Ƙarfe ɗaya da mintu arba’in suka firfito masallacin da ya cika yayi maƙil mafi akasarin matasa suna cikin shigar sukuwane.
Yana fitowa gida ya nufa sabida bai son yawan hayaniya, kuma zaiyi baccinsa da ya saba dashi, baccin tsakanin azahar da la’asar.
Su Jalal kuma cikin abokansu suka nufa.
Yana dawowa Falon Hibba kaɗai ya samu ta kunna tv tana kallon Film ɗin India kamar zai hanata kuma dai sai ya wuce.
Bayan tayi mishi sannu da dawowa.
Yana shiga ɗakin ya tura ƙofar ɗakin ya rufe ba tare dasa key ba.
Kana yasa hannunshi ya kashe fankar, tare da kashe wutan ɗakin.
A hankali ya iso bakin gadon. Zare Al’kyabbar ajikinshi yayi ya ajiyeshi bisa gadon.
Kana ya zare jallabiyar jikinshi itama ya ajeta kan gadon ya rage dagashi sai 3 qtr da ƙaramar rigar.
Dan sosai yake jin bacci, sanadin ɗan zafin hadarin dake haɗuwa yayi yawane yasa ya ƙara gudun AC kana.
A hankali yayi taku zuwa, gefen gadon agogon hannunshi ya cire ya ajiye a kan Bedside drower’n dake kusa dashi.
Konciya yayi a nan a ƙasa bisa tayis babu shimfiɗan komai bare pillow.
Wannan tsarinshi ne da yakeyi, wanda yanayin hakane dan tuna konciyar ƙabarin da wata rana zai riskeshi.
Wani lokacin ma, harda AC’n yake kashewa.
Yana konciya ya fara tasbihi yanayi a hankali idonshi na rufuwa, wannene yasa yakeyin bacci a lokacin da yaso.
A can cikin masarautar Joɗa kuwa.
Cikin wani irin farin ciki Jalal Jamil suka nufi Side ɗin Hajia Mama jin labarin Ya Affan ya dawo daren jiya karfe biyun dare, a bakin Imran
A falo suka samu Hajia Mama cikin tarin bege da kewar ɗan uwan nasu Jalal yace.
“Mama wai Yah Affan ya dawo?”.
Cikin murmushin tace.
“Eh ya dawo”.
Da sauri Jamil yace.
“Yesss Jalal zomu tafi tafi Side ɗinshi Aunty Mami an shawo turai an dawo”.
Da sauri suka tsaya jin Mama na ce musu.
“Basa nan tunda safe Aunty Mamin naku ta matsa ya kaita gida wai Abban Yusuf ba lfy, to sun tafi can, Aryan ma yazo bai sameshi ba shima ya tafi can duk sun haɗe a can”.
Da sauri Jalal yace.
“Muje mu ɗauko shi dan wlh su Hamma Yusuf da Ya Aryan bazasu barshi ya dawo da wuriba”.
Cikin murmushin Jin yadda yaran ke son Juna tace.
“Yanzu kuwa zasu dawo, dan kunsansu duka uku da son daba, sun girmama su basu bar hawa doki da tsereba kuma kasan Yusuf zaice suzo wurin uban gidansa Malam Jabeer”.
To da hakane suka ɗan gamsu suka nitsu.
A can Dou Gire kuwa samun jikin Abban Yusuf da sauƙine yasa.
Suka shirya suka nufo Masarautar Joɗa.
Ummi ma tayi kolliyar sallanta tayi kyau ta fito falon, inda Hibba take.
Shatu kuwa tana ɗakinta lokacin ta gama yin kolliya tasa wani damdatsen Shadda lace mai masifar kyau, Royal blue ne mai kyau da ɗaukar hankali sai zaren lace-lace ɗin da akayi da red and pink guava mai masifar kyau, sai wani irin sheƙin shaddar takeyi tana fidda maiƙon kyau.
Doguwar rigace inrin fitet ɗin nan na zamani mai ɗan karen kai duk inda sirin yanken fisis ɗin yake an bishi da jerin duwasun shuwa riski masu sheƙin Daimond, cib-cib rigar tayi a jikinta.
Murza ɗauri ɗan kwali tayi irin mai stpes ɗin nan
Kana ta tura ɗan kwalin kaɗan wannan tattausan saje da suman dake konce a goshinta ya fito ras.
Sai ta baya kuma ta tsakiyar ɗan kwalin ta bar rami ta fito da jelan gashinta ya konto har kafaɗanta ba tare da ta kitseshi ba.
Wasu ƴan kunne da sarka na azurfa ta saka a wuyanta,
sai wani kekyawan agogon fata rea ƙirar Gucci ta manna a tsintsiyar farin hannunta da yake, ɗanɗase da zanen jan lalle mai kyau.
Gyale rea color mai masifar kyau ta ɗan yafa a kafaɗunta.
Wasu turaruka kala biyu ta fesa, kana ta kalli muskarta da jikinta a madubin.
Wayarta ta ɗauka ta ɗan kaikaice ta ɗauki kanta hoto ta cikin madubin tayi kyau sosai.
Wasu takalma marasa tudu tasa suma rea color ne.
Tana riƙe da wayarta ta fito falon.
Da sauri Hibba ta miƙe tare da cewa.
“Wow! Wow!! Wow!!! masha Allah Aunty Shatu kin ganki kuwa masha Allah.”
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
“Kai gsky amaryar Sheykh ta fito da madarar kyau masha ALLAH”.
Ita dai sai murmushi takeyi dace musu.
“Ngd”.
Cikin jin kunya.
Hibba kuwa duk takun da motsin da zatayi sai ta ɗauke ta hoto.
Daga ƙarshe ta rinƙa yi musu selfi su duka huɗu.
Saida suka gajine kana suka zauna suna hira.
Nan suka kira Umaymah suka sha hira.
Suna cikin hira Ummi ta juyo da sauri jin muryar Affan yana sallama tare da cewa.
“Assalamu alaikum. Ina Umminmu ina amaryar Hamma tuzuru”.
Miƙewa da sauri Ummi da Aunty Juwairiyya sukayi tare da cewa.
“La Affan yaushe ka dawo”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Jiya da tsakiyar dare, ina Auntyn nawa”.
Ya ƙarishe mgnar yana shigowa cikin tsakiyar falon.
Tafa hannu Ummi tayi tare da cewa.
“Suwa nake gani kamar Yusuf da Aryan”.
Cikin dariya sukace.
“Muɗin ne dai Ummi”.
Cike da jin daɗi Ummi da Aunty Juwairiyya ke cewa.
“Kai maraba lale lallai yau munada manyan baƙi , oh duniya Yusuf da Aryan kamar ba kuba”.
Dariya sukayi tare da zama a kujeru.
Hibba kuwa tuni ta isa gaban Affan lakace hancinta yayi tare da cewa.
“Sakaliyar Umaymah ashe kina nan bana zakiga shagalin sallan Masarautar Joɗa”.
Cikin sauri ya kalli Shatu dake ce musu.
“Sannunku da zuwa”.
Da sauri ya juyo ya kalli Ummi kana ya kalli Aunty Juwairiyya tare da cewa.
“Wannan ce Auntyn nawa amaryar Sheykh Ustaz Malam Dr Jabeer akarmakallu”.
Murmushi Ummi tai tare da cewa.
“Eh itace”.
Cikin dariya ya kalli Yusuf da Aryan da suke gaisawa da ita yace.
“Kan bala’i ashe dama Sheykh Hamma Jabeer yana kallon mata kalli yadda ya zaƙulo zankaɗediyar sarauniya”.
Yusuf ne ya daki kafaɗarshi tare da cewa.
“Kaifa Affan ɗan iskane baka da mutunci, baiyi aureba kace mishi. Shugaban tuzuran Afirka.
Yanzu yayi auren kuma zakace yana kallon to dama ce maka akayi shi makaho ne?”.
Dariya sukayi baki ɗayansu,
Aryan ne yace.
“Bar Affan da shegiyar surutu”.
Dariya suka kumayi kana duk suka zauna.
Suka gaisa cikin tsokana Affan ya kalli Shatu dake danna wayarta tana kallon hotunan da sukayi yanzu yace.
“Aunty Amarya Hamman namu yana nan ne, ayi mana iso wurin shi mu kwashi gaisuwa”.
Shiru ta ɗanyi tare da kallon Ummi.
Da sauri Hibba tace.
“Eh yana nan yanzu ya shiga”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“To Aunty Sayyada ayi mana sallama dashi ace ɗaliban shi ne, Affan, Yusuf, Arya,”.
Cikin tsoron kada Shatu ta kuma zuwa ɗakin abun da ya faru jiya ya sake faruwa Ummi tace.
“Ai yana bacci ne yanzu ko”.
Da sauri Affan yace.
“No ba matsala in ance masa Yusuf ne, tashi kice muna sallama dashi.”
Cikin murmushin jin Yusuf da Aryan sunce.
“Eh gsky gwara mu gaidashi kada ya gammu a wurin sukuwa yace bamu nemi izininshi ba”.
A hankali tace.
“To bari a gaya mishi”.
Ta yunƙura zata tashine Ummi ta riƙe hannunta tare da cewa.
“Shatu kadafa”.
A hankali tacewa Ummi.
“Ba komai fa Ummi”.
Ganin hakane yasa Ummi ta sake mata hannun tare da cewa.
“To Allah yasa”.
Amin Amin Juwairiyya da Hibba sukace.
Shi kuwa Affan cewa yayi.
“Allah bazaiyi faɗaba in yaji mune”.
Kai Ummi ta gyaɗa sabida basu san me take tsoron ba.
Ita kuwa Shatu a hankali ta nufi Side ɗinsa.
Su kuwa hirarnsu sukaci gaba dayi a falon.
A hankali ta tura ƙofar falon nashi ta shiga.
Shiru babu kowa babu komai sai sautin ac dake tashi fuuuhhh.
A hankali ta lumshe idonta kana cikin sanyi ta nufi ƙofar ɗakin nashi.
Tare da cewa.
“Salamu alaikum! Salamu alaikum!! Salamu alaikum!!!”.
Shiru babu motsin komai, hakane yasa a hankali tasa hannun hagun ta dafa ƙirjinta dake bugawa.
Kana tasa hannun damanta ta tura ƙofar Bedroom ɗin.
Sai kuma gashi ta buɗu ƙofar.
Wani sassanyan ajiyan zuciya ta sauƙe jin wani irin masifeffen ƙamshi da sanyi daya ratsa mata jiki da zuciya.
Sallama ta kumayi shiru ba amsa.
A hankali ta cusa kanta cikin ɗakinta da yake duhu.