GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Can Cikin bacci take jin alamun kamar mutun na tsaye a kanta, cikin magagin baccin ta buɗe idonta.
Gabann Tv ta ganshi ya kashe TV kana ya juyo ya kalleta a fizge yace.
“Ba salla sai kallo da bacci”.
Jin haka yasa ta miƙe zaune tana gyara mayafin kanta.
Shi kuwa tuni ya wuce Side ɗinsa.

Tana idar da salla ta fito. Nan ta samu Saratu tazo, kitchen Suka shiga suka fara aikin yamman.

Sai gab da la’asar su. Ummi suka dawo da kaya niƙi-niƙi. Nan suka ajiye sukayi salla kana suka shiga kitchen ɗin.

Hibba kuwa yashuwa tayi a ƙasa tana birgima kamar bazata kai magriba.

Sai bayan sallan isha’i sun gama aikin sahur ɗin ne.
Suka dawo falo, nan Ummi ta nuna mata ɗinkunanta da aka bada tun Umaymah bata tafiba.
Sosai taji daɗin kayan da ɗinkunan, lallai tana son dogayen riguna Amman tana son surkawa da Shadda, atampa, leshi, musamman Waɗan nan ɗinkunan sunyi masifar kyau. Ko wanne dai-dai jikinta kamar an gwada ta.
Daga nan kuma suka nuna mata gellulluka da hibai da takalma da saraƙunan da suka zaɓo mata bayan sun zaɓawa kansu.
Sun nuna mata nasun ma.
Ummi ta ƙara da cewa.
“Duk zannuwan da abun ɗinkawan kuma an bawa Kabir telen suma duk cikin KMC suke.
Nanda salla dai komai zaizo dai-dai.
Cikin jin daɗi tace.
“Ngd matuƙa Ummi Allah ya saka da al’khairi”.
Amin Amin tace. Kana tace.
“Sheykh zakiyiwa godiya”.
Shiru tayi kamar bataji ba.
Hibba kuwa cikin jin daɗi tace.
Aunty Shatu na zaɓa mana wani Shadda lace mai masifar kyau iri ɗaya na ɗauka mana Royal blue and white Golding color. Nace a tsantsara mana dogayen riguna”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kai kinko kyauta mana”.
Daga nan suka tattara tarkacen suka nufi makoncin baccin su.

Zaune take gefen Ummi tana riƙe da waya cikin murmushi tace.
“Allah ko Umaymah munyi kewarki”.
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
“To ko zaku zomin Barka da sallane”.
Da sauri tace.
“Eh Umaymah Allah in ya yarda zamuzo ki tambayan mana shi”.
Cikin dariya Umaymah tace.
“Yoh mace da mijinta sai wani ne zai tambayar miki”.
Cikin sanyi tace.
“Uhummm”.
Ita kuwa Umaymah cewa tayi.
“Ina Umminku?”.
Da sauri tace.
“Gata ta ƙarishe mgnar da miƙawa Ummi wayar.
Cikin fara’a suka gaisa kana Umaymah ta tambayeta ya yaran nata, tace duk suna lfy.
Nan take ce musu ta cewa Shatu ai a saudia zasuyi salla.
Sosai Shatu ta tayasu Murna.

Suna cikin hirar Hadimai guda uku suka shigo da jakukkunan guda uku.
Rusunawa sukayi bayan sun gaidasu ne,
suka ajiye jakukkunan tare da cewa.
“Gashi biyun inji Lamiɗo ɗaya kuma Gimbiya Aminatu ce tace mu kawo miki”.
Sukarishe mgnar suna kallon Shatu.
Godiya tayi musu kana ta kalli Hibba data miƙo mata kuɗi sun kai dubu biyar.
Ta gane manufar Hibba shiyasa ta amsa ta basu.
Godiya sukayi kana suka tafi.

Jim kaɗan Hadiman Hajia Mama sukazo da saƙon Hajia Maman.
Sosai Shatu tayi godiya ta mashi kuɗi a hannun Hibba ta basu.

Nan Hibba ta tattara kayan ta shigar dasu, zata shigar dana HAJIA MAMA tace
“A Hibba barsu zan shiga dasu.”
Gefe ta nuna mata tace ajiyesu anan.

Bayan sunyi sallan azahar sun fito zasu Fara aiki ne ta kalli Ummi tace.
“Ummi bari inje inyi godiya wurin Hajia Mama”.
Cikin tsareta da ido tace.
“Ki bari mana sai ansha ruwa sai in rakaki daga nan kiyiwa Lamiɗo ma godiya.
Duk dai wannan kyauta da yakeyiwa duk ahlin masarautar Joɗa in lokacin salla ya gabato amman muje kiyi godiyar.”
Da sauri tace.
“No Ummi ba sai an rakani ba, zanje ni ɗaya ma, kinga nasa al’kyabba”.
Daga nan ta fice, cike da mamaki suka bita da ido.

Bayan kamar 37 minute ta dawo cike da fara’a sukaci gaba da aikinsu.

Can da suka fito dan yin sallan la’asar,
Ba kayan ba dalilinshi. Da sauri Hibba tace.
“Aunty Shatu kin shigar da kayan ne?”.
Ci gaba da tafiya tayi tare da cewa.
“Maisu ta aiko an kwashe mata abunta dai”.
cikin mamaki sukabi bayanta.

Yau azumi goma sha huɗu gobe 15 in Allah ya kaimu.

Bayan yaci abinci ne ya kira Umaymah nan yake ce mata.
“In Allah ya kaimu gobe iwar haka ƙarfe goma na dare zuwa sha ɗaya jirginmu zai tashi Umaymah”.

“Kai da waye zaku tafi ne?”.

“Nida Dr Aliyu, da Barrister Kamal, sai kuma Ya Hashim da Galadima, da Wambai da Abba na da cimgan ɗin shi”.

Da sauri tace.
“To wai kana nufin kai bazaka je da taka cingam ɗin bane?”.

Cikin sanyi yace.
“Kiyi haƙuri Umaymah dan Allah na roƙeki kada kice inje da kowa, dan Allah a barni mana in huta in na bar ƙasar kam”.

Shiru Umaymah tayi saida taji ya kai ayane tace.
“Shi kenan Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, kuma muna nan tafe”.

Amin Amin yace kana sukayi sallama.

Washe gari kab mutanen masarautar Joɗa masu zuwa Umrah sun gama shirin su.

Bayan ansha ruwa anyi sallan isha’i ne suka shiga kitchen dan aikin sahur, koda ta ɗauko Foodflaks ɗin da akasa mishi abin buɗa baki ko buɗe su baiba.
Hakane yasa Ummi tace to maza ta dafa mishi wani abun.

To tace kana ta juya ta ɗauko, kaza, kwai, dankalin turawa kaɗan, maggi, gishiri, tattasai, attaruhu al’basa mai Curry,
Duk ta matso dasu kusa.
Sai kuma ta ɗebo Kabeji karas.
Ta miƙawa Saratu tace.
“Yauwa Sara goga min su ƙananan, kada ki haɗasu wuri ɗaya, kana ki yayyaka min al’basa sannan ki jajjaga min wata.”
Ta faɗin tana tura mata Attaruhu da al’basan.
Cikin nitsuwa Saratu tace.
“To Aunty ba matsala”.
Ita kuwa Ummi meda hankali tayi kan girkin sahur ɗin.

Wanke rabin kazar tayi, tare da sata a tukunya ta watsa al’basa da maggi da tafarnuwa da citta da kanamfari kaɗan.
Sannan ta rufeshi. Tasa wuta yadda ya kamata.
Kana ta jawo robar dankalin ta fara ferewa tare da cewa.
“Allah aikin nan yana yawa Ummi, kusan wuni muke a kitchen mu kuma kusan kwana shima wai bazaici abuba sai sa mutane aiki”.
Tayi mgnar cikin gajiya da kuma iya gskyar ta, dan muddin kasha ruwa tafa burinka ka samu ka huta.
Juyowa Ummi tayi ta ɗan kalleta tare da cewa.
“A’a ai bakya son hutun tunda kikaje kika samu Juwairiyya kikace ta huta taji da aikin gidanta, nan zaki rinƙa yi, sannan in Hajia Maman ta aiko ki kora Hadiman dashi, ko kisa Hibba ta kaiwa bayi shi.
Kinga duk sun gaji sun daina kawowa, sai Na Gimbiya Aminatu, shi kuma Sheykh yace a dena kawowa tunda kice zaki iya da aikin.
Yanzu da kin bari suna kawowa dai da wata ranama sai munga dama mushiga madafa”.
Sunkuyar da kanta tayi tare da yin shiru kamar bata nan.
Yes ta san duk abinda Ummi ta faɗa hakane.
Ƙarisa feree dankalin tayi kana ta wonƙeshi fes ta ɗaurashi a wuta, ya dafu sosai kana ta sauƙeshi a gefe.
Zuwa lokacin kazar ma tayi lugub, haka yasa ta sauƙeshi ta juyeshi a plate, zare ƙasusuwan tayi duka, sannan ta ajiyeta gefe kusa da dankalin.
Jajjageggen Attaruhu da al’basan da Saratu ke miƙa mata ta amsa.
Cikin plate ɗin dafeffen dankalin ta juyeshi kana tasa kazarma a ciki.
Sannan ta jujjuyasu ta caƙuɗasu da kyau, kana tasa Maggi gishiri ɗan ƙanƙani, sai kuma Curry.
Kwan dake gefe cikin ɗan wani kwanon tangaran ta jawo, ta fasa kwan ta juye cikin haɗin kaza da dankali da jajjagen ta ɗan gwarayasu.
Hibba data shigo yanzu ne tace.
“Yauwa My Aunty dama kwaɗayi ne ya koroni nazo in shiga kitchen.”
Murmushi tayi tare da cewa.
“To matso ki tayani aikin ɗan zuba min ruwan zafi kan Karas ɗincan.
In yayi ɗumi ki juye ruwan cikin kwandon kabejin nan ruwan zafin ya ɗan razana ganyen, sai ki miƙo min shi nan”.
To tace tare da fara aikin.
Ita kuwa Shatu ɗiban haɗin ta rinƙayi tana mul-mulawa kamar Yan boll,
saida ta gama sannan, ta ɗaura man gyaɗa.
yayi zafi ta fara suyasu,
saida ta soyasu duka tasa a Foodflaks kudun kada yayi sanyi ta matsar dashi gefe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button