GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Kafin suje kuwa tuni bacci ya ɗauke shi, an ɗaura mishi ruwa da allurai.
Sauran Doctors ɗin sun fita.
Sai Dr Arabi da yake zaune gabanshi.
Da sauri Affan yasa hannun shi ya taɓa jikinshi tamkar wuta.
Jalal kuma yatsarshi daketa karkarwa yake kallo tare da rauni a fuskarshi yace.
“Yah Arabi meya sameshi ne?”.
Cikin sanyi Dr Arabi yace.
“To wlh nima shigowa kawai nayi na sameshi yanata karkarwa, yace min zazzaɓi yakeji sanyi na damunshi.
Na kira Nurse ta kawo min injections and drip kafin muyi mishi allurar ma tuni ya kusa suma, abun yafa bani tsoro.
Amman Alhamdulillah kunga yanzu kuma da sauƙi”.
Ajiyan zuciya sukayi kana suka zauna a nan, ba tare da sun gayawa kowa ba.

A can masarautar Joɗa kuwa.
Cikin tarin firgici da al’ajabi Jamil da Ummi ke kallon Shatu.
Data fizgo macijin da ƙarfi cikin tukunyar.
wurgar dashi tayi a ƙasa sai gashi yayi wutsul-wutsul sau biyu, shike nan ya mutu.”
Mazargin mondo ta fitar da kuma hula wanda duk na Sheykh ne.
Cikin murya mai rauni tace.
“Yanzu Jamil zaka iya taɓasu.
Haɗasu kaje in akwai inda zaka wurgar dasu ka wurgar dasu, ka fasa tulun.
Kada ka binne macijin ya bushe akeso.
Ummi ɗauki Hular Yah Sheykh da zariyarshi a wonkesu.

Da sauri Jamil yace.
“Eh akwai inda zan wurgar dasu”.
Nan ya tattare macijin da da layun ya saka cikin tulun ya fita.
Key ɗin ƙofar baya ya ɗauka ya buɗe ya tafi cikin Garden ɗin.
Tafiya yayi sosai saida yaje can cikin dajin ya fasa tulun macijin da layun suka watse kana ya juyo ya dawo ba tare da ko waiwaya ba sabida tsoro.

Ita kuwa Ummi bathroom ɗin shi ta shiga a take ta wonkesu kana ta fito dasu.
Cikin sanyi Shatu tace.
“Wai hannuna Ummi yi sauri ki wonko gero ki kawo min ruwan tsarin.”

Da sauri Ummi ta fita.
Murmushi tayi ganin Ɗalha mai gyaran tayis yaci yayi haniƙan yana kallon tv.
Cikin sauri tace.
“Yi haƙuri dan Allah Ɗalha muna tattare ɗakin ne da yake tayis ɗin ƙasan gadone ya fashe”.
Cikin shan iskar yace.
“Ba komai Ummi”.
To tace kana taje ta wonke gero, sannan ta fito da ruwan tsarin tazo.
Tana zuwa ta bawa Shatu cikin ramin ta watsa ruwan.
Kana ta fara tura ƙasar da kuma fashesshe-fashesshen tayis da fulo ɗin tanayi tana yayyafa ruwan.

Dai-dai lokacin Jamil kuma ya shigo.

Ganin yadda hannunta yaketa karkarwane yasa ya tayata tura ƙasar saida suka gyara komai fes kamar ba fasawan ganganci akayiba.
Kana ta miƙe tare dasa hannun hagunta ta riƙo na damanta tana cewa.
“Shima Yah Sheykh dole zaiji wani abu a jikinshi duk inada yake”.
Sai kuma tayi shiru tare da rumtse idanunta tace.
“Wash hannuna”.
Cikin sauri Ummi tace.
“Sannu hannun ya gaji ko”.
Kai kawai ta gyaɗa mata.

A haka suka fito falon. Kai tsaye bedroom ɗin ta ta nufa.

Shi kuwa Jamil yayiwa Ɗalha jagoro,
Suka shiga suka gyara wurin da aka fasa ɗin fes.
Kana Ummi ta share wurin ta goge, sannan suka tura gadon suka maidashi.

Nanma ta ƙara gyara ɗakin Jamil kuwa ya ɗauki Ɗalha ya maidashi wurin aikinshi.

Ummi na gamawa taja ƙofar ta rufe tana al’ajabin wannan abu da ta gani da idonta.
Kitchen ta wuce ta ɗaura musu Lunch tana kiran Umaymah ta gaya mata duk abinda ya faru.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kaɗan daga cikin mafarkan da nakeyi kan Sheykh ya auro ba fulatar daji sun fara tabbata.
Ya Allah kasa abinda zai faru a sanadin shigowar Shatu masarautar Joɗa ne kake nunamin a mafarkaina”.
Umaymah ta faɗi lokacin da Ummi ta mata bayanin abinda ya faru.
“Amin Amin, Ummi tace kana ta katse kiran jin muryar Aunty Juwairiyya da Hibba.”

Umaymah kuwa da sauri ta kira Lamiɗo ta gaya mishi abinda ya faru.
Murmushi yayi irin nasu na manyan sarakuna yace.
“Alhamdulillah warakafa nan shigowa masarautar Joɗa baki ɗayanmu zamu rabu da mugun iri a cikinmu, kada ki gayawa kowa Khadijatu kinji ko”.
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
“In sha Allah kuwa ko Jadda bazan gaya mishi ba”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Masha Allah, Allah ya miki al’barka Khadijatu da ace duk ƴan uwa haka suke riƙe ƴaƴan yar uwarsu da zumunci ya ƙara ƙarfi kin musu abinda mahaifiyarsu bazata iya musuba”.
Amin Amin tace kana ya katse kiran.

A cikin ɗakin Shatu kuwa.
Wani irin…!

                        By
          *GARKUWAR FULANI*

Ya ruggumeta da kyau a jikinshi.
Jinyadda taketa fizge-fizgen zata kwance kanta.
Wani irin tsuma jikinshi ya rinƙayi can cikin naman jikinshi yake jin tsuman.

A hankali ya manna kanta, kan faffaɗan ƙirjinshi,
hannunta mai ciwon data ɗaura a tsakiyar kan natane ya zubawa ido.

Sosai hannun yayi jazir sai kelli yaki, alamun kumburin da yayi.
A hankali yasa hannunshin ya tallabo hannun.
Wani irin ihu tasaka da ƙarfi.
Sai dai bai bari ihun ya fito daga bakinta ba, yayi maza ya rufe mata baki da tattausan tafin hannunshi yana ta mai-maita.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Tabbas da in ya barta ta kurma ihun shike nan ta tabbata zautacciya,
yin ihun da take son yi dai-dai yake da sihirin ya gama shiga jikinta ya ratsa zai kuma haukatata.
Shiru tayi tana zazzare idanunta da hawaye ke zuba babu ƙaƙƙautawa, shi kuwa Sheykh a hankali ya janye hannun nata data aza a kai ya tallabeshi da tafin hannunshi.
Sannan ya manna ƙirjinshi da nata ƙirjin da kyau.
Har suna iya juyo bugun zuciyar juna.
Sunkuyo da kanshi yayi tsakanin kafaɗarta da wuyatan

Bakinshi ya saita cikin kunnenta.
Hure gashin daya baje kan kunnen yayi ya matsa,
sannan ya kawo bakinshi gab da kunnenta har tattausan lips ɗinshi na taɓa tattausan kunnenta.

Lumshe idonshi yayi tare da gyara tsayuwar nasu da kyau.
Ita kuma sai fiffizgewa take sonshi jikinta duk yana karkarwa ga zufar dake tsiyayo mata.

Hannunta dake cikin hannunshi ya kalla yadda yaketa rawa, gashi zafi jau kamar wuta.

A hankali yayi gyaran murya tare da yin bisimilla.
Cikin ɗan-ɗaga sauti ya fara karanta Suratul Baqra cikin kunnenta cikin fidda harrufan da karsashin yadda zai ratsa kunnuwanta.

Yanashi yana cire tafin hannunshi dake bakinta,
wani irin manna kanta tayi da ƙirjinsa,
ta lumshe idonta wasu hawaye masu ɗumi suka fara kwaranya.
hannunta na hagu dake da lfyar tasa bisa kafaɗanshi ta zagayo wuyanshi da kyau.

Shi kuma hannunshi da ya janye daga kan bakinta ya maida kan ƙugunta ya ruggumeta tsam a jikinshi.

A haka yaci gaba da karatu, in yazo wasu ayoyin yakan maimaita karshensu kafin ya kuma kama forkon na gaba.

A hankali ta fara sauƙe wasu tagwayen numfarfashi, ji takeyi azaba da raɗaɗin yana ɗan lafawa.
Al’farma Annabi da Alqur’ani kenan.
A hankali ta daina duk fizge-fizgen ta dawo sai kukan da takeyi mai sauti amman sautin a hankali ne.

Kuka take sosai ganin hakane, ya gyara tsayuwar tasu.
Kana ya tallabo kanta ya kalleta.
A hankali ya girgiza kanshi tare da jawota suka nufi bakin gado.
Yana cewa.
“Uhummm baku samu wurin zamaba a kanta in Sha Allah bazamu zauna inuwa ɗaya dani da kuba, zaku bar jikinta.”

Ajiyeta yayi kan gadon kana shima ya hau ya zauna.
da sauri ya riƙo hannunta da take son maidashi tsakiyar kanta ɗin.

Karatu ya fara yanayi yana ɗan hura mata sassanyan iskan bakinshi.
Tub, tub, tub, haka yake ɗanyi tare da fesa iskar, kana ya zuba mata ido cikin idanunta.
A hankali tayi ƙasa da kanta.

Shi kuwa haɗe fuska yayi tare da cewa.
“Ɗago ki kalleni mana”.
Kai ta girgiza alamun a a.
Shikuwa hannunshi ɗaya yasa ya tallabo haɓarta, dan ta kalleshi da sauri ta rumtse idanunta.
Cikin kausasa murya yace.
“Buɗe idon ki kalleni!”.
A hankali ta buɗi baki cikin irin Muryar da yaji tayi mgna kwanaki dashi tace.
“Bazan iyaba, kunyarka nakeji!”.
Watsa mata wani kallo yayi tare da cewa.
“Ƙarya ne, bakiji kunyan Allah’n daya haliccemu ya halicceku ya kuma yi mana iyaka a tsakaninmu ya hanaku cutar damu, ta hanyar mazonsa ya ƙaiyade muku dukkan motsinku, ya hanaku cutar da bani Adam.
Duk bakiji kunyarsu ba, kika shiga jikin yarinya ƙarama, kina sata yin wasu abun da ba halinta ba,
bakiji tsoron Allah daya hanakuba.
Bakiji kunyar iyayenta ba, kina cutar musu da ɗiyarsu sai ni?”.
Cikin sanyi murya cike da alamun tsufa, tace.
“Ni bana cutar da ita, Ni ba muguwa bace, ban taɓata cutar da ita ko wani nataba duk tsawon shekarun da nake tare da ita”.
Da sauri cikin faɗa yace.
“To meyasa zaki shiga jikinta”.
A hankali cikin zubda hawaye tace.
“Ni tun tana jaririya nake jikinta, kuma ni makaran gadone na ahlinsu daga wurin kakarta mahaifiyar mahaifinta”.
Da sauri yace.
“Rufe min baki, makaran gado,
Ku kuɗine ko wata kadara ce, ku cikin kadarorin da Allah (S.W.A) ya lissafa cikin jerin jadawalin abinda za’a gada?.
Ko dan kinga ina binki a hankali ne yasa zakiyi min zancen banza na mutanen banza”.
A hankali tace.
“Jikana ka kontar da hankalinka muyi mgna”.
A fusace yace.
“Waye jikan naki, kina Jinnu ina bani Adam ta ina na zama jikanki.
An ƙi a kontar da hankali tsohuwa dake kinzo kin liƙewa yarinya kina ƙoƙarin sata tana yaye suturar jikinta tana shirin yin ihu.
Ko baki san cewa matar aure bace, baki san daraja da kimar dake cikin aure bako?”.
Cikin fushi itama tace.
“Ni bani nasata yarda kallabin kanta ba, zafin ciwo da takeji ne ya gigitata yasata yarda kalkabinta.
Sannan batun ihu da kakeyi kuwa.
Aikin da mugayen Masarautar Joɗa sukayi data taɓane yake shiga jikinta.
Ni kuwa na zone sanadin karatun Rugyan da kayi ta mata, amman duk wancan abun da takeyi ni bana kusa ma.
Kuma ni ba mai cutarwa bace.
Batun darajar aure kuma na fika sani.
Kai kama tsaya inda takene bare ka raya auren ka tabbatar da ita matarka ce kai mijinta ne?.
Kasa sabgogi a gabanka, kana sane da magautanka sun saka a tsakiya kayi, burus dasu, suna neman rabaka da rayuwarka.
Ita kuma dole in taimaketa sannan dama Aysha in dai bata da lfy ko zazzaɓi ne tana kuka haka ciwonta yake.”
Cikin haɗe fuska yace.
“Eh wato da ban ƙonaki bane, kikemin baki ko. T taimako bana son taimakonki ki fitamin a jikin matata, bana so, zakisa tayi ihu ta fita tsakiyar masarauta bayan kin san inada magautan to meyasa zaki nemin abinda zaisa magautana farin ciki.
Tai mako kuma bama so, muda mukeda ubangijin taliƙai wanda yasan zahiri da baɗinin shi yake taimaka min, ba tare da yasa mana ciwon kai ko fita haiyaci ko kukaba dan haka fice min a jikin matata”.
Murmushi tayi tare da jinjina kai kana tace.
“Matarka kuma yau”.
A hatsale yace.
“A a matarki ce, in ba matata ba?.”
Sai kuma yayi bisimilla zai fara karatu da sauri tace.
“Tsaya Muhammad Jabeer ɗan Habibullah jikan Nuruddee, Bubayero, Joɗa, Sule Usmanu jinin sarki Muhammad Bello, ni bazanyi faɗa da kaiba kafi ƙarfin haka duk da ni ba cutar daku nakeyi ba. Naga ranka ya ɓaci ina jinin.
Wai matarka kace ko?”.
Wani irin kallo yayi mata tare da ɗago hannun shi zai shararamata mari yana cewa.
“Wai ne ma ko?”.
Da sauri tayi murmushi tare da cewa.
“Kamar gibtawar ido zan gudu jikinta, ka kwaɗa marin a kanta”.
Ai fa a kufule ya kai marin.
Hannunshi na isa fuskarta tana yin atishawa.
Zafin marin ya sauƙa kan fuskarta cikin azaba ta ɓare baki tare dasa kuka tana mai shafa haɓarta ido na zubda hawaye a gigice idonta na ganin duhu sabida zafin marin bata gama dawowa haiyacinta ba murya na rawa tace.
“Wayyo Allah na me nayi maka zaka mareni, ka barni inji da ciwo ɗaya mana”.
Hararanta yayi tare da miƙewa ya sauƙa gadon yana cewa.
“Mutun jiki duk al’janu, sai hegen bakin rashin kunya mutun in ba lfy bazaiyi addu’a ba sai kuka”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button