GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ƙananan robobin da a ƙalla suma nonon dake cikinsu zai kai kwanon sha ɗaya da rabi ta fara firfitarwa.
Kana ta fito da madaidatan ƙoren da zasuci kwanon sha biyu da kaɗan sai manyan da sukaci kwanon sha uku da rabi-rabi.
A hankali ta jerasu kan table ɗin dake tsakiyar kitchen ɗin.
A hankali ta buɗe ƙwaryar forko dake gabanta.
Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah kunɗirmo ya konta yayi bacci yayi kyau”.
Leƙowa Ummi tayi tare da buɗe na kusa da ita.
Nonon yana konce yayi lib ya daskare yayi fari ƙal-ƙal sai alamun maiƙon man nonon da yayi ɗan yellow-yellow kaɗan.
A hankali suka fara bubbuɗe fefeyayen tsakan zaren taburma da aka rufe ƙoren dashi.
Gaba ɗaya duk sun konta sunyi kyai
Yan madaidai robibin da akasa take ɗauka na fura ɗaya na dakkere ɗaya sai na sugar ɗaya kana da ludayin duma. Sai ta jerasu kan fefeyayen da robobin.
Ganin haka yasa Saratu da Laraima suka matso suna taya.
Har saida ta jerasu kab. Gwanin sha’awa.
Manyan ƙore biyu ta maida cikin Fridge.
Kana ta irga sauran tsakanin manya da ƙananan
Ƙoren da robobin su
Talatin da tara
Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
“To Ummi gashi mun gama ki gaya musu duk inda zasu kai.
Zasu isar ko”.
Cikin jin daɗi Ummi tace sosaima kuwa harma da sashin bayi zai isa sabida part-part talatin garemu a cikin masarautar Joɗa.
Sai sashin bayi part takwas.
Cikin jin gamsuwa da tsarin Shatu tace.
“Yanzu a kai ƙore biyu sashin Lamiɗo kana duk manyan iyayen Sheykh akai musu kwarya ɗaɗɗaya, sai sashin Ya Jafar kinga manyan ƙoren sun ƙare sai abin na tsakiyan a kai sauran sashin ƴaƴansu robobin kuma akai sashin bayi”.

Haka kuwa akayi su Sara suka fara rabawa.
Ita kuwa Ummi ita da kanta da Hibba suka kai na sashin Gimbiya Aminatu.
Kana suka dawo da kuloli har uku na abincin sallan da Gimbiya Aminatu ta basu.
Kana ɗaya daga cikin tace na Sheykh ne a ajiye mishi.
Koda suka dawo samu sukayi su Saratu sun gama rabawa kab.
Kamar yadda Ummi ta tsara.
Har sun tattare ko ina sun gyara sun share sun goge sun tafi.
Zuwa lokacin kuwa gaba ɗaya kan dinning table ɗinsu cike yake da Foodflaks iri da kala abinci kala-kala.
Wani irin kallo Shatu tayiwa kulolin kana tayi murmushin da ita kaɗai tasan ma’anarsa ta juya ta nufi tsakiyar falon.

A gaggauce sukayi wonka kowa yayi shirin idi.
Ƙarfe tara saura kwata duk suka fito falo.
Tuni lokacin kuma liman har ya fara huɗuba.
Su Jalal, Jamil Ya Jafar suna tsaye cikin shiga ta al’farma.
Karon forko dataga manyan kaya a jikin Jalal.
Sai kamanninshi da Hamma Jabeer ɗin nasu ya fito sak-sak kamar an tsaga kara hatta rashin yawan dariyarsu iri ɗaya ne.
Sai dai shi Sheykh ko yaushe zakaga lips ɗinshi na motsawa yana tasbihi saɓanin Jalal da zaka ganshi baki a tsuke.

Hibba ce ta fito cikin tarin farin ciki da son Jalal yayi murmushi tare da cewa.
“Masha Allah ya Jalal kayi kyau kafisu duka”.
Ya Jafar dake karatu kamar ko yaushene ya kalli Shatu da Hibba da sukayi shigar atampa iri ɗaya da manyan hijabai har ƙasa ga sallaya da carbi a hannunsu sunyi matuƙar kyau, murmushi yayi musu kana ya juya yayi gaba.
Jamil ne yace.
“Aunty Shatu sai mun dawo, in munci abinci sai mu sharewa.
Oga, Dr, Garkuwa, Malam, akarmakallahu, Sheykh, mijin Sayyada, ɗin ɗakinshi”.
Dariya sukayi dukansu yadda ya jero masa sunayen nashi.
Ummi dake cikin shiga ta al’farma ta miƙa tare da cewa mu tafi.

Suna fita suka rufe ƙofar.

Suka tafi masallacin. Masarautar Joɗa ɗan yin sallan idi.
Suna fita su mata sukayi gefen mata su kuwa maza sukayi gefen maza.

Bayan an idar da sallane kuma sai suka zagaya suka shigo ta asalin ƙofar sukayi yadda sunna ta koyar.

Suna dawowa kuwa a falo suka zube nan sukaci suka sha sukayi
haniƙan.

A dai-dai lokacin kuma su Sheykh dama sauran al’ummar Annabi duk an sauƙo sallan idi.
Suna ɗawafin ban kwana.
Sosai Sheykh ke baza ido ko zai sake ganin wancan mutumin amman ina hakan bai samuba.

Koda suka fito daga ɗawafin ban kwana.
Kai tsaye gidan Sheykh Abdulkareem suka wuce.
Nan yayi musu addu’o’in komawa lfy.
Kusan duk baƙin gidan a ranar suka bar gidan.
Da su Aunty Hafsat ma ranar suka juya Masco hakama Ibrahim.
Koda suka iso Airport kowa da inda ya nufa.
A nan Ibrahim ya ruggume Sheykh tare da ɗan dukan bayanshi yace.
“In Sha Allah Auren Haroon dani za’ayi”.
Shima Sheykh ruggumeshi yayi gam-gam tare da cewa.
“Allah yasa, ina kewar rashinka a ƙasar mu”.
Aunty Rahma ne tace.
“Kai jirgifa ba jiranku zaiba oga Sheykh”.
Sakin juna sukayi kana kowa ya nufi inda jirgin ƙasarsa yake.

Bayan duk matafiya sun shiga, jirgin ƙasar Nigeria wanda zai sauƙa jihar Ɓadamaya.

A hankali ya zauna.
Ya Hashim na gefenshi.
Kasan cewar yana kusa da window ne, ya ɗan juya yana kallon mutanen daketa hada-hadar nufar inda jiragan ƙasar su jihohinsu suke.
Can cikin wasu ayarin mutane maza da mata ya hango wannan fuskar da ya gani.
Sun nufi can ciki suna tafiya yankin da jiragen ƙasar Cameroon suke.
Cikin tarin mamaki ya bishi da kallo tabbas badon jirginsu ya fara ƙugin tashiba da ya fita yaje ya tabbatar da fuskar dattijon da yake hangowa.

A haka dai suka ɓacewa ganinshi.
Kana jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasarmu ta haihuwa.

Ana gida Nigeria kuwa cikin Jihar Ɓadamaya a Masarautar Joɗa.
Zaune suke a falon.
Shatu na waya da Junaidu nan yake ce mata,
Sun samu sauƙi dukansu.
Ance za’a sallamesu bayan salla.
Kuma harda ɗinkunan kayan salla akayi musu.

Bayan sun gama waya da shine ta kira Rafi’a.
Nan suka gaisa har ta bawa Ummi su gaisa.
Bayan ta bawa Ummi wayarne.
Jamil ya ɗan kalli agogon hannunshi a hankali ya miƙe tare da kallon Shatu yace.
“Muje mu gyara Side din boss kar ya dawo ya samu da datti”.
Kai ta gyaɗa mishi kana ta amshi wayarta da Ummi ke miƙa mata.
tare da ce mata.
“Eh dan Allah Shatu tashi maza-maza kuje share wurin da kyau”.
A hankali ta miƙe tare da cewa.
“To.”
Hibba ce ta bisu a baya.
Jamil na gaba ita Shatu’n tana tsakiya.
Hibba na bayanta.
A haka suka shigo falon. Da komai na ciki yake fes-fes babu wani daddi ko ƙura ko hargitsewa, sabida an share falon safiyar yau, sai ƙamshi da sanyi ke tashi.

A hankali Jamil ya ɗan sa hannunshi tsakanin ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu sheƙin Daimond dake matsayin labulen Dinning area ɗin shi.
Ita dai Shatu ido ta zuba mushi,
ganin ya zaro key ɗin a cikinsu.
Ƙofar bedroom ɗin ya nufa tare da cewa.
“Muje.”
To sukace kana suka biyo bayanshi.
Tana nazarin wurin da suke ajiye key ɗin.
Key ɗin ya saka cikin raminshi tare da murzawa.

Da sauri Shatu ta rumtse idanunta.
A hankali take jin zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.
Shi kuwa Jamil tura ƙofar yayi bayan ya murɗa key ɗin ya buɗe.
Wani irin masifeffen harbawa da azaban ƙarfi zuciyar Shatu tayi.

Kutsa kai cikin Jamil yayi.
Tare dasa hannunshi jikin ginin a hankali ya kunna wutan ɗakin hasken ya gauraye ko ina,
jikin window ya wuce ya yaye labulen tare da buɗeglass ɗin.
Iskam cikin Garden ɗin dake bayan window wanda ɗawisu yake ciki.
Ya buso ɗakin.

Juyowa yayi ya kalli Shatu da ke tsaye bakin ƙofar.
“Ku shigo, in nuna miki yadda zakiyi mishi”.
A hankali Hibba ta ratsa gefenta tare da cewa.
“Aunty Shatu mushiga”.
Ido ta buɗe a hankali tare da bin bayan Hibba da kallo.
Kana ta ɗaga ƙafarta da kyar ta.
Taka cikin ɗakin, wani irin azabebben sarawa kanta yayi tamkar ana buga mata guduma a tsakiyar kan.
Cikin rawan ƙafa ta ɗaga ƙafafuwan ta,
Tayi taku huɗu zuwa biyar.
Ta kusa isa tsakiyar ɗakin.
Kenan.
Wani irin jujjuyawa taga kanta nayi.
Wasu irin ababe masu ban tsoro ta fara gani suna gilmawa cikin ƙwayar idanunta, shiyasa taketa jujjuya kanta.
Ta kalli gabas ta kalli yamma ta kalli kudu ta kalli arewa.
Hibba ce ta juyo tana kallonta jin Jamil nata mgna bata bashi amsaba.
Cikin sauri ta matso kusa da ita ganin yadda taketa jujjuya kai, ga idanunta da suka juye suka zama kamar harari garke, kana sai Rollin ball eyes ɗin ta take da sauri-sauri.
Cikin Mamaki Hibba tace.
“Aunty Shatu! Aunty Shatu!!”.
Shiru ba amsa hakane yasa.
Jamil juyo kanshi ya kalli inda suke, da sauri ya juyo gaba ɗaya jikinshi ganin.
Wani irin karkarwa da jikin Shatu keyi.
Hibba kuwa da ƙarfi cikin tsoro tace.
“Aunty Shatu lfy kuwa?”.
Ita kuwa Shatu, zuwa yanzu bata jinsu bata kuma fahimtar me suke faɗa hankalinta ya juye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button