GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Da Sallama a bakinshi suka kutsa kai cikin falon.
Wani irin dariyar jin daɗi Affan da suke can Dinning area yayi, suna cin abinci da Ummi ta matsa suci.
Wani irin murmushi Yusuf da Aryan ma sukayi tare da miƙewa suka nufi inda uban gidan nasu ke tsaye da kekyawar tauraruwarshi mai haskawa.
Affan kuwa wayarshi ya zaro yana kekkebta musu hoto tare da cewa.
“Ga amarya, ga ango, suna carabki da zallan kyau da ƙamshi”.

Murmushi sukayi dukansu, ita kuwa Shatu tana tsaye gefenshi.

A haka su Affan suka iso.
Suna Isa Affan ya ruggumeshi shima Sheykh ruggumeshi yayi tare da make ƙeyarsa.
Da sauri ya janye kanshi tare da cewa.
“Wayyo Allah na yanzu Hamma Jabeer na girma harda yaran nawama ban wuce dukaba”.
Murmushi yayi tare da, Ruggume Yusuf da Aryan Allah ya sani yana masifar son yaran nan har gobe bashi da ɗalibai sama dasu yana sonsu so na musamman, duk sanda ya gansu yakan tuna ƙuruciyarsu tun suna yan shekara goma sha biyar-biyar yake tare dasu shi ya horas dasu.
Yana tura irin tarin ƙalubale da suka fuskanta a gasar Polo da kuma irin nasarorin da suka samu Especially Yusuf nashi yana tuna yadda yaran suke sheƙiyanci in sun haɗu, yana jinsu tamkar su Jamil.

Cikin murmushin ya shafa kansu tare da cewa.
“Sannunku da zuwa”.
Cikin jin daɗi sukace to.

Bisa kujera ya zauna su kuma suka zauna a ƙasa a gabanshi kan carpet.

Ita kuwa Shatu a hankali ta juya ta nufi kitchen ganin Ummi ta nufi can.
Hibba kuwa na gefensu tana gayawa su Jalal ga Ya Affan fa.

Da gefen idonshi ya bita da kallo.
Har ta ɓacewa ganinsa, Allah ya sani yana son abu blue baya iya cire idonshi kan abu mai kalar shiyasa yake jin baya gajiya da ganinta, da zai samu kada tayi nesa dashi, dan tayi mishi kyau sosai farar fatarta ta fito fes kamar balarabiya ji yake tamkar ya bita duk inda tayi.

Cikin murmushin ya kalli Aryan yace.
“Aryan Ina su Yusuf ƙaramin”.

“Alhamdulillah suna lfy Malam”.

Kai ya jinjina tare da cewa.
“Masha Allah”.
Sai ya kuma kalli Yusuf yace.
“Ina mai sunana baka zomin da shiba”.
Murmushi Yusuf yayi tare da cewa.
“Malam baka tambayi Aryan ƙaramin ba da yakeso ya zama kamarka sai ka tambayi mai sunanka”.
Dariya sukayi kana yace.
“Ayyah my Aryan, sun kusa tafiya ai in sha Allah Jami’atul Madina zaiyi karatunshi”.
Da sauri suka juyo suka kalli Jalal da Jamil da suka shigo da sauri.
Ruggume Affan sukayi suna cewa.
“Oyoyo ya Affan”.
Hannu ya basu suka tafa kamar sa’ao’,insa ne su.
Cikin dariya yace.
“Tun ɗazu nake kiranku bakwa ɗagawa.
Nace waɗannan ana can cikin hayani “.
Murmushi Jamil yayi tare da miƙawa Yusuf hannu wanda ke cewa.
“Oh wato Affan kawai kuka gani mu ko oho ko”.
Cikin ɗan sakin fuska Jalal yace.
“Afwan Hamma Yusuf ya Aunty Zahra da Mama”.
“Suna lfy. Sun gaidaku”. yace tare da bashi hannun.

Kana suka gaisa da Aryan.
Sannan suka miƙe sukace bari suje wurin Aunty Mami.
Cikin dariya Affan yace.
“Eh kujema kuzo da ita taga matar babban yaya”.
Da sauri Jamil yace.
“A a ka kawota da kanka dai”.
Ya ƙarshe mgnar suna fita.

Su kuwa cikin yin ƙasa da kai Yusuf yace.
“Uhum dama Malam zamu ɗan shiga wasan daba ne in batsala”.
Murmushi mai faɗin Sheykh yayi tare da cewa.
“Wato ku dai har yanzu baku girma da batun doki ba”.
Shiru sukayi sai Affan ne yace.
“Tab Yusuf kuma da in ya ga doki bai hauba jikinshi har rawa yakeyi”.
Murmushi Sheykh yayi kana yace.
“To muje muyi salla. Tukun tunda sai anyi sallan la’asar za’a fara ko”.
To sukace tare da miƙa ganin ya miƙa dan tuni uku da kwata ta wuce.
Affan ne ya kira Ummi tare da cewa suzo zasu tafi.
A tare suka fito kitchen.
Sabbin kuɗi rafa yan dubu-dubu Yusuf ya miƙawa Hibba ƙulli ɗaya dubu ɗari kenan yace.
“Gashi miƙa wa Ummi ta raba muku.”
Affan ma ya basu.
Hakama Aryan.
Hibba sai tsalle take tana cewa.
“Yessss my brother’s Allah ya ƙara buɗi Amin Amin sukace kana suka juya zasu fita.
Cikin tsare girma Shatu tace.
“Mun gode, a gaida gida”.
Gida zaiji sukace kana suka fita suka tafi.

Suma su Ummi wucewa sukayi yin al’wala.

Ana idar da salla kuwa aka fara hawan daba, hawan sarki dama duk sauran shagulgula na gidajen masarautun gargaji yayin wurin taron bikin salla.
MASARAUTAR Joɗa ta cika tayi maƙil da bani Adam.

Haka dai akayi taron lfy aka tashi lfy sai kuma gobe in Allah ya kai rai.

Washe garin ranar da sassafe.
Sheykh ya tafi asibitinshi.
Ko karyawa baiba.
Sai kusan sha ɗaya ya dawo da alamun yunwa da gajiya tare dashi.
A falon ya zauna suna gaisawa da Ummi dan basu gaisaba ya tafi daga masallacin can ya wuce.
Ummi kuwa tasa Shatu ta kai mishi breakfast ɗin shi da yanzu kam in yacima ya zama lunch ne.

Hibba kuwa na can ɗauki tana ƙenƙesa ado.

Cikin isa da ƙasaita Gimbiya Saudatu ta shigo tsakiyar falon babu ko sallama.
Haɗe fuska Sheykh yayi tare da cewa.
“Wannan banzan ɗabi’a na arnatakun baya, dan ko arna yanzu suna cewa konkon, mutun kamar shanu ko mahaukaciya”.
Cikin isa ta iso tsakiyar falon.
Dai-dai lokacin kuma Shatu ta fito falonshi.
Cikin shigar doguwar riga mai ruɓi biyu.
Kanta ta ɗago ta kalli Shatu kana ta kalleshi cikin yin dariyar mugunta tace.
“Eh kam tabbas tunda ka auro mahaukaciya dole kasan hali da ɗabi’un mahaukata ai.
Zuwa gaba kaɗan kaima zaka fara ihu da kuka da sume-sume irin na wannan al’janar fulanin daji daka auro ɗin”.
Cikin tarin mamaki Ummi ta kalli Shatu ta kuma kalli Hibba da yanzu ta fito, cike da al’hinin ta yaya taji wannan batun ya fasa Masarautar Joɗa yes in dai Gimbiya Saudatu taji to ai shike nan kowa ma zaiji.

Shi kuwa Sheykh ba gane inda soki burutsunta ya nufaba yayi.
Ita kuwa cikin watsa musu kallon ku sakarkaru ne tace.
“Kuna mamakin ta ina naji, cewar ji shekaran jiya iwar haka dai wannan matar tashin tana yashe a sume da ido a wulkice tana ƙarkarwa farfaɗiya kamar mazari ne.
To ai Ni duk wanda yaci tuwo dani miya yasha.
Inada tawa a cikinku duk motsinku ina dashi a tafin hannuna.
Nan gaba kaɗan zamu samu riƙeƙƙiyar mahaukaciya a masarautar Joɗa”.

Cikin tsuke fuskarsa yace.
“Yanzu ma ai muna da su mahauka ta kam, ke ɗin me banbancin ki da zararrun”.
Shiru yayi ganin yadda Shatu keyin taku a hankali cikin isa ta nufi gaban Gimbiya Saudatu.
Ummi da Hibba kuwa miƙewa tsaye sukayi.

Shi kuwa Sheykh gyara zamanshi yayi tare da ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya.

Ita kuwa Shatu a hankali ta isa gabanta.
Ido ta zuba mata tare da yi mata kallon tara saura kwata.
Cikin dakkeyar Muryar rashin tsoro tace.
“Toh Bushiya mai mugun baya, Bushiya mai bayan ƙayoyi masu kama da allurai, ki buɗe idonki da kyau ki kalleni Ni AYSHA ALIYU GARKUWA ba sa’ar yinki bace uwar mahassadan duniya, in kina cin ƙasa to tabbas ki kiyayi ta curi, ki bar min mijina ya sarara ki far masa rayuwa, ɗan shi ba sa’an yinki bane ki bar min mijina ya huta baya son ihun nan da kikeyi mishi, zan kuma iyan komai dan ganin na kauda dukkan abinda baya so.”
Wani irin daɗi ne ya rufe zuciyar Ummi da Hibba Sheykh kuwa ƙafarshi kawai yake kaɗawa yana mai binta da wani irin kallo mai tarin ma’anoni kalmarta ta Mijina yake ji tana sa duk wani hudan gashin jikinsa na amsa amon kalmar yana ratsa jikinshi da zuciyarsa haka yasa bai san sanda wani yalwataccen murmushi ya subce mishiba, tabbas Shatu akwai ƙarfin hali.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu tsuru tai da ido.
Itako Aysha cikin karsashi tace.
“Na lura ke dabbace, sam bakya gane yarukan mgna na bani Adam, kinfi son sai an miki irin yarukanku na dabbobi.
Kina tsaye da farin yawu a bakinki kina zubda jini.
Yayinda wasu ke bayanki da jini a bakinsu suna fidda farin yawu.
Sokuwar rama mai tsami.
Ni nan da kike ganina da idona tar a buɗe na shigo Masarautar Joɗa, kada ki ganni haka Ni ɗan hakine da zaki iya renawa amman tabbas zan tsole idanun magauta ruwanshi ya tsiyaye.
In kin san fullanci to.
MIN MI KURORI CITTA NFAMƊA NHEYAH NI DAKKEN YAJIN BORKONE INYI KAƊAN IN KUMA ISHI MUTUN
Ki tsumayeni tabbas zanyi daka inyi tankaɗe inyi rairaya a masarautar Joɗa!.
Ke ko kallo baki isheni ba domin bata ke akeyi ba da manyan Magauta nakeyi.
Ja mugun bakinki ki fice min a gidana!”.
Rab-Rab.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button