GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A sashin Gimbiya Saudatu kuwa wani irin dariya mai cike da masifar jin daɗi tayi tare da cewa.
“Dai-dai kenan yaro zai dawo ya taradda da mummunan lbrin matarsa ta zama zautacciyar mata…!

                      By
       *GARKUWAR FULANI*

“Mummunam labarin amarya ta haukace.
Ai kaɗan ma kenan, kowa yaci tuwo dani miya yasha. Hegen yaro mai jajayen kunnuwan da shegen baki mutun nace masa cuta zai ce ajali, kana ce mishi cas zaice maka kulle, wannan bakin nashi mai zaro zance da inada hali dana rufeshi kirib”.

Hadimarta dake zaune gabanta wacce taji cikekken bayanin abinda ya faru da Shatu a sashin Hajia Mama da itama yar rahotontace ta kamo mata.
Shiyasa itama ta kawo mata rahoto.
Cikin jin daɗi ta kalli Laminu dake gefe yanata murmushin jin daɗi tace.
“Shiga ɗaki zaka samu kuɗi a kan gadona, kazo ka bata tukuicin wannan daddaɗan labari mai armashi”.
To yace kana ya miƙa ya ɗauki kuɗin yazo ya bata, tayi godiya kana ta miƙe ta fita.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu Baba Basiru da Baba Nasiru ta kira ta shaida musu abinda ya faru.
Nan sukayi ta murnar abun, da shirya yadda abin zai ɗunguzuma yaci gaba.

A can su Sheykh kuwa saida aka idar da sallan isha’i kana kowa ya nufi Side ɗinsa kamar yadda sukeyi duk shekara in sunje umrah sun dawo.

A Babban falon sashin Jabeer kuwa.
Ummi ce zaune bisa kujera Hibba na gefenta.
suna mgn da Umaymah a wayar Hibbab nan Ummi ke sanarwa Umaymah abinda ya faru ɗazu da hantsi na firgitarwa.
Cikin tarin mamaki da al’ajabi da tsoro tace.
“Ummin Jabeer to yanzu ina take? Kuma ya jikin nata? Meya jawo hakan ne?”.
Juyawa Ummi tayi ta kalli bayanta a hankali tace.
“Tana ɗakinta tunda tayi sallan isha’i ta konta, yau ko abinci babu abinda taci, tunda gari ya waye, dan koda muka dawo idi munci dukanmu amman ita ko ruwa bata shaba, kuma har yanzu babu abinda taci”.
Cikin fargaba Umaymah tace.
“Jazlaan ɗin ya shigo wurinku ne? Ya sanine ko bai saniba?”.
“A a bai shigoba, eh gsky babu wanda yasan da wannan zancen duk Masarautar Joɗa, saini, da Jamil, Jalal, Hibba, Juwairiyya, Jafar.
Mune kaɗai muka san da zancen”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Umaymah ta sauƙe cikin sanyi tace.
“Kada ku damu zanyi mgna da Jazlaan, kada ku gaya mishi, in lokacin saninshi yayi zai iya sani”.
Ta tace tare cewa.
“Masha Allah gashi ma sai yanzu ya shigo”.
Tana faɗin haka ta katse kiran.
Ta miƙe da sauri hakama Hibba cikin jin daɗi suke cewa.
“Oyoyo mutanen saudia garin Manzon Allah, Barka da zuwa lfy da dawowa lfy”.
Ɗan gajeren. Murmushi yayi tare da ƙarasowa cikin falon.
Jalal, Jamil, Ya Jafar na biye dashi a baya.
Bisa kujera ya zauna tare da kallon Ummi fuska ƙunshe da annuri yace.
“Barka dai Ummi na sameku lfy!?”.
“Lfy lau Alhamdulillah Sheykh ya kuka baro Sheykh Abdulkareem da ahlinshin.
Ina mai sunanka Sheykh Jabir Ali”.
Cikin jin daɗin kulawarta ga yan uwan mahaifiyarshi yace.
“Alhamdulillah suna lfy, Sheykh Jabir Ali yace in gaidaku gaba ɗaya”.

Cikin jin daɗi tace.
“Ina amsawa kuwa ngd matuƙa”.
Jamil dake riƙe da jakukkunan da Sheykh yace ya ɗauko a motarsa ne ya wuce dasu.
Yaje ya ajiyesu a bedroom ɗin shi kana ya dawo falon.

Hibba kuwa ruwa ta kawo mishi.
Murmushi yayi tare da amsar goran zam-zam ɗin yace.
“Baku shanye tsohon ba Ummi ni gashi na samo sabo”.
Hibba ce ta ɗan kalleshi tare da cewa.
“Hamma Jabeer, su Sitti ma sun dawo ne?”.
Kai ya gyaɗa mata alamar eh.
Kana ya miƙe tare da cewa.
“Ummi bari inje in ɗan huta”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai dole kam saida hutu dan gajiya da rashin bacci kam ka kwasosu dole kayi ramuwar bacci”.
Ta ƙarishe mgnar tana kollonshi tuni ya shiga corridor’n shiga cikin falonshi.

Dama kuma tuni ita da kanta ta kai mishi abinci a Dinning table ɗinshi.

Nan sukaci gaba da hira.
Hibba na cewa.
“Umaymah na ta dawo na kusa komawa”.
Cikin taɓe fuska Jalal ya kalleta a fakaice.
Jamil kuwa dariya yayi tare da cewa.
“Za dai ki gudu yarinya faɗi gskyarki”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Ba wani tsoro ai na gaya mata ta kontar da hankalinta.”
Jafar kuwa karatunshi yakeyi.
A hankali saɓanin baya da in zai karatun da ɗan ƙarfi yakeyi.

Sosai suka ɗan yi hira kana suka watse kowa ya tafi makoncinsa.

Shi kuwa Sheykh yana shiga.
Ya rinƙa sauƙe numfashin gajiya tare da rage kayan jikinshi.
Wonka ya shiga yayi kana yasa wasu riga da wondo masu taushi yazo ya konta.
Ba tare da yasha ko ruwaba, sabida tarin gajiya da bacci.
Gaba ɗaya wunin yau a zaune yayi yishi ko a ɗan tsaye.
Gashi rabonsa da bacci tun jiya da safe da ya ɗanyi kaɗan kafin ya tafi harami sallan walaha.

Yana konciya kuwa yayi addu’o’in ya shafa jikinsa.
Kana ya fuskanci allon majigi dake liƙe a bongon ɗakin wanda yake ɗauke da full ƙura’an. Karatu ya farayi daga ƙasa zuwa sama wato nasi.
Ɗaga nan bacci yayi awon gaba dashi ko inna’alzzan bai jeba.

Ummi da Hibba kuwa suna isa falon Shatu cikin kula Ummi tace.
“Kije ku kwana kinji ko Hibba babu abinda zai sameki,
Bazata miki komaiba, bata da lfy bai dace mu barta ita ɗaya ba”.
Cikin sanyi Hibba tace.
“Gsky Ummi bazan iyaba wlh ina tsoro”.
Cikin hikima Ummi tace.
“To muje ki hau gado ku kwanta ni kuma sai in kwanta a ƙasa kam carpet ɗin.
Gyada tayi cikin gamsuwa da hakan.

Haka sukayi Ummi ta kwanta a ƙasa ita kuma Hibba ta konta gefenta a ɗan tsorace.

Ita kam Shatu batama san sunayi ba, domin bacci mai nauyi takeyi.

Haka dai Ummi tai shiru saida ta tabbatar Hibba tayi bacci kana ta koma ɗakinta.

Washe gari da safe bayan Ummi, Saratu, da Hibba sun gama karyawa ne.
Shatu da tunda tai sallan asuba ta koma ta konta kan sallayar sai yanzu ta fito.
Tayi wonkanta fes ta ƙenƙesa ado da kolliyar ta ba irin mai ramɓatsau ɗin nan ba.
Komai dai-dai tayi abunta.
Riga da siket ne na Mateyal mai taushin gaske, White Coffee mai kyau.
sai ɗan ƙaramin gyale ta yafa a kanta, cikin nitsuwa ta fito.
A falo ta zauna tare da juyowa ta kalli Ummi dake shirya abinci a Dinning table.
“Ina kwana Ummi”.
Tace cikin muryarta Normal.
Cikin kulawa Ummi ta juyo tare da cewa.
“Lafiya lau Shatu. Kin taso kenan”.
Murmushi ta ɗan yi tare da cewa.
“Ummi meyasa baki tadani ba, kika shiga kitchen da kanki”.
Kai ta jinjina tare da ɗaukan cup mai ɗan girma,
Tea mai kauri ta haɗa a ciki kana,
ta taho inda take miƙa mata cup ɗin tayi tare da cewa.
“Gashi amshi kisha, aiki kam ai saida lfy”.
Amsa tayi tana murmushi a hankali tace.
“Lfyata lau ai Ummi kawai dai baccin ne ban san meyasa nake ta yinshi ba”.
Kai kawai Ummi ta gyaɗa mata,
Kana ta juyo tace.
“Hibba kawo mana namu abincin nan muci.

Najiyo Muryar Jamil suna zuwa, kuwa wata ƙil dasu Imran zasu zo”.
To tace kana ta ɗauko musu nasu Foodflaks ɗin da plate and spoons da ta kawo musu.

Jolof ɗin taliyace da kifin banɗa dasu Kabeji da karas da green beans da dai sauran kayan haɗin.
Sai kuma, ferfesun kayan ciki.
A plate ɗaya Hibba tasa musu, da ita kana ta sawa Ummi.
Kana tasa musu fork, tare da cewa.
“Bismillah Aunty Shatu sauƙo muci ko”.
To tace kana ta sauƙo,
suka fara cin abincin.
Amman ina tayi loma ɗaya sai ta kusan 4 minute bata kuma sawa a bakiba.
Sai dai ta shanye tea ɗin ganin hakane yasa Ummi ta ƙara haɗa mata wani shayin.
Shima ta shanye abinta fes, taliyar kuma baifi cokali biyar ba tayi.

Su Jalal kuwa suna shiga suka wuce Dinning area suma sukayi breakfast ɗin kana suka fita, sabida hidimomin salla. Domin yau za’ayi hawan daba, Jalal kuma mayene mai zaman kanshi a kan sarrafa, doki, ɗan daga Affan sai shi.
Bayan Sheykh a iya sarrafa doki kab Masarautar Joɗa .
Amman shi Sheykh ya daɗe da cewa shi ya girma da yin wannan sakarcin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button