GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Yana tashi a wurin yan agaji sukayi mishi rakiya, har bakin motarshi.
Daga nan Masallacin Masarautar Joɗa ya nufa.
Sha biyu dai-dai tayi mishi yana cikin masallacin
tuni an shirya an kimtsa komai yadda abu zai tafi, shiyasa yana isa shida Alaramma Abdulƙadir suka fara.

A can cikin masarautar Joɗa kuwa.
Dai-dai lokacin Shatu ta fito cikin ɗakinta ta nufi falo.
Shiru babu kowa, haka yasa ta wuce kitchen da nufin yin wonke-wonken da sauran gyara-gyare ganin komai tsab-tsab ne yasa ta dawo falonta.
A hankali ta nufi ɗakin Ummi.
daga bakin ƙofa ta tsaya tare da yin sallama.
Cikin kula Ummi ta amsa mata tare da cewa.
“Ki shigo mana”.
To tace kana ta shiga, cikin sanyi tace.
“Ina kwana Ummi”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Lfya lau Alhamdulillah, amman yanzu dai ina wuni ne ko”.
Cikin murmushi tace.
“Eh hakane fa, yanzu har sha biyu da rabi tayi”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ai tunda naji Sheykh ya fara tabsir nace to rana ta tsala”.
Shiru suka ɗan yi tare da kasa kunne, ras muryarshi ke tashi sabida ansa amsa kuwa ta cikin masarautar.
shiru Shatu tayi tare da yin ƙasa da kanta tana mai lumshe ido, Allah yasani tana masifar son tabsir ɗin shi, in taji yana jan baƙi sai take jinta kamar a harami take.
Ummi ce ta ɗan kishin ƙiɗa tare da cewa.
“Gyara zamanki muji wa’azin.”
Kai ta ɗan ɗago tare da cewa.
“Ummi naje kitchen zan mana wonke-wonken na samu an gyara komai ba dai ke kikayi aikinba?”.
Cikin maida hankalinta ga sauraron tabsir ɗin tace.
“Nice nayi, amman daga yau Saratu zata na zuwa tanayi wanke-wanke da share-shere da yan gobe-goben da dai sauran ƴan wasu aiyuka, kamar fere dankali ko doya da tsinkan ganyen ko wanke wake ko jiƙa shinkarfa masa da kai markaɗe, duk itace zatayi mana, mu kuwa in munyi azahar mu shiga kitchen,
zatake ɗan taimaka mana da wasu aiyu kan. Amman banda girki, hadimar Gimbiya Aminatu ce, amman duk azumi nan ake bamu ita”.
Cikin gamsuwa da hakan tace.
“To ba damuwa Ummi, amman dan Allah in ɓata zoba, kada kice zakiyi aikin ki barshi ni zanyi”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Zama tazo, kullum da asuba ana idar da salla zata zo.
In ta gama aiyu kanta kafin ƙarfe goma dai zata tafi, sai anyi sallan azahar kuma zata zo.
Daga nan kuma sai mun gama aikin buɗe baki, ta tafi dana Gimbiya Aminatu da nata, sannan sai ansha ruwa anyi sallan isha’i da asham sai ta dawo tayi yan wonke-wonken da taimaka mana aikin sahur, to in ta tafi kuma sai washe gari in anyi sallan asuba ta dawo.”
Cikin ɗan fito da idonta tace.
“Wannan zirga-zirga haka Ummi to ta zauna anan kawai mana ta huta”.
Juyowa tayi ta ɗan kalleta kana tace.
“Mijinki ba irin waɗannan mutanen bane, baya son a turo mishi yara suzo suyi ta zirga-zirga a kanshi, kinga duk lokutan da take zuwa basa haɗuwa.”
Baki ta ɗan taɓe tare da yin mgna a zuci.
“Kai mutun komai tsari, wannan babu shakka baida gskya ne wannan ɓoye-ɓoyen waya sanima ko cin zan-zanane a jikinshi da saɗaure wata ƙil shiyasa yake kima tabka-tabkan Al’kyabbar ajikinshi dan ya boye abubuwan”.
Murmushi Ummi tayi dan ta lura Shatu bata san mgnar ta fito fili ba.

Shiru Shatu tayi ganin alamun Ummi na jin wa’azin,
Hakane yasa tayi shiru sabida kada ta takura mata.

Ƙarfe ɗaya dai-dai na rana, akayi addu’a aka rufe taron sai kuma Goben in Allah ya kai rai.

Da yawa mutane basu fitaba,
mafi akasari Kur’anai suka ɗauka suna karatu.
Kamar yadda Sheykh yakeyi.

Ƙarfe ɗaya da rabi aka kira sallan azahar.

Miƙewa Shatu tayi tare da cewa.
“Ummi bari inje inyi salla zan zo muyi wata mgna”.
Cikin binta da ido Ummin tace.
“To”.

Bayan anyi sallan azahar an idar ne, ta fito ta nufi ɗakin Ummi, ganin bata nan ne, yasa ta nufi falo, nan kuwa ta sameta zaune bisa kujera.
gefenta taje ta zauna.

Tana zama wata ƴar matashiyar budurwa ta shigo,
cikin nitsuwa tazo ta rusuna gabansu tare da gaidasu, Cikin kula Ummi tace.
“Yauwa Saratu kin zo ko?”.
Cikin nitsuwa tace.
“Eh Ummi nazo ɗazu bakwa nan sai na koma sai yanzu na kuma zuwa”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Yayi kyau,”. Inda Shatu take ta ɗan kalla tare da cewa.
“Ɗiyata ga Saratu. Saratu ga Saiyada Shatu matar Sheykh Jabeer”.
Cikin mamaki da dariya sunan da Ummi ta liƙa mata wai Sayyada, ta kalli Saratu tare dake gaisheta cikin ladabi da biyayya,
fuska a sake ta amsa.

Cikin sanyi Saratu tace.
“Ummi me za’ayi ne?”.
Gyara zama Ummi tayi tare da cewa.
“Ki wonke shinkafar masa dama na jiƙata, kana ki gyara mana ganyen alaiyahu, sannan ki fere Arish.
Sai kuma ki jajjaga kayan miya, ki yanka al’basa mai ɗan yawa.”
Cikin nitsuwa da bin umarni tace.
“To Ummi”.
Ta ƙarishe mgnar tare da miƙewa ta nufi kitchen, tana shiga ta fara aiyukan da aka sata.

A falon kuwa, gyara zama Shatu tayi tare da kallon Ummi cikin sanyi tace.
“Ummi dama mgnar da zamuyi ko!.”
Sai kuma tayi shiru tana nazari, jin muryar Ummi nace mata,
“Uhum ina jinki faɗi”.
Sunkuyar da kanta tayi a hankali tace.
“Uhumm dama cewa, zanyi in ba matsala a rinƙa yin abun buɗa bakin ana kaiwa masallacin Masarautar Joɗa mana, tunda dole talakawan gari na zuwa nan sallan magriba.”
Murmushi mai yelwa Ummi tayi tare da cewa.
“Allah sarki, Shatu mai tausayi, ba matsala amman ki tambayi mijinki in ya amince dai ba matsala, dama kuma ana fitar da abinci a sashin Gimbiya Aminatu, da Gimbiya Saudatu da kuma gidan Galadima, da Hajia Mama.
Da gidan Dr Aliyu da sauran duka, kuma ko Juwairiyya ma tanayi”.
Murmushi ta ɗanyu tare da cewa.
“To Ummi muma ai muna son ladan wannan aikin”.
Da sauri tace.
“A sosai ma kuwa. Sai dai ki sanar da maigidankin in ya yarda yanzu incewa Saratu ta ƙara hannun sosai”.
cikin kwaɓe fuska tace.
“To Ummi shi wannan sarkin zirga-zirgan ina zan ganshi?”.
Cikin yin ƙasa da murya Ummi tace.
“Yana falonshi yanzu ya dawo, yana wucewa kina fitowa, jeki sameshi da sauri kada yayi bacci ya zama kin tadashi a bacci dan babu abinda yafi ɓata mishi rai sama da ya fara bacci a tadashi”.
Cikin juya ido tace.
“Ummi to ni me zan ce mishi?”.
Murmushi Ummin ta kumayi kana tace.
“Abinda kika cemin shi zaki ce mishi, tashi kije musan yadda zamu fuskanci aikin”.
Ta ƙarishe mgnar tana miƙar da hannunta, a hankali ta miƙe tsaye, doguwar rigar jikinta ta gyara tare da yane mayafinshi.
Ganin ta tsaya ne yasa Ummi cewa”
“kije mana.” Allah yasani badon tana son ladan aikin ciyar da marasa ƙarfi da basu abin buɗa bakiba da bazata sake zuwa tambayar abu wurin wannan kurman ganganɗinba, tun randa taje tana mishi mgnar yacewa Umaymah ta bar musu Hibba ya shareta take jin haushinsa in ta ganshi kamar ta ɗirka mishi dundu a baya.
Muryar Ummi data kuma jine yasata, juyawa, ta nufi corridor’n da zai sadata da falonshi.

A hankali take taku, tana jin sanyin tayis ɗin wurin na ratsa mata ƙafa,
sallama tayi a bakin kofar tare da kutsa kai ciki, tana mai murtuƙe fuska.
Bisa 1 str ta sameshi zaune, da alamun waya yakeyi da Umaymah.
Dan taji yana kiran sunanta.
Gefenshi ta ɗan tsaya tare da kallonshi ta wutsiyar ido.
Shi wai ko shi kaɗai ko a ɗakinshi shi ɗaya sai ya zauna da kima-kiman riguna, ganshi wata ƙil basa damunshi”.
Haka taketa maganar zuci, har ya gama wayar da yakeyi bata, saniba.
shi kuwa baibi ta kantaba yaci gaba da ɗan aikin da yakeyi a wayar.
Jin shirune yasa ta ɗan kalleshi, ganin ya gama wayar da yakeyi ne yasa, cikin dakiyar murya tace.
“Uhummm dama so nake in ba matsala ko zamu rinƙa yin abin buɗa baki ana kaiwa masallacin, da kuma bawa bayi nasu daban”.
Bai kulata ba, asalima yamutsa fuskarshi yayi, ya lura wannan abar bata gama iya sanin makamar mgna ba, ji yadda take mgn a kaikace.
Kamar ba ba fullatanaba, bayan anyi ittifaƙin bayan larabawa babu ƙabilar dake da luggar iya sarrafa harshe sama da Fulani.
Shiru tayi tare da tura baki kana ta ɗan murguɗashi, tare da cewa.
“Ayyah ka amince mana?”.
kanshi ya sunkuyar tare da ɗaga system ɗinshi ganin biyu dai-dai ta cika.
Miƙewa tsaye yayi tare da motsa lips ɗinshi a hankali yace.
“Eh”. Da sauri ta juya ta fita tana hararan bayanshi.
Shi kuwa bedroom ɗinshi ya wuce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button