GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin wani irin layi da rawan jiki tamkar mazari ta nufi tsakiyar ɗakin.

A nan ta tsaya gis gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Cikin tsananin tsoro da firgita.
“Hibba ta juya a guje tana cewa.
“Wayyo Ummi! Ummi!! Ummi!!! Kizo zakiga yadda Aunty Shatu keyi.”
Ummi dake falo ita da Aunty Juwairiyya,
Kamar daga sama suke jiyo muryar Hibba tana rabka musu kira cikin firgici da razani.
Haka yasa Ummi da Aunty Juwairiyya miƙewa da sauri suka nufi corridor’n da suke jiyo muryar Hibba na fitowa.
Kiciɓis sukayi a bakin ƙofar falon.
Cikin sauri Ummi ta ture Hibba ta wuce da gudu ta nufi cikin ɗakin.
Sabida jiyo muryar Jamil na cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahuwani’imal wakil. Ummi! Ummi!! Kizoooo”.
Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka shigo.
“Dai-dai lokacin kuma rawan da jikin Shatu keyi ya tsananta.
Wani irin kuka tasa tare da tafiya ƙasa luuu zata faɗi

Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka tarota.
Bisa jikin Ummi ta faɗi hakan yasa itama Ummi tayi ƙasa ta zauna.

Babu abinda suke maimaitawa sai innalillahi wa innailaihi rajiun.
A kiɗime cikin tsananin gigita Jamil yace.
“Subahanallahi Ummi ta sumafa”.
Jiki na rawa Aunty Juwairiyya ta juya da gudu babban falon ta fito tare da ɗauko goran ruwan sanyi.
Kana ta juyo a da sassarfa ta nufi can.

Hibba kuwa a gigice take gayawa Jalal da Ya Jafar abinda ke faru.
Da sauri ya Jafar ya tashi ya nufi can.

Jalal kuwa ya zauna dan ya lura Hibba tayi masifar tsorita.

A ɗakin nashi kuwa,
Shiru ta lafe jikin Ummi kamar babu rai koda.
Ummi ta yayyafa mata ruwan sanyi a fuskarta, a banza saida ta kuma watsa mata a karo na uku ne.
Kafin taja wani dogon numfashi cikin sanyi da tsoro Ummi tace.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ta sunkuyo kanta tana ɗan kiranta.
“Shatu! Shatu!! Shatu!!!”.
Ba amsawa kuma bata buɗe ido ba,

A hankali ya Jafar ya zauna gefensu, karatun da yakeyi yaci gaba dayi.

Cikin sanyi ta buɗe idanunta.

Sai kuma ta yunƙura a hankali ta tashi zaune.
Da sauri Ummi ta zaro ido ganin yadda idanunta suka juye a murɗe.

Ita kuwa Shatu miƙewa tsaye tayi, cikin rawan sanyi da karkarwa, ta fara zagaya ɗakin a hankali taje baki Bathroom nanma buɗe ƙofar tayi ta shiga.
Jim kaɗan ta fito.
Idanun suna yadda suke sai dai.
Yanzu hawayene keta shatata babu ƙaƙƙautawa.
A hankali tazo bakin gadon.
Sai kuma kawai sukaga ta faɗa kan gadon a sune!
Wannan shine tashin hankali da ba’a samishi rana.
Da gudu suka kumayi kanta, cikin firgici da tsananin tsoro Ummi ta ƙara yayyafa mata ruwan.
Amman shiru, haka suka tsaya cirko-cirko, shi kuwa Ya Jafar sai gashi yana karatu yana kuka kamar dai yadda yakeyi kafin a auro Shatu a masarautar Joɗa in Sheykh baya nan.

Gaba ɗaya sun birkice sunma rasa me zasuyi.

Aunty Juwairiyya kuwa itama kuka ta farayi.
Jiyo kukanta da na Ya Jafar ne yasa, su Jalal da Hibba shigowa.
Ganin tana can yashe kan gado a sumene yasa Hibba ma kuka.
Cikin ƙarfin hali Jamil yace.
“Aunty Juwairiyya Hibba kada kuyi kuka, kuja hankalin mutane nan.
Gashi yau salla ba mamaki akwai mutane a cikin Garden.”
Cikin tashin hankali Ummi tace.
“Bari inje in sanarwa Gimbiya Aminatu abinda ke faruwa, ta sanarwa Lamiɗo, sai in biya in sanarwa Hajia Mama.”
Da sauri Aunty Juwairiyya tace.
“Eh yafi kam”.
Ta juya zata fita kenan sai sukaji tayi wani irin nakasheshen dogon numfashi mai sassanyan sauti.
Da sauri Ummi ta juyo ta dawo jikin sanyi tace.
“Shatu! Shatu!! Shatu!!!”.
Shiru babu amsa sai binsu da ido tayi ɗaya bayan ɗaya.
Ganin hakane Jamil ya matso.
Tofi ya farayi mata.

Ummi kuwa ci gaba da kiran sunanta tayi.
Cikin tsoro Hibba tace.
“Ummi kinga idonta ya koma dai-dai.”
A tare sukace Alhamdulillah.
Sai kuma Ummi ta kuma kiranta.
“Shatu!”.
A hankali tace.
“Na’am Ummi”.
Sai kuma ta kalli inda take, kana ta juya ta kallesu baki ɗayansu, cikin mutuwar jiki ta yunƙura ta tashi.
Murya a sanyaye tace.
“Jamil sharan kenan ka tsaya kanata kallona.
Gaya min ya za’ayi sharar”.
Cikin sauƙe tagwayen numfarfashi suka kalli juna,
Cikin mamaki Jamil yace.
“No ki huta kawai my Aunty zan share”.
Bata da ƙarfi a jikinta ko ta dage tace sai tayi sharar.
Bazata iyaba jikinta duk a mace.
Hakane yasa tace to.
Hannu ta miƙa Ummi tare da cewa.
“Ummi ɗan jamin hannuna mana”.
To tace tare da kamo hannun.
Ta tsaida ita, cikin tafiyar sanɗa ta juya ta nufi hanyar fita.
Binta sukayi a baya gaba ɗayansu.

Jamil kuwa dube-dube yayi a cikin ɗakin kana.
Ya fara tattarewa da kimtsawa da sherawa, ya canza mishi beshit and blanket, da rigunan pillows.
Kana ya goge ko ina fes
Sannan ya shiga bathroom ya wonke ya goge mishi.

Su kuwa suna biye da ita har falonta.
Ganin ta wuce bedroom ɗinta ne yasa Hibba da Juwairiyya suka tsaya.

Ita kuma Ummi tabi bayanta.

Ganin tana shiga ta hau gado ta kwanta ne a take sai bacci yasa Ummi ta juyo ta fito.

Can babban falon suka koma suka zauna.
“Ikon Allah sai kallo wannan abu da ban tsoro da ban mamaki”.

Ummi ta faɗa cikin al’hini.

Jiki a mace Aunty Juwairiyya tace.
“Sosai kam wannan al’amari ya firgitani”.
Hibba dai sai zuru-zuru tayi da ido.

Nan sukayi ta mamakin wannan abin.

Jamil na fito shida Jalal suka tafi.

Shi kuwa Ya Jafar bayan matarsa yabi suka tafi.

Hibba kuwa da Ummi nan suka zauna.
Ummi ce ta kalli Hibba tare da cewa.
“Sai anjima zan kira Umaymah na sanar mata abinda ya faru”.

Kai kawai Hibba ta kaɗan mata.

Ita kuwa Shatu baccin tayi mai nauyi sai kiran sallan azahar ne ya tasheta.

Su Sheykh Jabeer kuwa suna can sunata keta hazo.
Tafiya awa huɗu ne zai kawosu ƙasar mun.

A hankali ta buɗe idonta, miƙa tayi tare da yin salati.
Kana ta tashi zaune.
Bathroom ta shiga, wonka tayi da ruwan ɗumi.
Kana tayi al’wa tana fitowa.
Ta zura Hijabi tayi salla.
Bayan ta idarne, ta zauna gaban dreesing mirror.
Simple makeup tayiwa fuskarta.
Sannan ta sauya shiga, wani tattausan lace mai ɗan karen kyau da tsada tasaka duguwar rigace tayi cib-cib da jikinta. Kasan cewarta kalar pink guava da ɗigo-ɗigin mint green ne yasa tayi masifar dacewa da kalar jikinta.
Gyara gashin kanta tayi ta tubƙeshi tare da kitsen jelar.
Ta saketa bisa kafaɗunta.
Ɗaurin asseta tayi ya zauna ɗas a kanta, tattausan gyale minti green color ta yafa a kafaɗunta.
Kana ta fesa turarukan ta masu daddaɗan ƙamshi.

Sosai jan lallen gargajiya dake kan ƴan fararen yatsun hannunta yayi masifar kyau.
Ga kuma zanen da akayi a saman hannun hakama ƙafafun ta, suma sun sha zanen jan lalle tayi kyau sosai,
Ta fito ras da ita.

Baki ɗauke da sallama ta foto falon.
Cikin murmushi Ummi ta amsa sallamar tana mai kallonta,
Hakama Hibba da Ummi ta kokkontar mata da hankali taji tsoron ya ragu.
Gefen Ummi ta zauna, tana kallon Hibba na ɗaukarta hoto tana cewa.
“My Happiness Aunty kinyi kyau”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Na kaiki ne?”.
Da sauri Hibba tace.
“Kin fini ma”.
Murmushi ta kumayi tare da cewa.
“Ngd matuƙa”.
Sai kuma ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi me zamuyi abincin dare”.
Cikin jin tausayinta Ummi tace.
“A a akwai abinci harda na gobe da safe ma, yanzu kam ki huta, sai dai in akwai abinda kikeso ki gaya min in yi miki”.
Kai ta jujjuya alamar a a kana tace.
“To Ummi a kaiwa Hadimai wani abincin kada ya lalace a banza ko”.
Cikin gamsuwa Ummi tace to.

A can Airport kuwa ƙarfe uku dai-dai jirgin Ahlin masarautar Joɗa ta sauƙa.
Nan motoci suka kwatsosu.
Suna isa masarautar ana kiran sallan la’asar hakane yasa matan cikine kawai suka shiga cikin gida su mazan.
Masallaci suka wuce.
Ana idar da salla kuwa fada suka wuce baki ɗayansu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button