GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin wani irin kallo Hibba ta miƙa da ƙarfi tare da…!

Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 ko kiyi min TRANSFER din 1k Dan samun Special Group ta asusuna na 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.

                      By
            *GARKUWAR FULANI*

Tare da cewa.
“Lahh Ummi kalli Hamma Jabeer kusa da Uncle Jabir Ali ɗin can”.
Cikin Murmushin Ummi tace.
“La ai kuwa, Allah sarki masha Allah, tabarakallah. Allah ka ƙarawa Annabi daraja, Allah ka ƙara bamu hasken addini da imani a zuƙatanmu.”
Amin Amin Hibba tace.
Tare da juyowa ta kalli Shatu da tayi kamar bata jisu ba,
Sai tea ɗinta take zuƙa a hankali.
A zahiri zakace idonta kan cup ɗin yake, amman a baɗini kan allon TV’n idonta yake, ta zubawa fuskarshi ido. Duk da bawai kai tsaye shi kaɗai ake ɗaukaba, limamin dake jansu ake ɗauka hakan yasa suma suka fito da yake yana cikin mamun limaman sahun forko.

Sosai take ƙare mishin kallo tare da tsarin shigarsa dana mutanen da yake cikinsu.
Sam bazaka iya bambance shi da suba, Especially ma Sheish Jabir Ali da yake matuƙar kama dashi.
Haka nan taji wasu irin zafafan hawaye masu ɗumi suna tsastsafo mata cikin jijiyoyin idonta.
Ta kuma kasa janye ƙwayar idanunta kanshi. Tana kallon tsarin shigarshi da kullum take ganinshi a matsayin takura.
Lumshe idonta tayi, kana ta buɗe su.
Ummi ta kalla wacce farin cikin ta ya fito fili.
Hakama Hibba. Sai murnar abun takeyi tamkar tayi tsalle ta shiga cikin TV’n,.

Ganin sun sunkuya kai ruku’uh da zasu tafi sujjada ta biyu ne, kuma an ɗaga camerar an maidata ɗaukar samane.
Yasa ta miƙe a hankali bisa santa table dake tsakiyar falon ta ajiye cup ɗin kana ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi kinji masallacin Joɗa ma sun fara sallan kuma muna zaune”.
Da sauri Ummi ta miƙa tare da cewa.
“Farin cikine ya rufeni Shatu,. Muje muyi al’walan mu tafi”.
Uhum tace ta juya ta nufi falonta tana mai share hawayenta da har yanzu suke zubowa, tanajin zuciyarta na amsar wani nannauyan abu a kan Sheykh, ta yarda ta gamsu cewa mutun me ibada da imani da ilimi abin sone a zuciyar kowane mutum na gari.

Bayan sunyi al’wala ne suka fito cikin manyan jihabai ƙatti har ƙasa suka nufi woje.
Ananne Shatu tai mamakin ganin yadda kusufa-kusufa matan masarautar ke fitowa, duk suka nufi hanyar zuwa masallacin ta ƙofar dasu Lamiɗo ke bi.

Suna fitowa jikin masallacin sai ga wani ƙaton rumfa na ƙara an lailayeshi da wani irin yashi fari ƙal-ƙal kana ga hasken wuta a cikinsa.
ko wacce da sallaya a hannunta tuni wasu kuma sunma shimfiɗa sallayunsu sunbi jam’i hakanan matan maƙota da sauran matan bayi da hadimai duk nan suke zuwa.
A jeru gaba ɗaya ananne ga kafaɗar matar sarki gata baiwa.
Babu matsayi ko milki bare isa ko ƙasaita.

Haka dai suka bi jam’i sai ƙarfe uku aka idar akayi addu’o’in kana akashafa aka kai sujjadar ƙarshi ta witirin.

Kana akayi taiya akayi sallama duk kowa ya nufi gidanshi.
Daga nan kuma aka kama aikin sahur.

Suna dawowa Hibba ta kuma kunna TV nan ta samu su tuni su sun idar. Wasu nata ɗawafi ne sai addu’o’in ake jerawa.
wanda sai kaji tsikar jikinka na tashi sabida yadda yake ratsa zuciya da jini.

Washe gari da bayan sallan isha’i da asham, yanzu Jalal da Jamil ne kaɗai ke zuwa dan Imran da Sulaiman ma dasu aka tafi.

Haka yasa yanzu duk suna zama a Dinning table suyi buɗa baki a tare.
Jalal ne ya ɗan kalli Ummi cikin cin Beans salad da Shatu tayi musu.

Hibba ce keta santi tana cewa.
“Alhamdulillah yanzu dai saura mana azumi tara ko takwas”.
Murmushi sukayi, ita kuwa da sauri tace.
“Kai takwas nema in sha Allah”.
Jamil kam tuni yake dariya tare da cewa.
“Tara ne”.
da sauri ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi wai haka ne?”.
Cikin dariya tace.
“A a ban saniba Hibbat.”
Plate ɗin data zuba ferfesun jan nama ta jawo tare da fara ci tana lumshe ido tace.
“Takwas ɗin nema in Allah ya yarda”.
Allah yasa haka Shatu tace.
Sai yanzu Jalal ya ɗan kallesu tare da cewa.
“Ashe dai duk kanwar jace”.
Murmushi Ummi tayi kana sukaci gaba da cin abinci.

Yau dai ana zaton salla saura kwana biyar ko shida.

Da hantsi suna zaune dan yau sun tashi da wuri.
Aunty Juwairiyya ce tayi sallama tare da shigowa, Bayan Ummi ta amsa mata.
Gefen Hibba ta zauna tare da cewa.
“Alhamdulillah Ummi ɗinkunan mu sun dawo, yanzu KB ya kawosu ya shigo ko?”.

“Eh ya shigo mana”.

Juyawa tayi ta kalli Hibba tare da cewa.
“Je kice ya shigo Hibba yana nan zaki kanshi cikin baƙar mota”.
To tace tare da miƙewa da sauri.

Jim kaɗan suka shigo tana gaba da jaka a hannunta yana biye da ita a baya da ƙattin jakunkuna guda biyu da wani yaro shi shima da manyan jakukkunan biyu.

A tsakiyar falon bisa carpet suka aniye jakunkunan kana, ɗaya yaron ya juya ya fita.
Shi kuwa Kabir ya zauna a ƙasa bisa carpet ɗin tare da cewa.
“Barka da hantsi Ummi”.

“Barka dai Kabiru, munyi Sa’a an cika mana al’ƙawarin ko”.

Murmushi yayi tare da cewa.
“Sosai ma kuwa Ummi aini telane mai amana”.
Hibba ce ta ɗanyi murmushi tace.
“To ka bari a yebeka mana”.
Cikin dariya ɗan matashin yace.
“A a ai duniyar yanzu kawai ka yabi kanka, dan ba lallai bane wani ya yaba maka”.
Dariya sukayi duka.
Kana ya fara firfito da kayayyakin.
Ko wanne da sunan maishi a jikinshi.

In ya fito dana Ummi sai ya miƙa mata, in ya fito dana Aunty Juwairiyya da yaranta sai ya miƙa mata.

Hakama na Hibba yana fitarwa yana miƙa mata.

Shatu da yanzu ta fitone, ya kalla tare da cewa.
“Barka da safiya Sayyada Shatu”.
Murmushi tayi Allah ya sani in sun ce mata Sayyada dariya suke bata wato irin ita matar Al Sheykh ko.
Cikin nitsuwa da danne dariyarta tace.
“Barka dai”.
Sai kuma ta ƙara so ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi waye ne shi?”.

“Telan mune”. Ta bata amsa a taƙaicd.
Cike da mamaki tace.
“To ina ya sanni?”.
Hibba ce ta amshi zancen da cewa.
“A hoto ya sanki, da mukaje kai ɗinkunanki hotonki kawai aka nuna mishi, ya ɗinka kuma kinga komai yayi dai-dai ko”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Lallai kam yayi ƙoƙari”.

Cikin dariya yace.
“Uhum ai na iya aikina sosai Sayyada”.
Yanzu kam dariya sukayi duka.
Kana ya zaro kayanta a ƙalla kala takwas ya miƙa mata.
Amsa tayi tare da cewa.
“Sannu”.
Hibba kuwa irga kayan tayi tare da cewa.
“Kb saura kala bibbiyu a namu nan gani basu”.
Kanshi ya ɗan sosa tare da cewa.
“Wannan yarinya akwai son kalato laifin mutum to sai jibi zan kawosu ko kuma in bawa Su Jamil in sunje amsar kayansu”.
Cikin murmushin Aunty Juwairiyya tace.
“Yauwa ka bawa su Jalal ɗin ma kawai”.

To yace, kana ya miƙowa Ummi ƙatuwar jakukkuna guda uku tare da cewa.
“To Ummi ga na yaranki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ka kyauta min Kabiru ngd matuƙa, Allah yayi al’barka”.
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.

Ita kuwa Ummi Saratu ta kwaɗawa kira tana zuwa.
Ta tace.
Jeki kira duk sauran hadimai suzo duk wadannan Kabiru yazo ya gansu ranar.”
Da sauri tace.
“To kana ta juya ta fita.
Ita kuwa Ummi. Inda take zaune ta nunawa Shatu.
Tare da cewa.
“Zo nan ki zauna, zasuzo, ko wacce zata gaya miki sunanta, sai ki duba sunan jikin kayan sai kibata, su duk kala ur’uku akayi musu.

Zaki basu da kuɗi dubu biyar-biyar.
Kai ta gyaɗa kana da sauri ta koma ɗalinta.
Sabida. Sai yanzu ta gano me zatayi da wannan kuɗin da ya bata kenan.
Kuɗin ta kwaso kana tazo ta zauna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button