GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A can sashin Sheykh ya samesu, Juwairiyya da Jalal ɗin da Affan sun tasashi a gaba, Affan yanata kuma, shi kuwa Jalal sai tattaune laɓɓansa yakeyi, da sauri Jamil ya iso cikin sanyi yace.
“Affan je ka gayawa Mama”.
Da sauri Affan ya juya har zai fita kuma ya dawo jin Juwairiyya na cewa.
“No Affan kada kaje, ka gaya mata, nasan yanzu tana bacci ne”.
Shi kuwa Ya Jafar sai ya shiga ɗakin nan ya fito ya shiga wancan ya fito yana kuka kuma.

Shigowar Abbane ya sasu su Jalal duka fita.

A hankali Abba ya kamo hannunshi suma suka fito, da mamaki a fuskar Jamil ya bisu da ido.

Shi kuwa Abba yana riƙe da hannun babban ɗan nashi suka wuce har makoncinsa,
Gefen gado ya kontar da dashi, kana a hankali yake shafa kanshi cikin taushi da tausayawa yace.
“Jafar kayi haƙuri kayi baccinka kabar kuka, Sheykh yana lfy lau, ya tafi ƙasar Saudia ne shida kakarku Sitti.”
Shiru yayi yana kallon mahaifin nashi.
Shi kuwa Abba, kanshi yake shafawa yana kontar mishi hankali a take yayi baccinsa.

Bayan sallan ishane Jamil yaje wurin Kakansun ya sanar mishi halin da ake ciki ya ƙafarsa cewa.
“Allah rene, magar gsky kace Hamma Jabeer ya dawo, sabida abin ya Jafar yana tsananta in bayanan”.
Murmushi kakan nasu yayi tare da cewa.
“Uhum ai Allah ya sauƙaƙa abinda zai taso Sheykh ya dawo ba tare da an gama dai-dai-ta abinda ya kaishi ba Dole shi wannan mai saɓulellen mondon Jalaluddin shi zai dena yawon iskanci ya zauna ya kula dashi tunda yafi kallonshi a madadin Sheykh”.
Cikin takaici Jamil yace.
“To ni zan kai Ya Jafar saudia wurin Sheykh ɗin suci gaba da zama a can in sun so, tunda dai kun san Sheykh shine GARKUWAnmu”.
Cikin kontar da murya kakan nashi ya ɗan tausasashi kana yace in yaje ya turo mishi Jalal.

A can Saudia kuma, sosai aketa shirya yadda ɗaurin Auren Sheykh da Jazrah zai kasance, duk da basu sanar mishiba, sabida kashedin da Sarki Jalaluddin da Nuruddeen sukayi musu dan ko yaushe in dai ana shirya batun aurenshi muddin yaji sai yaƙi fir yayi ta kaucewa dole a ƙarshe aure ya fasu, to wannan abunne yasa ba’a sanar mishiba.
Sai dai yasan batun zuwan da Jazrah take sashinsu wai nune da ita suke zaɓa mishi in tayi mishi.
To shi kuwa bayan gaisuwa ko sannu bai taɓa haɗasu da itaba.

Haroon kuwa da Jannart sunata shirye-shiryen dawowa gida Nigeria.

A garin Bani kuwa,

Yau tun bayan sallan isha’i yaro ya shigo yace, Ya Salmanu yana sallama da Aysha,
haka kuwa ta fita taje,
Suka zauna a dakalin ƙofar gidan nasu suna hango yadda,
Yara keta wasa a dandali domin ranar jumma’a tafi ko wacce rana a garesu wurin shanawa.

Ya Gaini ne ya fito riƙe da hannun Junainah, a bakin ƙofar suka wuce Su Shatu
Bayan sun gaisane ya wuce riƙe da hannun ƙanwar tasa,
Murmushi Salmanu yayi tare da cewa.
“Shatu, inaga dai aurenmu dana babban yaya rana ɗaya za’ayi shi”.
Murmushi itama tayi, tare da cewa.
“Tab shifa har an kai kayan aure”.
Ido ya ɗan lumshe tare da cewa.
“To ai in kin bani dama nima gobe-goben nan sai a kawo kayan aurenmu ko?”.
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta, alamun jin kunya.

Su Ya Gaini kuwa kai tsaye ƙofar gidan Ahaji Haro sukaje,
A bakin ƙofar suka tsaya, sunkuyowa ya ɗanyi a hankali yace.
“Yauwa ƙanwaliya maza shiga cikin gidan kicewa Addanki Bintu tazo”.
Cikin happy tace. To kana ta shiga cikin gidan da sallama.

Kamar yadda gidansu yake hakama gidan Ahaji Haro duk suna zaune a tsakiyar gida da yaranshi da matanshi sunata hira, bayan ta gaidasune taje gefen Binto cikin raɗa ta gaya mata saƙon ƴaƴansu.

Wani ɗan kekyawan matashi ɗan kimanin shekaru sha takwas mai sunan Junaidu ne ya kalli Junainah cikin tsananin so da ƙaunar yarinyar yayi murmushi tare da taɓa mamanshi cikin raɗa yace.
“Inno ga surkarki in Allah ya yarda”.
dariya suka ɗan yi dan kowa yasan Junaidu yasan son da yakewa Junainah tun tana ƙaramar ta.

Ita kuwa Junainah hannun Binto ta riƙo suka fito tare,
Junaidu na biye dasu a baya,
Koda suka fita, Gaini ne ya kalle Junaidu tare da cewa.
“Yauwa Junaidu raka min Junainah gida ko”.
To yace kana yabi bayanta suna tafe suna hira, sunzo dai-dai ƙofar gidansu Ahaji Umaru ne suka samu Ya Seyo da Hinde suna hirarsu.

Koda suka wuce, murmushi Junaidu yayi tare da cewa.
“Junainah sai yaushe zan fara zuwa muma muyi hira ne?”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Sai na ƙara girma kafin nan Addana tayi aure”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ko dai bakya so nane”.
Da sauri cikin yarinta tace.
“A a ina sonka mana”.
Dariyar jin daɗi sukayi baki ɗayansu, sun zo kusa da ƙofar gidansu.
Ya Ba’ana ne sukayi kiciɓis dashi, murmushi yayi tare da cewa.
“Yauwa Ƙanwaliya kuzo mu shiga in baki aike ki kaiwa Shatu”.
To sukace kana sukabi bayanshi, a tsakar gida suka samu, Iya Bultu majaifiyar Ya Ba’ana kena ƙatuwar mace baƙa ƙarin da ita, ga jajayen idanu, fuskarnan a haɗe ta kalli Junainah dake gaidata da fullanci cikin tsananin tsawa tace.
“Ke tafi daga nan ƴan iskan fulani masu jajayen kunnuwa, dan uwarki Ni ba fillatace da zaki gaidani da fullanci, hegu kwarkwasa fidda mai gida a gidanshi yan iska masu kama da al’janu, in sha Allah ƙarshen zamanku a wannan yanki yana nan tafe”.
Da sauri Junainah ta koma bayan Junaidu, shi kuwa Junaidu wani irin tafasa zuciyarshi keyi akanme zata zagesu dan kawai sun gaidata da fullanci.
Bukar ne mijinta wanda yake babarbaree ya kalleta tare da cewa.
“Kuma dai al’barkacin fulanin kikeci”.
Ba’ana ne ya ɗan harari mahaifin nashi tare da waskewa yace.
“Fulani kecin al’barkacin ta dai, tunda kowa ya sani wannan yankidai na Ɓachamawa ne, ba fulaninba”.
Cikin ƙarfin hali Junaidu yace.
“Ato ai dai ba kyau aka bamuba da kuɗin mu aka bamu, kai kamma ya Ba’ana kaifa bawanmu ne tunda kai babarbarene”.
Wani irin suka kalawan yaron suka mishi a ƙahon zuciyarshi amman sai ya dake,
ledan su ayaba da inabin ya bawa Junainah tare da cewa.
“Uhu Junaidu kenan aini ba bakanuri bane ni ba Bachamene, Dan da in zama bawan fulani gwara in zama bawan karnuka”.
Haka nan kalamansu ke tafasa zuciyar Junainah da Junaidu, haka yasa fuska a hade suka juya suka tafi, har sunje bakin ƙofar fita Ba’ana yace musu.
“Yauwa kuce mata ina zuwa yanzu bari inyi wonka”.
To sukace kawai suka fita suka tafi.

A ƙofar gidansu suka tsaya gaban Ya Salmanu da Aysha, ledan Junainah ta ajiye a tsakiyarsu cikin jin haushi tace.
“Addana gashi inji ya Ba’ana wai in kawo miki, yace kuma yanzu zaizo wai wonka kawai zaiyi”.
Tana kaiwa nan tayi cikin gida shi ma Junaidu Binta yayi a baya, har gabansu Ummey ya tsuguna suka gaisa kana yace.
“To Ummey ga Ƙanwaliya na rakota Ya Ganin ne yace in rokata har cikin gida”.
Murmushi Ummey tayi tare da cewa.
“Mun kuwa gode, ka gaida min Innonka kace mata, in Allah ya kaimu gobe ta turo min Hari tazo tamin kitso”.
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“To saida Safe Bappa”.
Allah ya bamu al’khairi sukace baki ɗayansu.

Daga nan ya fito, har ya wuce Ya Salmanu yace.
“A a Junaidu zoka amshi tsarabar mana”.
Cikin girmamawa yace.
“A a Ya Salmanu ya isheni”.
Cikin kula Salmanu yace.
“Ni kam yaushenene zaku koma school?”.
Da sauri yace.
“Saura kwana biyar hutunmu zai ƙare”.

“To Allah ya taimaka yanzu aji nawa kane”.

Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
“Ina SS 3 ne fa, Ya Salmanu na kusa gamawa ai”.

“Masha Allah, Allah ya taimaka”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button