GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin ikon Allah shida dai-dai suka gam kan aikinsu.
Bayan Shatu’n ta taya Hibba suya kwai daban, ta jerasu a Foodflaks, in ta ajiye fefeyin soyayyan ƙwai da yaji haɗi da diddigin kifi, sai ta zuba soyayyan Arish a kai kana ta kuma rufeshi da fefeyin kwai haka ta rinƙa jerasu saida ta cika kulan.

Ummi kuwa ta sawa Saratu komai nata.

Sannan suka kimtsa wurin fes suka fito da komai suka jera a dinning table.

Nan duk suka wuce ɗauki.
Wanka sukayi, kana sukayi al’wala sannan suka fito falo. A nan suka samu Imran, Jalal, Jamil, Sulaiman.
Cikin gajiya Ummi tace.
“Yauwa Jalal ku ɗauki manyan kulolin nan ku kai masallaci.
Sauran madaidaitan kuma ku ajiyewa sarkin bayi.
A bawa bayi da hadimai”.
Murmushi Jamil yayi tare da cewa.
“Eh lallai bana bayi sun samu uwar gijiyar data tuna dasu, bayan kuma anayi musu nasu na daban”.
Cikin lumshe ido Shatu tace.
“Eh suma suci abinda muke dafawa da kanmu, ba sai na gandun nasuba”.

Miƙewa sukayi suka ɗauki kulolin sun zo falon kenan Sheykh na shigowa, wani hadimi na biye dashi da manyan ledodi cike da ƴaƴan itatuwa.
Kusan a tare suke mishi sannu da dawowa.
Murya a bushe alamun ƙishi yake amsa musu kana ya nunawa Ummi leda ɗaya yace.
“Ummi a wonke wannan a haɗa da dabino mudu uku a basu su kai masallaci”.
Ya ƙarishe mgnar yana wucewa.
Da sauri Ummi tace to.
Ta miƙe kenan Shatu tace.
“Ummi zauna bari in wanke sun”.
To tace kana ta koma ta zauna.
Ita kuma taje ta wonke ta zubasu a tray kana ta ɗauko plates and cups masu yawa, tazo ta miƙawa Imran.
Da sauri suka amsa suka tafi.

Jim kaɗan suka dawo, cikin gajiya Jamil yace.
“Ummi ansha ruwafa mun samu Ladan na cin dabino”.
Da sauri Hibba ta miƙa tare da cewa.
“Su ladanannan haka suke basa kiran salla sai sun sha ruwa.”
Dariya sukayi mata kana suma suka miƙe sukabi bayanta.

Zama sukayi bisa kujerun kowa da abin yake hari.
Sai dai kab ɗibsu da dabino suka fara.
Ummi ce ta kalli Shatu tare da nuna mata babban tray’n da aka shirya komai na buɗa cikin Foodflaks guda 3 madaidata masu kyau, sai plate ɗin da aka shirya fruits masu ɗan karen sanyi, tupa, inabi ,kankana, abarba, gwanda, Lemu, ayaba, kana da dabino, da kwakwa,
Sai goran zam-zam madaidaci, kana sai cup da tea spoon a ciki, sai fork and knife a gefe da gefen plate ɗin dake cike da fruits ɗin komai biyu akasa.
Kulolin kuma ɗaya masane a ciki, ɗan namiyar kuma miyar Masar ne, sai ɗayan kuma, soyayyan ƙwai da dankalin, ɗayan kuma ferfesun kayan cikin ne.
Cikin nitsuwa Ummi ta ɗago tray ta miƙa mata tare da cewa.
“Yauwa gashi kai mishi lokacin shan ruwan na tafiya, yanzu zakiga ya fito”.
Cikin sanyi da gajiya ta amshi tray’n kana ta nufi falon nashi, cikin nitsuwa take takun, a hankali tayi sallama tare da kutsa kai cikin falon.
A can bisa Dinning area ta hangoshi yana zaune, kan kujera ɗaya, ya kuma jawo ɗaya kujerar ya ɗaura sawunshi a kai ya miƙesu, System ɗinshi na bisa cinyarshi.
A hankali take takowa saman steps ɗin tare da ratsa cikin jeren ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond sai sunkuyar da kanta tayi sabida ɗauke mata ido da suke.

A hankali ta isa kusa dashi, cikin tura baki tare da ɗan murguɗashi ta ajiye tray’n, a tsakiyar table ɗin.
ɗago kanta tayi da niyar ta ɗan juya, ta fita.
Wani irin buɗe idanin tayi gaba ɗaya tare da zubasu, bisa sharaban ƙafarsa ta dama, wanda sanaɗin zaman da ya ɗan yi ya miƙe ƙafafuwan nashi bisa ɗaya kujerar ne yasa suka ɗan baiyana, wani irin kallo mai cike da ɗimuwa takeyiwa zanen dake bisa ƙafarshi ta dama, da sauri ta rumtse idanunta tare dasa hannun hagun ta kama kanta sabida wani irin sarawa da ya farayi da ƙarfi.
Cikin sauri ta juyo tare da miƙa hannun damanta ta sauƙeshi kan…!

         Akwai kayan gyara na amare da uwar gidaye da masu jego, ga mai buƙatar saya ga number ta 09097853276



                        By
       *GARKUWAR FULANI*

Ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond da yayiwa wurin labule.
Yayin da kuma hankalinta da idonta duk suke kan ƙafar tashi tana kallon zanen da take gani har kamar motsawa yakeyi a jikinshin, da kuma suffar macijiya.
A hankali ta ɗago ƙafarta tare da take step ɗin forko, hankalinta kuwa duk yana baya, har ta juya kanta gaba ɗaya sam ganinta baya gaba.
Cikin rashin sa’a kafar ta tsallake step ɗin forko bata isa kan dandamalin ta biyu ba, ta sauketa, cikin akasi ƙafar ta sule tare da yin shuuuuu tayi gaba.
Wani ƙara mai ɗan karfi irin na maiyin azumi ta sake tare da rumtse idanunta da ƙarfi tana jiran taji ta ina ɗin ta zai karye.
Wani irin ihu ta kuma sakewa, lokacin da taji ta faɗi gib a kan stpes ɗin kanta ya bugi dandamalin sama.

A hankali ya juyo kanshi ya kalleta a fakaice,
Ba tare da yace mata ko ƙalaba ya juyar da kanshi ya fuskanci tray’n data ajiye mishi, plate ɗin fruits ya ɗan buɗe kana, ya ɗauki Fork ɗaya, janye ƙafafuwan shi, yayi ya sauƙo dasu ƙasa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci Dinning table ɗin da kyau.
Fork ɗin yasa ya fasa cikin dabino da yake irin na kwali nanne mai laushi ne,
ture ɗan yayi gefe kana ya soki dabinon a hankali ya kai bakinshi, bayan yayi addu’o’in buɗa baki.
Ido ya lumshe jin lokacin da sanyi da zaƙi da ɗanɗanon dabinon ya game mishi baki.

Ita kuwa Shatu kuka tasa tare da riƙe ƙugunta, da kanta cikin muryar kuka take cewa.
“Wayyo Allah na. Wayyo Ummey na, bayana ya karye ƙuguna ya ɓalgace, kaina ya fashe ƙeyana ya tarwatse”.
Ta ƙasa Glass ɗin table ɗin ya ɗan kalleta, kana ya maida kanshi yaci gaba da cin dabino, yana maijin wani irin masifeffen dariya na taso mishi jin raki da Shatu ke zubawa.
Saida yaci ƙwaya bakwai, kana a hankali ya fara tsira Fork ɗin kan ƴaƴan inabi masu masifar sanyi da daɗi, ci yakeyi yana jin ƙishin daya addabi moƙoshinsa na wucewa.
saida ya tsinke nonon inabin kab ya cinye, kana ya fara soka kankana da akayiwa ƙaƙanan yanka kana aka barbaɗa garin madara a samansu, shima shanye rabinshi yayi.
Wani sassanyan gyatsa yayi tare da ture tray’n gefe.

Ita kuwa Shatu sosai taji zafin faɗuwan ga azumi ga gajiyan aiki ga faɗuwa ga haushin yadda duk ihun da tayi babu wanda ya kulata, bare a kawo mata agaji, abun ya haɗe mata sai hawaye share-shere ta tabbatar da a gidansu ne tayi wannan ihun da gaba ɗaya iyayenta da yayunta da ƙanwarta duk suna kanta, da tuni an ɗagata a wurin ma.
Bege da kewa da kukan rashin yan uwanta da watseman ahlinsu ne ya tunzura hawayenta.
Ta kasa tashi sabida jikinta duk rawan yunwa da gajiya yakeyi ba ƙarfi sam.

A hankali ya miƙe tsaye bayan ya sha ruwan zam-zam mai ɗan sanyi kan ƴaƴan itatuwan da yaci.
System ɗinshi ya ajiye kan Dinning table ɗin, tare da wayarshi.
Gefenta ya ɗan ratsa ya fara taka steps ɗin tare da kallonta a fakaice.
Yana gab da sauƙane ya ɗan motsa lips ɗinshi tare da cewa.
“Kaɗan kenan in dai baki dena samin ido a jikina ba,
Faɗuwa harda kareireyewa zakiyi in baki kiyayi yimin kallon ƙurillaba, na lura ku mutanen wancan dajin bakuda abinda kukafi so sama da kallon killataccen wuri na jikin mutun.
Muddin baki dena satan kallon jikina ba, sai waɗannan mayatattun idanun naki sun tsiyaye kin huta ki zama makauniya babu ɗan jagora.
Kiyi dai a hankali ko kya samu ki mutu da idonki,”.
Ya ƙarishe mgnar yana tafi kamar bashi yayi mgnar ba.
Ita kuwa Shatu hannun tasa ta sharce hawayenta tare da rakashi da hararan kai mugune.

A falon ya samu su Ummi sunata dariya.
Cikin sauri ya kalli su Jamil yace.
“Kai wannan dariyar na menene, ku taso mu tafi masallaci”.
Cikin dariya Jamil yace.
“Allah ko Hamma Jabeer ina zaton Hibba bata taɓa azumi ba sai bana.
Ga yadda ta dawo wuni ɗaya, wai a haka kuma har ta fara lissafin wai yauwa yau mun kai ɗaya mun rage”.
Ɗan gajeren murmushi yayi tare da cewa.
“Muhibbata tashi kije kiyi salla sai ki ɗan konta ki huta kafin a kira isha’i ko”.
Cikin sanyi tace.
“To Hamma MJ”.
Jalal kuwa cikin yin ƙasa da murya yace.
“Gobe ma zakiyi ne ko zaki huta”.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Zanyi Umaymah tace, bana ko ɗaya in nasha sai na biya”.
Murmushi ya ɗan yi tare da cewa.
“Ashe dai kin girma”.
Da sauri ta sunkuyar da kanta, shi kuwa yabi bayansu Jamil.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button