GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Su Ummi kuwa, kitchen Suka kuma shiga.
Sanin yau tabbas akwai baƙi masu ɗimbin yawa da masarautar Joɗa zata amshi baƙoncinsu.
Domun ƙananan sarakunan wasu garuruwanma duk zasu zo da tawagar su.
Haka yasa suka shiryawa taron haiƙan ƙadaran ko wani Side dake gidan za’ayi abinci a ciccika manyan kuloli a kai fadar Lamiɗo, wani a kai sashin bayi.
Kana kuma ko wani Side da baƙin su.
Haka yasa su Ummi da Saratu da Larai zagewa.
Sukayi abinci kala-kala kana suka ciccika kulolin aka kai fada akai wurin bayi.
Sannan sukayi nasu kuma suka sassaka a Foodflaks masu ɗan karen kyau suka jera a Dinning table,
tare da plate, spoons, and forks. Kana sun cika Fridge kuma da drinks kala-kala.
Sun kuma yi Pepper Checken mai zafi na zabbi.

Sai kusan ƙarfe ɗaya suka gama komai,
Su Saratu suka kimtsa komai kana suka tafi.

Su kuma duk suka shiga ɗaki da nufin yin wonka.
Tuni zuwa lokacin Masarautar Joɗa ta fara ɗinkewa da baƙi tako wani sashin.

Sheykh Jabeer kuwa, tunda ya tashi.
Ya nufi cikin Garden ɗin nan da ababen tarihin masarautar Joɗa yake.

Zazzagayawa yakeyi yana dubawa, dan tabbatar da babu wani abun da zai cutar da wani ko wata.
Sabida yasan yau manyan baƙi zasu shigo ciki.
A nuna musu ababen tarihi da dai sauransu.

Gefen da curin da macijiyar nan yake ya nufa.
Ya dudduba ƙofofin ba hayaƙi ba komai.
Sai dai in mutun ya kasa kunne zaiji sautin numfashin macijiyar ka da ƴan ƙanana kuka irin na ƙananan macizai.
A hankali ya ƙara matsowa bakin curin. Cikin nitsuwa yayi gyaran murya.
sai kuma yaji sautin kukansu da kuma numfashin uwar ya ƙaru sosai.
A hankali yace.
“Assalamu alaikum, ya ke wannan halittar Ubangijin sammai da ƙasai”.
Gyara tsayuwarshi yayi jin numfashin na ƙara matsowa.
A hankali yace.
“Ba cewa nayi ki fitoba, nazo in roƙeki ne kamar yadda Manzon Allah ya sanar mana, dukkan halitta tanaji.
Kuma ina kaga wani abun cutarwa a gidanka ka haɗashi da Allah da Manzonsa kace ya fita.
Manzon Allah ya bamu tabbacin.
Muddin ba mai cutarwa bane zai fita.
In yaƙi fita kuwa ka kasheshi”.
Ɗan zagaitawa yayi jin kukansu ya kuma tsananta, cikin sanyi yace.
“Ni bazan roƙeku kan ku fita ku bar muhallin zamanku da ban san tsawon shekara nawa kuke rayuwa a wurinba.
Kuma bansan dalilin zamanku a wurinba.
Shiyasa bazance ku bar Masarautar Joɗa ba.
Kuma bazan kasheku ba,
Sai dai roƙana garemu.
Munada baƙi a Masarautar Joɗa kuma yau zasu shigo, dan Allah da Manzonsa, kada ku fito ku baiyana kanku ga baƙinmu kada ku razana mana baƙi kada ku cutar mana da mutanenmu.
Kuyi zamanku a muhallin ku”.

Shiru sukayi tsit alamun sun jishi kuma sun gamsu”.
Fahimtar hakane yasashi cewa.
“Na barku lfy”.
Yana faɗin haka ya juya, Lamiɗo da Galadima ya gani tsaye a bayanshi.
Murmushi sukayi tare da matsowa inda suke.
Galadima ne yace.
“Kada ka damu da fitarshi da zamanshi da yaranshi
Domin kai ke ganinshi a nan, amman duk in da wani mugu ya shigo masarautar Joɗa da nufin yiwa Lamiɗo wani abun zai ganta da yaranta a gabanshi.

Amman wanda yake jinin wannan gidan bazai ganshiba.
In kaga mutun ya ganshi saida sahalewar Lamiɗo”.
Shiru yayi yana kallonsu.
Shi kuwa Lamiɗo a hankali yace.
“A ƙalla yafi shekaru ɗari biyu da arba’in a cikin wannan curi a wannan Masarautar tun zamanin baban kakana Joɗo yake nan, ba kuma tsafi bane, ba sihiri bane, kamar yadda kowa ya sani shi maciji curi gidan zamansa ne, to bulalin caɗin masarautar Joɗa kuwa suma asali nan suke da zama curin ne ya binnesu, kana macijiyar ta shiga ciki, shine ma dalilin hana shaɗi to sai dai lokaci zuwa lokaci in an sarki maici yazo wurin yayi sallama macijiyar kan fito, in zata fito takan fito da balalin a binɗinta. Sai daga baya ta fara fita ita da ƴaƴanta suna yawo cikin masarautar Joɗa ne, muka gane yunwa ke sata fitowa, sai ta shiga cikin kaji tasha kwayaye ta haɗi ƙananan kaji.
Lokacin da muka fuskanci haka sai muka fara kawo mata kwai a matsayin abincinta.
Daga baya muka fahimci in mutun ya shigo da mugun nufi tana razanashi”.
Taɓa bakinshi yayi cikin rashin yarda bare gamsuwa yace.
“Ni dai ban tambayeka ba, inma tsafine kaidashi Ni nan Muhammad Jabeer bani dalaifi a ciki nayi-iya yina in rabaku da wannan tsarabe-tsaraben na masarauta kun ƙiya”.
Ya ƙarishe mgnar yana juyawa ya nufi wurin da tsuntsayen wurin suke.
Gefenda aku yake ya nufa.
Tana ganinshi ta kaɗan fiffigenta tare da cewa.
“Sheykh Jabeer ya dawo”.
Murmushi yayi tare da shafa kan akun yace.
“Ya dai tsuntsuwa mai daraja ya gida”.
Cikin irin mgnarsu na Ali tace.
“Lfy Sheykh ya madina garin Manzon Allah”.
Ta ƙarishe mgnar tana kaɗa kanta da jelarta alamun yiwa sauran tsuntsaye rigimar ance mata tsuntsuwa mai daraja.
Murmushi mai faɗin Sheykh yayi ganin.
Ɗawisun nan tazo gabanshi ta tsaya ta buɗe dogon jelanta ta kaɗashi tayi sama dashi.
har yana taɓa gemunshi cikin sanyi yace.
“A a kekyawar tsuntsuwa mai kyan ado da tafiya”.
A hankali ta karkaɗa jelan kana ta fara zagayashi.
Tana nuna mishi kyan tafiyar.
Su kuwa sauran tsuntsaye kuka suka farayi.
Murmushi mai faɗi ya kumayi tare da cewa.
“Tsuntsaye masu zaƙin murya da sauƙin firewa”.
Aifa nan suka tashi sama suna shawagi a wurin.
A hankali ya juyo ya kalli tarin tattabarun dake gabanshi mazan ciki suna ƙotowa wa matansu.
Kai ya rausayar tare da cewa.
“Iyayen soyayya duk cikin tsuntsaye bayaku a soyayya”.
Ai sai suka fara irin kukansu nan guggdu-gudduu guuu”.
A hankali ya fita yankin tsuntsayen bakin ƙoramar dake gudana a tsakiyar Garden ɗin ya nufa.
Inda agwagin ruwa keta shawagi a bakin wurin.

Zama yayi yana nazartan lamuran halittun ɗan adam.
Ko wanne halitta akwai mace akwai na miji.
Kuma ko wanne halitta namiji baya iya rayuwa saida macce.
To shi menene matsalarsa da duk manyan likitocin duniya suka kasa ganowa, kowa sai yace mishi lafiyarshi lau.
Shi kuma yasan baida lfyar maza, tunda bai taɓa jin wani abu ya motsa a zuciyarshi bare yasa wani sashi na jikinsa motsawa ba yana dai jin shi wasu lokutan a namiji jim kadan lbri zai sauya.
Gefenshi Lamiɗo da Galadima sukazo suka zauna.
Bisa wani carpet da hadimin da ya shigo yanzu ya shimfiɗa musu.
Yana fita wani ya shigo da kayan abinci.
Cikin kula Lamiɗo yace.
“Taho nan muci abinci Ustazu”.
Hannunshi yasa ya shafa cikinsa.
Sosai yakejin yunwa hakane ya sashi gyara zama nan sukaci abinci su ukum su.

Gani. Ƙarfe ɗaya tayine, lokacin salla ya ƙara to.
Ga ɓaki nata shigowa masarautar Joɗa.
Yasa suka tafi.

Shi yana shigowa bathroom ya wuce. Wonka ya fesa mai rai da lfy kana yayi al’wala.
Kana ya fito ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da gajeren wondo 3 qtr yasaka kana yasa tattausar rigar mai guntun hannun. Duk kalarsu Royal blue ne, sai ya ɗauka farar jallabiya. Fara mai ɗan karen kyau.
Kana yasa baƙar al’kyabbar jikinshi tare, dasa hirami mai fari da ja, yayinda hakama takalmanshi fari da ja.

Wasu sabbin turaran da ya seyo ya fesa a kan sabbin kayan da ya saka masu ɗan karen kyau.

Wani irin ƙamshi yakeyi mai daɗin shaƙa.

A hankali ya fito falonshi, kallon abinci dake jere kan Dinnin yayi kana ya wuce ya fita.
A falon ya samu su Jalal da alamun da al’wala a jikinsu.
Can falon Shatu yajiyo muryarta tana kiran Hibba dake ɗakin Mama.
Sai yanzu da yaji muryarta ne ma shi ya tuno da ita a gidan.
Kai ya kaɗa yasa ƙannenshi a gaba suka tafi.
Suna isa masallacin akayi sallan azahar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button