
Wani irin bugawa ƙirjinta keyi kana.
Kanta na sarawa da masifan ƙarfi.
A hankali ta juya gefen mashigar ɗakin hannun tasa ta lalubi abin kuna wutan ɗakin danna ɗaya daga ciki tayi,
hakan yasa ƙoyin wutan ɗaya mai kalar Sky blue ya kawo wuta.
Sanadin hakane ɗakin ya kawo wani irin haske mai ƙayatarwa.
Yanayin wutan ɗakin labulayen da kayan jikinta dana jikinshi sukazo iri ɗaya.
Juye- juye tayi tare da cewa.
“To ina yak”.
Shiru tayi bata ƙarisa rogowar mgnar ba hangoshi can ƙasa yana konce rigingine yayi pillow’n da tafukan hannunshin.
A hankali tayi taku uku zuwa biyar ta matso kusa dashi cikin sanyin da ya fara yimata yawa ga cikinta dake tsuma a hankali tace.
“Salamu alaikum”.
Ko motsi baiyiba bare tayi zaton zai amsa.
Sallama ta kumayi shiru ba amsa.
Ganin hakane ta matso a hankali take takun saɗab-saɗab take taka sawunta a hankali har ta isa kusa dashi.
Da sauri ta zubawa ƙafar damanshi ido.
Ajiyan zuciya tayi mai sanyi tare da mgnar zuciya.
“Uhumm ashe dama yana komciya a ƙasa haka babu shimfiɗan komai ba pillow, da kuma ƙaramar riga da wondo iya guiwa.”
A hankali ta iso gab da kanshi,
Cikin yin numfashi a hankali wai karya jita, ta rusuna ta zauna bisa sawunta irin zaman yin tahiyan salla.
Cikin ƙurawa babbar yatsar ƙafar damanshi inda ta rinƙa biyo wannan zanen macijin dake kwance lib a ƙafarshi.
Da ido tabi zanen har kan guiwarshi inda iya nan wondon 3 qtr ya rufe.
A hankali ta ƙara sunkuyowa ta kurawa wurin ido, tare da mgnar zuciya.
“To iya ina wannan zanen tafiyar macijin ya tsaya ne a jikinshi?”.
Jim kaɗan tayi kana a hankali.
Ta miƙa hannunta, cikin sanɗa a hankali hankali tasa yatsunta biyu ta kamo bakin ƙafan wonɗon ta ɗan jawoshi a hankali tayi sama das…!
Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 in Kuma special Group kikeso wanda a mako biyu ake gaba part 1 kuma abiyu za’a gama Part two da izinin Ubangiji yimin TRANSFER ɗin 1k ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. sai ki turo screenshot shaidar biyanki ta wannan number 09097853276.
By
*GARKUWAR FULANI*
Ta ɗan ja tayi sama da bakin ƙafan wonɗon wanda yake na robane bakin a tsuke yake.
Da sauri cikin tsoro da rawan jiki ta saki robar.
Pat ya fetti a jikinshi.
Ganin ya motsa.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani sassanyan numfashi ya ja mai tsawo tare da fesoshi a hankali kana, ya mirgina a hankali ya juya ya kifu cikin kasalan nauyin bacci ya ɗaura kanshi bisa cinyarta,
Kana ya ware hannayenshi da sukayi ɗan tsami sabida pillow’n da yayi dasu.
Ware hannayen yayi tare da miƙarar dasu.
Ya zama tana tsakiyar hannunshi kana kanshi na kan cinyoyinta.
Haɗe hannuyen nashi yayi ya sarƙafe yatsunshi wuri ɗaya, ya zama ya zagayeta tako ina yayi mata ƙawanya.
Ya cusa hancinsa cikin mayafinta yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinta dana kayanta.
A hankali ya kuma gyara kwanciyarshi da kyau kana yaci gaba da sauƙe sassauƙan numfashin.
Ita kuwa Shatu wani masifeffen tsalle da bugu zuciyarta keyi tamkar zaiyi tsalle ya fito woje.
Gaba ɗaya ida nunta kan sumar kanshi ta zubasu.
Tare da kallon tattausan sajenshi dake kwance lib-lib a gefen fuskarshi.
Wani sassanyan numfashi ta sauƙe tare da lumshe idonta cikin zuciyarta tace.
“Allah shi ƙara”.
Sai kuma tayi sauri ta buɗe idonta tana tambayar kanta.
“Allah shi ƙara me ɗin? Ya ƙara ruggumata ko meyeye”.
Cikin kauda zancen a ranta ta ɗan muskuta dan janye jikinta. Amman sai ta ji ya riƙeta gam-gam, yana ƙara cusa kanshi cikin jikinta yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren jikinta.
Cikin tsoro murya na rawa a hankali tace.
“Yah Sheykh!”.
Karab sautin muryarta ya ratsa kunnuwanshi.
Sai dai ko motsi baiyi ba,
A hankali ta kuma ce.
“Yah Sheykh! Yah Sheykh!!”.
Shiru babu amsa sai numfashin da yake fiddawa a hankali yana kuma shaƙan ƙamshin jikinta.
Cikin sanyi ta ɗan ɗago hannunta a hankali tasa taffin tattausan hannunta, ta ɗan rinƙa buge gefen fuskarshi a hankali a hankali tanayi tana cewa.
“Yah Sheykh! Yah Sheykh! ! Tashi wai Affan dasu Yusuf sunzo, shine Affan yace inzo in tasheka”.
A hankali ya buɗe idonshi,
Yanayin yadda take ɗan marin gefen fuskarshi da hannunta wanda ke ɗaure da agogo.
A hankali ya ɗago hannunshi ya ɗan kan hannunta ya kamoshi ya riƙe, cikin tsoro ta fara kiciniyar kwace hannunta,
Sai kuma tayi zuru, jin ya ja hannun da ɗan ƙarfi ya kawoshi dai-dai saitin fuskarshi.
Idonshi ya zubawa yatsun hannunta da kullum in ya gansu da jan lalle yake tuna mishi baya.
Da sauri tace.
“Wash Allah na”.
Jin ya murɗa hannun ya juyo da fuskar agogon inda zai gani.
Ƙarfe biyu da miti arba’in da ɗaya.
Du-du baccin 40 minutes yayi tazo ta tasheshi.
“Harda zuba min maruka”.
Ya faɗa a ransa.
Ita kuwa kan tattausan suman ta ajiye sinsiyar hannunta.
tana jin kanta na sara Especially in ta kalli saitin ƙasan gadonshi.”
A hankali ya sake hannunta kana ya yunƙura ya juya rigingine,
ya fuskanci sama, ita kuma tana zaune tana kallon ƙasa hakanne yasa suna fuskantar juna, cikin wani irin yanayi ya zuba mata ido na wasu sakanni.
Shigarta tayi masifar mishi kyau. Kodan tasa kalan kayan da yafi sone.
Cikin muryar bacci yace.
“Shine harda dukana? Meyasa ne ku mutanen garincan kuke son dukan mutun da kallon jikinsa?”.
Cikin tura baki tace.
“Cinyana, nagaji kanka nauyi”.
Bai janye idonshi a kantaba ya yunƙura ya tashi zaune tare da juyowa ya fuskanceta.
tanƙwashe sawunshi yayi tare da cewa.
“Me zaki kalla a jikina? Woto Kin zama kamar ɓarauniya ko? Me kike son gani? Wani abu kike sone?”.
Cikin tura baki tace.
“Nifa tada kai a bacci kawai nayi”.
Hannunshi yasa ya riƙo hannunta, yatsunta ya zubawa ido, cikin wata murya mai sanyi yace.
“Masha Allah, kinyi kyau.”
Wani irin sanyi taji kalmar tashi tasa mata a ranta, ido ta ɗan ɗago ta kalleshi.
Shima ita yake kallo, ido ya lumshe jin sautin zazzaƙar muryarta a hankali tace.
“Nagode”.
Tonƙoshe kansa yayi bisa kafaɗa kana hankali ya sake hannun nata.
Fuskarta ya kalla tare da taɓe baki yace.
“Waya koya miki irin sa lalle Mammeyyyyy nah!? Dan tafi ko wacce mace iya lalle”.
Cikin sanyi da nazartar yadda ya kira sunan Mammeyyyyy da yadda lokacin ɗaya idonshi suka fara sheƙin tsastsafo da zafafan hawayen da ba zubowa zasuyiba.
Cikin son gano meke cikin zuciyarsa tace.
“Ummeyy nah ce ta koya min tun ina ƙaramar”.
Yatsunta ya jujjuya kana ya miƙe tsaye.
A hankali ya juya ya nufi bathroom sabida baya son ta hango wutar ƙunar dake ransa.
Ita kuma binshi da ido tayi,
tare da langoɓar da kanta tana kallon sharabansa da gargasa yayi musu ƙawanya.
A haka ta shiga wani nazarin tana mai maimaita sunan da taji ya kira da cikekken so shaƙuwa ƙauna tausayi rauni shogoba Mammeyyyyy. Ta maimaita sunan a fili.
Shi kuwa Sheykh Jabeer al’wala yayi kana ya fito.
Yayi mamakin ganinta a zaune bata fita ba.
Hararanta yayi ganin yadda taketa kallonshi. Jallabiyar shi ya zura, kana yasa al’kyabbar, tare da sa Hiraminshi.
Sannan ya fesa turare.
Duk inda yayi tana binshi da ido.
Wayarshi da yafi yawan riƙewa ya ɗauka ya zura a al’jihunsa.
Sannan ya nufi bakin ƙofa inda takalminshi suke yana cewa.
“Wannan kallon maitan fa”.
Da sauri ta janye idonta.
Cikin daƙilewa yace.
“Kada ki cinyeni da ido fa. Bana son kallo, ko kina bina bashine?.”
a hankali ta miƙe tare da lumshe ido ta biyu bayanshi.
Tana gyara mayafinta tare da cewa.
“Ni ban kalleka ba”.
“Uhummm.” yace a taƙaice.
Kusan a tare suka fito.
Yana gaba tana bayanshi,
Suka fito tsakiyar falonshi.
Tsayawa ya ɗanyi ya gyara masaƙalin Al’kyabbar tashi.
Shiyasa ya zama a jere suke tafiya tana gefen damanshi.
A haka suka fito cikin corridor’n.
Suka doshi Falon cikin kwarjini da dacewa da juna sai ƙamshi da sheƙi zallan kyau sukeyi.