GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Da suke konce kamar gawarwaki.

Tsaye suke jikin motar, yayinda biyu daga ciki dakeda uniform ɗin police officers, kuma suna cikin motar da itama ta police ɗinne.

Ɗaya daga cikin mutun huɗu dake gaban motarne, yasa hannu ya rufe ƙofar, sannn ɗaya kuma ya kira waya, cikin yaren Ɓachamanci yace.
“Mun sace mutun biyar, uku yaran gidan Malam Liman ne, biyu daga ciki yaran gidan Ahaji Horo ne”.
Ɗan jim yayi alamun karɓar umarni.
Tsawon daƙiƙu biyar sannan ya ƙatse kiran kana ya juyo ya kalli, sauran tare da cewa.
“Yace ku, ku tafi dasu a cikin motar, ku wuce dasu,inda kuka shirya, mu kuma yace mu ɗan tsaya nan, yanzu zaiyiwa shanun Rugar Malam Liman kiranye da dogon fito.
To in shanun suka nufi inda yake ba mamaki wasu su biyo shanun daga cikin makiyayan, to yace idan sun biyosu mu kashesu!”.
Kusan a tare suka sara mishi tare da busa sigarin dake hannunsu.
Nan mutanen cikin motar sukaja, suka tafi.

Su kuma saura mutun huɗun, komawa mafakarsu sukayi.

Can cikin tsunƙurun dajin kuwa.
Ba’ana ne zaune cikin taron matasan ƙabilar ɓachama da a ƙalla sun kai goma, cikin kausasa murya da bada umarni yace.
“Zanyi fito ɗaya zuwa uku, cikin daƙiƙu 10 shanayen Malam Liman da Alhaji Haro da wasu. Zasu baiyana, a nan.
Suna zuwa ku jasu ku fuskanci gabas, ta ƙasar Jihar Gombe zaku ratsa, kana ku nufi ƙasar chadi daga can.”
Shiru ya ɗanyi tare da zuba musu idanu, wani irin azzalumi murmushi yayi cikin barbarci ya kalli biyu dake kusa dashi wanda ƴan ƙanwar Bukar ne su barebari ne, cikin izaya yace.
“Kada ku kauda ido akan ko wacce gonar makiyayin da zaku wuce ta gabanshi, ku shiga gonakin manoma, kuyi kiwo a ciki.
Idan manoman suna cikin gonakin in sun muku mgna ku kashesu, sannan ku gudu da dabbobin yankin wurin”.
Cikin barbarci ɗaya daga cikin su yace.
“Ba’ana, tsayuwa kiwon bazai ja mana tsaikoba, har cekiyar ya riskemu ba tare da munyi nisa ba”.
Murmushi yayi mai cike da fajirci sumar kanshi ya shafa tare da cewa.
“Ba’akana Ku kiwaci duk gonakin manoma, hakanne zai jawo faɗa tsakanin MAKIYAYA da manoman, daga haka saiku gudu, kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, domin su mutanen duniya sun ɗauka duk wanda suka gani da dabobbi yana kiwo, BAFULATANI NE, sam mutane sun kasa ganewa cewa ba sai Fulani kaɗai ke kiwoba, kaga mun tada faɗa mun kwashi dabobbinsu, mun kashesu mun gudu, kuma in sunje kai korafinsu ga hukuma a kamasu ko a korasu ko azagesu, ace suke haddasa faɗa tsakaninsu da manoma, sun zama ƴan ta’adda a idon duniya. Mun kwashe dukiyoyinsu”.
Dariya sukayi baki ɗayansu, kana suka sara mishi, juyawa yayi, ya fuskanci gabas kana ya durƙusa, ya zuba guiwowinsa duka biyu a ƙasa, yatsarsa manuniya ta hannun hagu ya kafa a ƙasa, kana yatsarsa ta hannun dama kuma, ya toshe kunnenshi na dama, da ƙarfi ya rufe idanunshi kana, ya tsuke bakinsa ya rinƙa zuro iskar wata zazzafar fito mai bala’in sauti.
Su kuwa sauran duk rufe ido sukayi dan jin fiton sukeyi tamkar zai fasa musu dodon kunne.

Shi kuwa Ya Lado yana cikin kiwonshi kawai yaga gaba ɗaya, shanun sun juya sun fuskanci gabas, kana sun ɗaɗɗaga kunnuwansu sama, daga baya kuwa sunata karkaɗa binɗinsu.
Cikin mamaki yake ratso tsakiyarsu.
Dan in makiyayi yaga dabbobi suna haka yasan akwai abun da suka gani, ko mutun ko iska, ko maciji ko dai wani abu na daban to sukanyi wannan alamar dan sanar da makiyayinsu.
So ganin hakane yasa Lado ya ƙara kutso kai cikinsu.

Su kuwa dabbobin gaba ɗaya fiton da Ba’ana yake hurawane ya cika musu kunne, ai fa a take suka nausa a guje suka fuskanci gabas, da wani irin masifeffen gudu.
Shanu da dawakai na gaba tumaki da awaki na baya hatta belbelun dake cikinsu, suna kiwo binsu sukayi.
Cikin ƙarfi Ya Lado yayi wani irin ihun wanda dashi suke kiran dabbobinsu, amman ina basu juyoba.

Da gudu ya fara binsu kana yana ihun neman taimako a wurin sauran makiyayan su.

Amman da yake gudun dabba dana mutun ba ɗaya ba,
Sun mishi nisa mai tarin yawa, hakanan shi kuma yayiwa sauran makiyayan dake biyoshi a guje su kawomishi agaji ya musu nisa.
A haka suka rinƙa gudu,
waɗannan mutun huɗun dake laɓene suka fito suka, tareshi ba zato ba tsammani kawai yaji an burma mishi wuƙa juyowan da zaiyi kuma yaji an kuma burma mishi wuƙaƙe a tako ina na jikinsa.
A nan take ya faɗi babu rai.

Su kuwa nan sukabi shanun da gudu.

Koda sauran makiyayan suka iso inda gawar Ya Lado take.
Hankalinsu yayi masifar tashi.
Tabbas sun san babu masuyi musu wannan aikin sai ɓachama.
Ko hanƙo kurar dabbobin basayi.
Hankalinsu yayi mummunan tashi ganin gawar Lado, ga kuma tashin hankali da firgici rashin ganin su Gaini da Giɗi da Seyo Manunu da Sale.
Junaidu ne yayi sauri ya kira mahaifinsu Ahaji Horo a waya ya sanar mishi halin da ake ciki.

Wannan mummunan labari yayi matukar firgita al’ummar Rugar Bani hankalin kowa ya tashi.

Hankali Bappa kuwa in yayi dubu to ya tashi,
kuka cur-cur yakeyi da idanunshi.

Junainah kam kuka da ihu harda burbuwa takeyi tana cewa.
“Wayyo Ya Lado, Bappa ku nemo min Ya Gaini na da ya Seyo”.
Sai ta kuma faɗa jikin Ummey daketa kuka tamkar ranta zai fita,
cikin kukan take cewa.
“Ummey kicewa Bappa suje su nemo min Ya Giɗi na, kada su bari a kasheshi kamar yadda aka kashe Ya Hashimu da Ya Isa, da kuma Yaya Lado”.
Babu mai iya bata amsa a cikin wannan gida.
Duk da tarin maƙota da suka cika gidan.
suna zagaye da Inna wacce, take sume tunda taji yaranta Rai uku babusu babu dalilinsu su ko gawarsu ba’a ganiba ga kuma mutuwar Lado wanda shine yasata, sumewa.
Faɗin tashin hankali da mutanen Rugar Kikan ke ciki bazai taɓa misaltuwa ba.
Saidai ƙunane wanda duk mai imani zai iya ƙiyastashi a ranshi.

A cikin garin kuwa tuni Arɗo Yabani yasa anyi shela anyi taron gaggawa, kowa ya shirya za’a shiga daji neman su Gaini, ko Allah zaisa a samosu.

Haka matasa kusufa-kusufa suka rinƙa kusa kai cikin daji suna ratsa tsaununka da kozozzabai.

Bappa kuwa da Arɗo Yabani da Ahaji Haro, da Ahaji Umaru ne da sauran dattawan rugarsu dana kewaye, gawar Lado suka ɗauko suka dawo gida da ita da sauran shanayensu gaba ɗaya matasa kuma suka bazama nemansu Gaini.

Su kuwa sauran matasa majiya karfi daji suka rinƙa ratsawa.
Amman babu koda kurar dabbobin nan, bare alamun su Gaini illa iyaka dai takalmansu da suka tsinto.

A Rugar Bani kuwa, hankali na matukar tashe, Bappa ya tasa gawar Lado a gaba wacce sunyi mata wonka sun kimtsata cikin sutura kamar yadda shariya ta tanadar.
Kuka mai tsananin cin raine ya kwabcewa Bappa, yana ruggume da gawar.
Inna ma da yanzu ta farfaɗo da kukan ta farfaɗo, kuka takeyi tamkar ranta zai bar gangan jikinta.
Hakama sauran matan maƙota.
Hiden da Binto ma kuka sukeyi sosai a gidajensu sabida ɓacewar samarin su.

Dattawan ne sukayi ta bawa Bappa haƙuri da tausan zuciyarshi.
Ganin dare yayine yasa akace dole a bar gawar tayi kwanan keso.

Su Sule, Iro, Ado, Junaidu, Madu, Ari, Sani, Ibi, ja’eh, Ori, Binbi, dama sauran samari majiya karfi kuma kab sun cikin daji.

Haka suka kwana a can. Suna tafiya suna nema, kafin gari ya waye, wasu sun isa har jihar taraba, wasu Gombe, wasu har bauchi, wasu har cikin iware da mutun biyu na taraba,
Wasu sun nausa da nisa, sabida in dai tafiyace bata taɓa bawa bafulatani tsoroba domin anyi ittifaƙin duk ƙabilun duniya babu ƙabilar da takai ƙabilar fulani saurin tafiya da jumurin doguwar tafiyar ƙafaba, bayan laraban da.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button