Daga nan ta miƙa ta nufi ɗaki dan yin salla.
Ana idar da salla suka fito, kitchen suka nufa ita da Ummi da Saratu da tun ɗazu tana nan.
Suka fara aikin buɗa baki sunayi suna kimtsa komai.
Kafin shida ta cikama sun gama komai.
Yanzu in sun zo buɗa baki ita da Ummi da Hibba tsakiyar falon suke dawowa.
Jalal, Jamil, Imran, Sulaiman, kuma su zauna a dinning table.
Ya Jafar kuwa wani lokacin har can falon Sheykh zai wuce suyi buɗa baki a tare.
Kana su tafi masallacin.
Haka dai komai yaketa wakana cikin aminci da tsari.
A wurin al’ummar Annabi kowa ya nitsu ya maida hankali kan ibada domin neman rabauta.
Ƙarfe takwas dai-dai suka shiga kitchen dan yin aikin sahur.
Cikin kula Ummi ta kalleta tare da cewa.
“Ɗauko kwanu kan nashi”.
Kanta ta ɗan juyo ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ai bai dawo yaci ba ko?”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
“Baya cin ƙosai, kuma kinga doyan ma jiya baiciba, ya gaji dasu ne, ki ɗauko a juyewa su Saratu shi ki ɗan haɗa mishi wani abu kafin ya dawo”.
Cikin ɗan kauda kai tace.
“Ummi ai ƙoshi yake shiyasa bazai ciba, a barshi kawai in yaji yunwar yacima wani bai saniba, ai yunwa ba Umaymah bace ko ke bare zaku lallaɓashi”.
Dariya Ummi tayi kana kuma ta haɗe fuska tare da cewa.
“Je kiyi abinda nace ko”.
To tace ganin kamar ran Ummi ya ɓaci.
Bayan ta dawo da kwanukan ne,
Suka bawa Saratu ta juye, kana ta harhaɗa wonke-wonken ta fara.
Ita kuwa Shatu cikin yin miƙa tace.
“Ummi me zan dafa mishin?”.
Juyawa tayi tana haura wurin da Fridge yake tare da ce mata.
“Duk abinda kika iya kika san ba mai nauyi bane”.
Kanta ta gyaɗa tare da cewa.
“To”.
Cikin ranta tace.
“Bari inyi Special Arish, in yaga dama yaci in yaso ya bari, mutun sai zaɓe-zaɓe kamar mai ciki.
Dankali ta ɗan ɗebo da Nama, kwai, tumatur, kabeji, Bama, maggi, tafarnuwa man gyaɗa, komai dai dai-dai misalin yadda zata buƙata duk ta ajiyesu kusa da ita.
Fere dankalin tayi ba tare da ta daddatsashi ba. Ta wonƙeshi fes kana tasa a ƴar tukunya tare da tarfa gishiri da ruwa dai-dai misali, sannan ta tafasashi.
Kwan ta ɗauka ta fasa ta kaɗashi da kyau tare dasa yankekken al’basa da Curry da maggi da tafarnuwa ɗan kaɗan.
Ganin dankalin yayine ta juyeshi a ɗan kondo ta tsaneshi.
Tare da ɗan barinshi yasha iska, kaɗan.
Kana ta ɗaura Naman da maggi da gishiri da Curry da tafarnuwa da al’basa. bisa wata a ɗan tukunta.
Sannan ɗaura man ta ɗauki dankalin ta tsomawa cikin kwan tana soyashi, saida ta gama ta ajiyeshi gefe.
kafin nan naman kuma yayi lugub yayi laushin.
saida ruwan ya kusa ƙarewa sai ta ƙara wata al’basar da tumatur suka nuna tare sannan ta kwashesu.
Kabejin ta yayyanka ƙanana sannan ta ɗauki dafaffan kwai ta yayyanka shi da ɗan girma.
Kana tasa Maggi da al’basa da Bama ta gauraya kana
Ummi ta miƙo mata ɗan ƙaramin Foodflaks alamun ta amsa ta saka.
Kanta ta jujjuya tare da cewa.
“Bari in sa mishi a plate kawai tunda ya dawo”.
Da mamaki Ummi ta kalleta tare da cewa
“Yaushe ya dawo?”
Plate ta ɗauko tare da cewa.
“Tun ɗazu”.
Da sauri ta sunkuyar da kanta ganin kamar Ummi na mata kallon Mamaki da tuhuma.
Ita kuwa Ummi cikin Binta da ido tace,
Ya akayi kika san ya dawo”.
Kai ta rausayar tare daci gaba da aikin kamar bataji Ummi ba.
Plate ɗin ta ajiyeta, ta zuba Arish ɗin gefe kana tasa haɗin naman gefe, ta kuma zuba na Kabejin shima gefe.
Ta shiryashi yayi kyau sosai.
Ɗaya plate ɗin ta kife kanshi.
Kana tasa spoon da Fork a cikin tray’n data ajiye plate ɗin.
Ɗan madaidaicin flaks ɗin coffee ta ajiye gefe, kana tasa cup da tea spoon a ciki.
Sannan turashi gefe.
Zuwa lokacin kuma tuni Ummi da Saratu su gama aikin sahur ɗin har Saratu ta tafi.
Sauran ta sako a wani plate ɗin tare da cewa Ummu gashi.
Amsa Ummi tayi tare da cewa.
“Ɗauki ki kai mishi to”.
To tace tare da ɗaukan tray’n ta fita.
A tsaye ta sameshi cikin wani tattausan jallabiya da alamun wonka ya fito,
Sai wani irin masifeffen ƙamshi yakeyi.
Cikin nitsuwa ta wuce ta bayanshi, inda yake tsaye yana kunna Tv.
Bisa santa table ɗin glass mai garai-garai dake tsakiyar falon ta ajiye mishi.
Kana ta juya a hankali ta fita.
Kai tsaye ɗakinta ta wuce, nan ta samu Hibba tuni tayi bacci.
Wonka tayi da ruwan ɗumi tare da shafa mai kana tasa wata tattausar rigar bacci gajera iya karta guiwa.
Hibaji ta zura a jikinta kana ta haura gado ta konta tare da jawo blanket ta duƙunƙune a ciki.
Sabida ita bata son sanyi, shiyasa takesa ƙaton hijabi kana ta shiga borgo.
Badon Hibba Bama dake masifar son sanyi da kashe AC’n zatayi.
Ƙarfe ɗaya dai-dai ta tashi bacci al’wala tayi kana tai ta nafila hakama Ummi.
Sheykh Jabeer kuwa tuni ya tashi shima.
Ya kira su Jalal ma a waya ya tashesu.
Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta isa falonshi da tray’n abincin sahur ɗin shi.
Ta ajiye ta juyo kenan shi kuma yana fitowa falonshi.
Tazo tsakiyar falon kenan tana tafiyarta a hankali ba zato ba tsammani taji daram-dam ƙaran bindigar da kullum da asuba sai an saketa sau biyu, ta kuma kasa sabawa dashi bare ta daina tsoronshi.
Wani irin tsalle da zabura tayi tare da ficewa a guje tana cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Bayanta yabi da kallo tare da taɓe baki kana ya nufi Dinnin area.
Washe gari da safe yau Jumma’a kuma, yaune azumi na shida.
Bayan sun fitone, Ummi ta kalleta cikin dariya dan tuno yadda ta fito falon Sheykh Jabeer a guje da asuba, tana jan Allah ya isanmata ana tsinka mata zuciya,
Cikin murmushin tace.
“Ummi dariyar me kikeyi ne?”.
Cikin gimtse dariyar tace.
“A babu, yauwa tashi muje ɗazu Gimbiya Aminatu ta aiko, wai tayi kewarki kwana biyu azumi ya ɓoyeki bakije ba”.
Cikin murmushin tace to muje Ummi”.
Ta ƙarishe mgnar tanayin gaba Hibba na biye da ita a baya.
Cikin sauri Ummi tace.
“A haka zaki fita ba al’kyabba”.
Kai ta ɗan dafe tare da cewa.
“Wayyo Allah na, Allah kuwa ni nauyi sukemin wannan tsarabe-tsaraben wuya gareshi”.
Murmushi Ummi tai tare da miƙewa ta ɗauko al’kyabbar.
Tazo tasa kana suka fita.
Da Side ɗin Hajia Mama suka fara,
A falo suka samesu.
Cikin fuskar ba yabo ba fallasa Hajia Mama ta amsa gaisuwar Shatu.
Batool kuwa sai auna mata harara takeyi.
Hira suka ɗan taɓa kana suka fito.
Har sun fito Shatu ta ɗan kalli Ummi cikin sanyi tace.
“Ummi jirani anan bari inje in isar da saƙon gaisuwar Ummey na wurin Hajia Mama”.
Da Mamaki Ummi tace to kana ta juya ta nufi ciki, ganin Hibba za biyota ne tace.
“A a jirani ina zuwa”.
Haka suka tsaya suna jiranta.
A hankali ta turo ƙafar falon.
Da sauri Hajia Mama ta zuba mata ido fuska cike da tsana.
Batool kuwa binta da ido takeyi ganin wani irin takun isa da ƙasaitar da takeyi.
Kujerar dake fuskantar wacce Hajia Mama ke zaune a kai ta zauna.
Ƙafarta ɗaya ta ɗaura kan ɗaya.
Kana ta jingina da kujerar, cikin tsare Hajia Mama da ido tace.
“Uhummmm kin sanni sarai, kar tasan karne, duk motsinki a tsakiyar tafin hannuna kike, dan haka gwara kiyiwa kanki gada ki fita harka da rayuwar mijina! Da ƙannenshi da wanshi. In kuwa kikaƙi zakisha mamakin Shatu.”
Tana faɗin haka ta miƙe, tana kallon Batool da tun randa akace Shatu tazo ta bawa Hajia Mama haƙuri da ta shigo tayi wasu kalaman ya ɗaurewa Batool kai ta kasa tantance tsakanin aya da tsakuwa, shiyasa batayi gigin yin mgn ba, sabida tuno abinda Shatu tace mata a ranar cewa.
“Mijina kike so ko, to kizo in ya amince ya kalli inda kike na daƙiƙi biyu rak zan sashi ya aureki”.
Da sauri Batool ta dawo daga duniyar tunanin da take jin ƙaran rufe ƙofar da Shatu tayi.