
“Ni dai ba ɗan aikenki bane, kuma bani nace kisa suturar da bai inƙanta ayi salla da itaba, dan haka babu ruwana. Al’barkacin salla zakiyi ne yasa na baki aron rigata, kina idar da salla ki cire min abuna”.
Ya gaya mata yana tsareta da ido.
Cikin yin mui-mui da baki tace.
“Uhummm”.
Shi kuwa juyawa yayi ya fita.
Daga nan Side ɗin da kayansu yake shida Ibrahim yaje.
Wata al’kyabbar yasa kana suka nufi masallacin.

Bayan an idar da salla sune suka dawo gida.

Tuni Umaymah kuma tasa Safiyyah da Aunty Rahma sun shiga kitchen da kansu sun haɗa breakfast.
Nan aka kaiwa su Affan da Ya Hashim, Imran Sulaiman.
Sukaci abinci kana suka kama hanyar komawa Ɓadamaya.

Sheykh, Ummi, Aysha, Hajia Mama da Batool da Jamil, Jalal ya Jafar kuwa su sai bayan sallan isha’i jirginsu zai tashi.

Haka kuwa akayi. Bayan sallan isha’i.
Su Umaymah Haroon, Ibrahim, Safiyyah, Sadiq, Azeex, Hibba Azima Aunty Rahma Ishma sukayi musu rakiya har Airport.
Sunata kewar juna,
A cikin mota ne, Aysha ta kalli Safiyyah dake gefen Umaymah da Mamma tace.
“Safiyyah ai zaku zo mana kafin ku tafi ko”.
Aunty Rahma dake jen motarce tace.
“In sha Allah kuwa, ai muma duk zamuzo, sabida zamu ɗan kwana biyu kafin mu koma”.
Cikin jin daɗi tace.
“To Aunty Rahma a bamu Ishma mana mu koma da ita sai kunzo ku taho da ita”.
Cikin dariya Hibba dake can baya ita da Hajia Mama da Ummi tace.
“Aunty Aysha wayo ko”.
Da sauri Aunty Rahma tace.
“Kada ki damu in sha Allah zasu dawo tare da Juwairiyya, kinga mu zamuyi ko kwana uku ne nan gaba kafin mu koma wurin Sittinmu, in mun koma kuwa bazai dadeba Juwairiyya zata komo to sai ta taho miki da Ishma’n”.
Cikin gamsuwa tace.
“To Allah ya kaimu Lokacin”.
Amin Amin sukace, kana dai-dai lokacin suka isa, harabar airport ɗin.
Nan suka samu su Aunty Juwairiyya da Azeema da Jazrah ma sun iso.
Gefensu Sheykh suka isa.
Nan sukayi sallama da juna, cikin bege da kewar juna.
Suka rabu.
Jin ana cekiyar matafiya.
Nan suka nufi cikin jirgi su kuma suka koma baya.
Basu dai tafiba saida jirgin ya tashi, kana suka juya suka koma gida.

Tsakanin Tsinako da Ɓadamaya tafiyar 40 minutes ne a jirgi.

A mota kuwa awa goma sha biyar ne.

So takwas dai-dai jirginsu ya tashi.

Su Affan kuwa dai-dai lokacin suka isa. Kasan cewar a gajiye suka isa, kowa wonka yayi kawai dama sunyi salollinsu a hanya sun kuma ci abinci sai bacci kawa.

8:40 dai-dai na dare jirginsu ya sauƙa a Airport ɗin Ɓadamaya.
Dr Aliyu, da Baba Kamal mahaifin Sulaiman kenan, sai Sarkin fada da Galadima ne sukaje tarbosu tun kafin su iso.

Tafiyar 24 minutes ne tsakanin Airport ɗin da masarautar Joɗa.
Tara da minti goma dai-dai motar Dr Aliyu ta iso har farfajiyar Side ɗin Sheykh, wanda Sheykh yake gaba kusa dashi, Ummi da Aysha suke baya.
Motar Baba Kamal kuwa Hajia Mama ce da Batool,
Sai,
Motar da Galadima ke ciki kuwa, Nan Ya Jafar da Jalal da Jamil suke ciki.
Kai tsaye kuma Side ɗinsu Jalal ɗin aka wuce dasu.

Itama Hajia Mama har bakin Part ɗin ta aka sauƙeta.

Da sauri Ummi ta buɗe marfin motar gefenta ta fita.
Nan Aysha ma tabi ta fita.
Shi kuwa Sheykh juyowa yayi ya kalli Dr Aliyu cikin nitsuwa yace.
“Baba Aliyu ngd matuƙa”.
Kai Dr Aliyu ya gyaɗa tare da cewa.
“To sai da safe”.
Allah ya bamu al’khairi yace.
Amin Amin yace kana yaja motar ya tafi.

A bakin ƙofar shiga falon suka tsaye.
Suna rike da jakukkunansu.
Gefen Aysha ya ratsa ya wuce, ya isa gaban ƙofar, hannunshi yasa ya ɗan zuge zip ɗin jakar dake hannunshi key ya zaro.
Kana ya zuge zip ɗin ya rufe.
Cusa key ɗin yayi a ramin kana yayi bismillah tare da murza key ɗin, kat-kat yayi sau uku kana yasa hannunshi ya tura ƙofar sannan ya wuce ciki tare dasa hannunshi ta sama jikin ginin ya kunna wutan falon kana ya juyo ya kallesu tare da cewa.
“Bismillah Ummi shigo”.
“To”. tace kana ta nuna Aysha hanya alamun tayi gaba.
Kafar dama tasa tare da cewa.
“Assalamu alaikum”.
Ba tare da ya juyoba yace.
“Wa laikissalam”. Ya amsa sallamar a hankali batama jishi ba.
Ummi na biye da ita a baya suka shigo cikin kekkyawan falonsu da sukayi kewarsa.
Ajiyan zuciya Aysha ta sauƙe tare da cewa.
“Masha Allah komai tsab, Allah sarki HIBBA AZEEMA ina kewarku Safiyyah ina begenki kusa Ayyah my Ishma fuskarki ta tuna min Junainah na, Aunty Rahma ganinki ya tada min begen ganin Ummey na.
Ayyah 40 minutes kawai ya nesantamu Umaymah, Mamma Ina kewarku Ina jinku kamar yadda nake jin Ummey na”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Kinga gama Umaymah na kira”.
Ta ƙare mgnar tana amsa kiran.
“Eh Alhamdulillah mun isa lfy gamu nan a tsakiyar falo, ɗiyarki nata kewarsu Hibba da Safiyyah naga harda ƙwalla a idonta”.
Ummi ta faɗawa Umaymah cikin kewarta.
Ita kuwa Aysha da sauri tasa hannunta ta shafi haɓarta sai ma lokacin ta gane ashe harda hawaye take zubdawa.
Ita kuwa Umaymah cikin murmushin tace.
“Wallahi gamu muma yau duk sai mukaji babu daɗi Safiyyah tace ita fa da Aysha ta tafi gidan ba daɗi”.
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
“Sabo kenan”.
“To ku huta gajiya”. Umaymah tace kana ta katse kiran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button