GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin tsoro tace.
“Dan Allah Yah Ba’ana ka bar fito min”.

Da sauri Sheykh ya miƙe tsaye cikin tsananin tashin hankali jin furucin da Shatu keyi tare kuma da kakkaucewan da takeyi alamun ana binta.

Su Jalal ma kab miƙewa tsaye sukayi.

Shi kuwa Sheykh da sauri ya nufi inda take.
Dai-dai lokacin su Ummey ma kab Suka fito sabida karan da Shatu tasa.
Sabida riƙo hannunta da Ba’ana yayi ya fara ja.
A zahiri ita kaɗai ake gani amman a badini shike janta.
Cikin rawan jiki ta tashin hankali tace.
“Bappa Yah Ba’ana ne yake jana wai zai tafi dani.
Yah Sheykh zai tafi dani”.
Ta ƙare mgnar da ƙarfi da kuma sakin kuka.

Shi kuwa Ba’ana shima kukan yakeyi cikin rauni da tsananin so yake cewa.
“Mata yanzu wani kike cewa yazo ya ceceki ya rabaki dani.
Shin bakya so nane?”.

Dai-dai lokacin kuma Jalal ya iso gab da ita.
Da sauri duk suka buɗe baki tare kallon yadda Jalal yayi sama ya faɗi ƙasa tib sabida wani irin azabebben naushi da Ba’ana ya kima mishi.
Wanda su ba ganinshi sukeyi ba.
Cikin wani irin tafasan zuciya irin na sojojin Jalal ya miƙe tsaye tare da nufosu.
Jin Shatu na cewa.
“No Jalal kada ka iso zai illa taka”.
Ina bai kulaba sabida ranshi ya gama tafasa.

Ai kuwa kamar da fari, suka sake ganin Jalal yayi sama-sama yayi ƙasa har saida Ummey tayi kansa da gudu hannu tasa ta dagoshi.
Tare da juyowa tana kallon gaban Shatu cikin sanyi tace.
“Ayyah Ba’ana kayi haƙuri kada ka cutar min da ahlina nasan kai mai al’khairi ne a gareni.

Bappa ne ya matso shima a hankali hakama su Affan da Yah Jafar.

Shi kuwa Sheykh jingina kanshi yayi da jikin bishiyar Ceɗiya dake gefenshi.
Hannunshi na dama yasa ya tallabe haɓarshi yana mai bin inda Shatu take da wani irin kallo.
Sabida da fari zatonshi ko makaranta ne suka dawo.
So yanzu ya fahimci ba makaranta bane.
Hatsabibancin Ba’ana ne,
Nazari yakeyi yadda zai fito mishi ta sigar da dole ya karya lagonshi da takwabin addu’a.

Da sauri su Ummi duk sukace.
“Innalillahi”.
Sabida ganin Ba’ana ya baiyana kansa garesu.
A take kuma ya ɓace.

Sai ya kuma sake baiyana ya kuma bace, saida yayi haka sau uku kana ya ɓace sai muryarsa ke tashin cikin rauni yace.
“Baroon kaci amanata ina sane na Barka.
Nayi hakane dan ka jawo shi wannan mai jajayen kunnuwa ya kawo min ita har nan.
Ku a zatonku tarkonku na faɗa baku san cewa nawa tarkon kuka faɗa ba sa’ansu ɗaya nayi tuba na gaske bazan sake kashe raiba.”
Sai ya kuma bayyana still hannunshi riƙe da hannun Shatu cikin rauni murya na rawa tace.
“Ayyah Yah Ba’ana dan Allah ka sakeni kada ka rabani da ƴan uwana da ƴata”.

Wani irin jujjuya kai yayi tare da cewa.
“Bappa kun kasa cika min al’ƙawarin da kukayi min ko.
Kai kuma Baroon kaci amanata ka muna furceni.
Shatu ke kuwa kin yiwa soyayya ta ta gsky riƙon sakainar kashi.
Wani abu kuke tunanin zaifi min ciwo da zafi sama da rabuwa da Shatu”.
Sai kuma ya kalli Sheykh daya zuba mishi ido yana takaronto addu’o’i babu ƙaƙƙautawa ido cikin ido ya tsare Ba’ana da ido.
Shi kuwa Ba’ana murya a mace yace.
“Ko na bar barun a raye kaima watan wata rana zai ci amanarka tabbas zaici amanarka maci amana kuwa gubane”.
Cikin sauri suka juyo kan Baroon daya saki wata iriyar gigitaciyar ƙara tare da komawa bayan Sheykh.
Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa inda Shatu take tana nufoshi alamun Ba’ana na matsowa inda yake.
Da sauri sojojin dake wojen suka shigo da gudu

Lokaci ɗaya mutane suka fara tururuwan shigowa gidan sabida ihun da Baroon yakeyi yana kiran sunan Ba’ana yana bashi haƙuri.

Jalal kuwa da sauri ya kuma nufo inda Shatu take wanda da ita suke gane inda Ba’ana yake.
Cikin tsoron kada ya cutar da Sheykh ya nufosu.
Gib ya kuma ture Jalal tare da cewa.
“Ummey ki gayawa wannan yaron zan illatashi fa ya dena matsowa inda nake”.
Gaba ɗaya tsoro ya rufesu jin furucinsa.

Jalal kuwa hatsala iya hatsala ya hatsalo allurar ta motso to amman kuma faɗa da Ba’ana tamkar faɗa da iska mai kaɗawa ne ko kuma duhu.
Da sauri Ba’ana ya juyo kawai sai ya fara dukan sojojin nan baki ɗayansu.
Ya bugi wannan ta nan ya bugu wan can ta can.
Kana ya haɗa da shaƙo wuyan Baroon.
Kurma ihu da kakarin mutuwa Baroon yakeyi da ƙarfi.
Wanda yasa gaba ɗaya gidan ya cika da mutane.
Harda su Arɗo Bani.
Bukar da Bugulu kuwa gefen Bappa suka tsaya suna kekrketa dariyar mugunta.

Junaidu kuwa gefen Junainah dake ta kuma ta tsaya yana bata baki.

Gaba ɗaya hankalin mutane ya tashi.
Su Bappa da Arɗo bani da sauran dattawan Rugar Bani duk sai haƙuri suke bawa Ba’ana sabida ganin yadda yaketa dukansu Jalal ba sauƙi.

Ita kuwa Shatu da gudu ta faɗa jikin Sheykh sabida saketa da Ba’ana yayi.

Ganin ta nufi wurin Sheykh ne ya sashi sakin wuyan Baroon tare da barin dukan su Jalal.
Ya nufo kansu Sheykh da Shatu.
Cikin tsananin ruɗani Shatun ke cewa.
“Yah Sheykh mu gudu zai maka illa”.
Jamil kuwa tuni ya fara aikinshi.
Affan kuwa da Yah Jafar Kara matsowa kusa da Sheykh suke gudun kada a cutar dashi.
Aunty Juwairiyya da Ummi da Sara da inna Amarya kuwa gaba ɗaya jikinsu rawa yakeyi.

Shi kuwa Sheykh murmushi yayi jin Shatu tace.
“Wayyoooooooo Allah Yah Ba’ana ka sakeni”.
Hakane yasa ya fahimci Ba’ana na kusa dashi.
Ido ya lumshe tare da ɗago hannunshi kana a hankali yace.
“Bismillahi”.
Yana faɗin haka yaji hannunshi ya sauƙa kan hannun Ba’ana kuma ya baiyyana kowa na ganinshi.
Cikin nitsuwa Sheykh ya fara karanto Ayatulkursi’u yana mai kallon Ba’ana ido cikin ido wanda a take ya karya duk wani sihirin da Ba’ana ke tutiya da tinkaho dashi da ayar Allah. (Haske ya kori duhu)

Da sauri Shatu ta koma bayan Sheykh ɗin.
Shi kuwa Sheykh juyowa yayi ya kalli su Jalal daketa haki cikin haki da tsananin tafasar zuciya suka nufosu.

Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Ba’ana ganin yadda yaketa fiffizgewa da buga ƙafarshi ta dama da ƙasa amman ina ya kasa ɓacewa.

Cikin sanyi yace.
“Jalal ku kamashi da sunan Allah bazai sake ɓacewa ba har abadan da izinin ubangiji”.

Ai kuwa da sauri Jalal yasa hannunshi ya damƙo wuyan Ba’ana tare da cewa.
“Bismillahi”.
Ai kuwa bai ɓace ɗinba.

Cikin wani irin tafasan zuciya da zafin yadda Ba’ana yayi ta libgarsu kamar shine sojan sune masu laifi cikin takaicin.
Yayi mishi wani irin azabebben shaƙa tare da kima mishi naushi a cikinsa tare da kalmar “Bismillahi”.
Wani irin azabebben ihu mai rakaɗi da baiyyana azabar da yaji yace.
“Wayyoooooooo Allah na rana,”.
Cikin haki Jalal ya kuma haɗa mishi wani naushin tare da cewa.
“Kasan Allah ne kafurin banza matsafi”.
Dai-dai lokacin kuma sauran abokanshi sojojin suka rufe Ba’ana da azabebben duka da ammaton sunan Allah wanda hakan ke ƙara kwance duk wani ɗaurin sihirin dake jikin Ba’ana.

“Ya ilahi ya mujibadda’awati.”
Mamey da Ummi ke faɗi sabida wani irin dukan zaban da su Jalal keyiwa Ba’ana.

Ita kuwa Shatu cikin tsananin tsoro da kerma ta ɗan leƙo.
Dai-dai lokacin Khalid ya murɗe hannun Ba’ana ɓas ya bada sautin karyewa.
Da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin wani irin kuka mai ciwo a rai.
Da sauri Sheykh ya juyo yana kallonta.

Bappa kuwa dasu Arɗo Bani dasu Yah Jafar kab Bukar da Bugulu suke kallo wa ɗan da suke wani irin kuka mai cike da tashin hankali.
Jamil da Affan kuwa sarawa su Jalal sukayi.

Mutanen Rugar Bani kuwa kab suna tsaye wasu tuni hawaye na zubo musu.

Da ƙarfi Ba’ana yayi wani irin azabebben ihu da kururuwa sabida taka hannunshi da Khalid ya karya.
Wanda Umar yayi ɗaya sojan ya murza tare da buga mishi naushin da saida yayi birgiman kule ya iso har gaban Sheykh.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button