GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ita kuwa Inna Amarya ta ɗauki sauran ta nufi cikin ɗakin Ummey dashi.

A hankali ta ratsa gefen Sheykh ta ajiye kwaryar a tsakiyar su.
Kana a hankali tace.
“Bismillah ga ruwa”.
Murmushi mai yelwa Sheykh yayi tare da cewa.
“Mun gode”.
Jalal kuwa hannunshi yasa ya ɗan tsinko gefen nonon inabi kana ya fara kaiwa bakinshi yana tsinka.
Ido ya lumshe tare da cewa.
“Wai ni kam Adda Shatu kuna da Fridge ne a garin nan”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Bappa kuwa miƙewa yayi ya fita yana cewa.
“Toh bari inje nan kusa kafin kusha ruwa”.
To sukace sanin bazai zauna ba.

Ita kuwa Shatu ruwa ta koma ta kawo musu cikin kwanon sha na asalin gargajiya.

Ajiyewa tayi tana kallon Affan da yake lumshe ido yana shan kindirmon.
Jamil kuwa Ayaba yakeci.
Yah Jafar ma nonon yake Sha.
Shi kuwa Sheykh dabinon yake ci.
A hankali ya kalleta tare da cewa.
“Ni zan sha nonon amman zumar bata ji minba a ƙaro min”.
Da sauri tace to tare da miƙewa a nitse ta shiga cikin ɗakin Bappa.

Ido ya ɗan zuba mata lokacin data fito riƙe da akoshi ta ajiye a gabanshi tana buɗe wa.
Da sauri ya ɗan jawo akoshin ganin asalin farar zuma da sakarta, yatsarsa yasa ya laso yasa a baki.
Girarshi ɗaya ya ɗan ɗaga mata tare da cewa.
“Kefa baƙuwa ce, zaki shige musu har ɗaki”.
Da sauri tace.
“Tab baƙuwa kuma ni da gidanmu”.
Yana mai lasan zumar yace.
“Gidanku na can masarautar Joɗa”.
Murmushi tayi kana ta miƙa ta koma wurin su Ummey.

Sosai suka sake anata hira da dariya ga sanyin safiya.
Ga yanayin garin ga farin ciki.

Junainah kuwa tana ruggume da Afreen tanata kiciniya da ita.

Ganin Inna Amarya ta koma Kitchen yasa Shatu Binta a baya.
“Inna Amarya me kike dafa mana ne?”.
Juyowa tayi tana kallonta bayan ta sauƙe tukunyar kana tace.
“Tuwone miyar kase da man shanu.
Sai Danderun Zabbi”.
Da sauri ta matso tare da cewa.
“Kai Inna Amarya kin biyani dama na dade banci miyar Kase ba”.
Gefenta ta zauna tare da jawo akoshin dake gefenta babba da karami.
Danderun ne a ciki sai tururi da ƙamshin yake zubawa.
Da sauri ta rufe.
Kana ta buɗe manyan da sukafi wannan tuwon ɗanyar shinkafane anyi mata asalin kwasan gargajiya an lailaye samanshi da man shanu.
Rufewa tayi.
Tana kallon Inna Amarya data buɗe tukunyar miyar data sauke.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Wannan miyar harda ta gobena”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Toh Shatu yanzu dauki tuwon da Danderun ki kai musu sai kizo ki kai musu miyar.
Da sauri tace to.
Ta ɗauka ta kai musu.
Ta dawo ta kai nasu Ummey kana tazo.
Ta zauna tana kallon yadda take zuba miyar.
Ƙwaryar dake gefenta ta buɗe.
Nanma tuwon ne da alamun na su Yah Giɗi ne.
Gefe kuma kwanukan Bappa ne.

Motsowa tayi tana cewa.
“Inna Amarya su Ummey duk basu wani damu da nama, Amman waɗan can kuraye ne.
Irin Jalal da Yayanshi sunfi son duk loma su tsakura da nama”.
Dariya Inna Amarya tayi tare da cewa.
“Yoh kice irin Giɗi ne su”.
Dariya tayi da sauri ta juyo jin Yah Giɗin nata dake Ruggume da Afreen yana cewa.
“Toh in banda irin Shatu wa zaiƙi nama, ko sunanshi mafa yana da daɗin ji”.
Murmushi tayi tuno lokacin da ya dirka mata dundu a tsakiyar bayanta sabida ta hana a yanka tsuntsuwar Boleru wacce da Ummey aka yanka”.
Ita kam inna Amarya naman ta kara musu.
Ita ta dauki nasu Ummey ta kai musu.

Ita kuwa Shatu ta kaiwa su Sheykh.
Murmushi tayi ganin tuni Jalal ya buɗe akoshin Danderun.
Yana ganinta yace.
“Yauwa Adda Shatu a kawo mana tray’n mana ko plate”.
To tace.
Kana taje ta kawo musu tirurruka guda biyu.

Ajiyan zuciya Sheykh ya sauke tare da cewa.
“Wai anya kuwa kunci abincin safe?”.
Da sauri Affan yace.
“Bamu ciba”.
Murmushi Yah Jafar yayi tare da cewa.
“Koma dai munci ai yanzu hantsi ya duba ludeyi.
Dan haka Affan sa mana”.
Allah sarki rayuwa mai daɗi ba girman kai.
Shatu ta raya a ranta.
Shi kuwa Sheykh dariya yayi.

Shi kuwa Affan ludeyin duma yasa ya zuba musu tuƙeƙƙen tuwon nan.
Kana ya zuba musu miyar kasen da yaji nama da kifi banda a saman tuwon.
Jalal kuwa ƙara min tray’n ya jawo.
Danderun ya juye a ciki fiye da rabi.
Ita kam Shatu juyawa tayi ta tafi.

Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Affan, Jamil, Yah Jafar.
Sun haɗa hannu cikin kono ɗaya suna cin abinci cike da gamsuwa da shaƙuwa da ƙaunar juna.

Haka nan yaji wani irin daɗi.
Jalal ne ya ɗan matso gabanshi da tray’n tare da cewa.
“Ni dai Allah ya sani ba cin tuwo zanyiba, Hamma Jabeer muci Danderun”.
Jamil ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.
“Manyan kuraye ba”.
Eh ɗin Jalal yace kana sukaci gaba da ci suna hira.

Ita kuwa Shatu bakin kitchin ɗin ta koma.
Gefen Yah Giɗi ta zauna.

Tare da sa hannunta cikin akoshin abincin da yake cin.
Kana ta kalli Junainah dake gefenshi riƙe da Afreen tace.
“Junnu kaita wurin Ummi kizo muci mana”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Ni na koshi naci da Ummey na a ɗaki”.
A hankali ta ɗan juyo ta kalli ƙofar ɗakin Bappa jin Sheykh yayi gyaran murya.
Ido ya juya mata, alamun me takeyi.
Cikin jin daɗin yanayin tace.
“Ina cin abinci da Yah Giɗi na”.
Murmushi yayi tare da juya kai.

Shi kuwa Yah Giɗi dama ya kaiwa abokan Jalal dake can ƙofar gida zaune kan taburma a gindin bishiya.
Suma sunci.

Haka dai sukaci suka sha sukayi haniƙan.
Kana Shatu ta tattare komai ita da Junainah.

Bayan sun gama ne Bappa ya dawo nan suka sake sabuwar gaisuwa kana suka ci gaba da hira.
Sannan sukaje sukayi sallan azahar a masallacin ƙofar gidan Arɗo Bani.
Kana suka dawo sukaci gaba da hira.

Shi kuwa Ba’ana yana fita.
Ya kalli Babanshi cikin zaƙuwa yace.
“Baba Mata tana Rugar Bani tabbas tazo”.
Da sauri Bukar yace.
“A a Ba’ana banji lbrin ba”.
Da sauri yace.
“Ga nan zobe na yana gaya min kana cemin a a”.
Sai kuma kawai ya juya ya nufi.
Bakin garin inda yasan zai samu Baroon yana zuwa yace.
“Baroon taso muje gidan malam liman indan mun isa ni zan zagaya ta baya kai kuma ka shiga ta ƙofar gida.
Ina da tabbacin yau Mata
na nan kuma yau zan tafi da ita.
Yanzu bari in kira su Droo baki ɗayansu.”
Da sauri Baroon yace to.
Kana sukayi maza suka nufi cikin garin.

Shi kuwa Ba’ana ya kira duk sauran yaranshi suka biyo bayanshi.
Ta bayan gidan suka zagaya.
Shi kuwa Baroon ya shiga cikin gidan kai tsaye sabida sanin Sheykh na ciki kuma zaije ya bashi bayani ne.

Yana shiga kuwa Sheykh ya yafi toshi da hannu da sauri ya iso.
Bappa kam ido ya zuba musu jin Baroon nayiwa Sheykh duk bayanin abinda Ba’ana yake shiryawa.
Murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
“Yanzu yana bayan gidan nan kenan?”.
Da sauri yace.
“Eh dashi da sauran yaran”.

Da sauri Sheykh ya kalli Jalal tare da cewa.
“Ka gayawa su Khalid su kula da duk wani dake jikin gidan”.
To yace kana ya kira su ya sanar musu.
Nan take kuwa suka miƙe suka fara ɗan zirya

Ajiyan zuciya mai nauyi Bappa ya sauke lokacin da Sheykh yayi mishi duk bayanin abinda ke faruwa.
Ya ƙara da cewa.
“Idan ban kamashi ba bazai daina bibiyar rayuwar Shatu ba, kuma zai iya ci gaba da yiwa mutane illa in ya rasata”.
Cikin sanyin jiki Bappa yace.
“Hakane”.

Dai-dai lokacin ita kuma Shatu ta fito cikin ɗakin.

Randunansu ta nufa.
Dai-dai lokacin kuma Ba’ana yana ta wurin ta bayan danga.
Tasa hannu zata ɗebo ruwa kenan taga zoben yatsarta ya kawo wani haske.
Da sauri ta miƙe tsaye.
Jin muryar Ba’ana cikin raɗa da leƙota ta tsakankanin karan da akayiwa danga a madadin katanka.
Da sauri ta dafe ƙahon zuciyarta jin muryarshi ras cikin kunneta murya cike da rauni yace.
“Mata! Mata!! Mata!!!”.
Ta sani duk duniya mutum ɗaya rak ke kiranta da wannan sunan.
Murya na rawa tace.
“Yah Ba’ana”.
Cikin rauni yace.
“Mata ina kika shiga kika mance dani.
Mata kika barni cikin ƙunci da ciwon rai da zuciya na rashin ki Mata wlh zan iya jure komai amman bazan iya jure rashin kiba”.
Kar-kar haka jikinta ya fara rawa.
Da sauri ta juya, da nufin zata koma ɗakin Ummey sai kuma ta tsaya tare da rumtse idanunta da ƙarfi.
Ganinshi ya ɓace ɓat ya dawo gabanta.
Cikin rauni yace.
“Ina zakije? Tafiya zakiyi ki barni!”.
Ya ƙare mgnar da rauni yana kuma ƙoƙarin kai hannunshi zai kamo nata.
Cikin tsananin ruɗani tace.
“A a, Yah Ba’ana kada ka taɓani ni matar aurece”.
Sai kuma ta kauce.
Da sauri shima ya kauce ya bita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button