GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Jalal da Jamil dake da Jafar shigowa ne, suka tafa mata da hannu bibbiyu.
Hakama Hibba. Ummi kuwa ƙasa tayi da kanta.
Shi kuwa Sheykh ƙanƙance idonsa yayi yana kallonsu yana kaɗa ƙafa ya watsa idanunshi cikin na Gimbiya Saudatu yana mata kallon itama ta isheki.
Aunty Juwairiyya kuma da tun ɗazu tana bakin ƙofar shigowa da sauri ta juya ta koma Side ɗin ta.

Ya Jafar kuwa sai murmushi yake tare da dunƙulawa Shatu hannunshi kamar haka????????

Wani irin juyawa Gimbiya Saudatu tayi tare da jan al’kyabbar ta ta fita.
Har taje bakin ƙofa Shatu tace.
“Ki riƙe kalmar mahaukaciya tabbas zakiga mahaukata a masarautar Joɗa zasu baiyana bila’adadin.”

Daga nan ta juya ta nufi Dinning area ɗin babban falon.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu ta juya ta fita.

Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya sauƙe ƙafafunshi kana ya miƙa ya nufi falonshi.
Haka nan yaji murmushi na tsubce mishi.
Tabbas ya gamsu da ƙarfin halin Shatu da rashin tsoronta, sai dai yana jiye mata tuggun mutanen da bata san halinsu ba.
Yana shiga yaci abinci kana ya shiga yayi wonka.
Kana ya ɗauki wayarsa.

Jalal, Jamil, Hibba, Ya Jafar, Shatu kuwa zama sukayi a falon cikin mamaki Ummi tace.
“To wacece yar leƙen asirin Gimbiya Saudatu a wannan sashin?
Ya akayi tasan abinda ya faru da Shatu?
Waya gaya mata?
Bayan in banda muyamu.
Ni Juwairiyya, Hibba, Jalal, Jamil, Jafar. Wanda shi baya mgna, ita kanta Shatu bata san meya faruba batasan ya akayi ba.
To waya fitar da wannan zancen a cikinmu?.”

Cikin gsky da gsky duk suka ce wlh babu wanda suka taɗawa mgnar Hibba harda ƙollarta tace.
“Wlh ita ko Umaymah ma bata gayawa ba”.
To lallai kam akwai buƙatar bincike a tsakanin mu.”
Ummi ta faɗa tana mai cike da al’hinin abin.
Ita kuwa Shatu uhummm. Kawai ta iya cewa tayi shiru bata ce komaiba.

Haka dai suka tashi taron.

Sheykh kuwa, number Umaymah ya kira bayan sun gaisa ne yace.
“Uhumm Umaymah wai me kika sani ne ya faru da wannan yariyar shekaran jiya?”.

Cikin tsoro da son kauda batun Umaymah tace.
“Wacce yarinyar kuma?”.
Fuska ya ɗan tsuke yace.
“Waccar yarinyar dai”.

“To bata da sunane ita”.
Ta kuma ce mishi.

Cikin gajiya da batun yace.
“To ni ba sanin sunanta nayiba, baku gaya min sunanta ba.”
Wani irin murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“Ban gane bafa Jazlaan”.
Hannunshi yasa ya ɗan shafi sajenshi.
Yana mai son yasan meya sameta, meya faru da ita, shiyasa a hankali yace.
“Yarinyar dai da kike cewa ɗiyarki!.”
Kai Umaymah ta jinjina tare da cewa.
“Laah ni nama mance bamuyi mgnarba, ran sallane tayi aiki ta gaji tunda safe bataci komaiba to ashe tanada olsa shine fa, ta shiga ɗakinka zatayi maka shara ta faɗi ta suma, da kyar aka samu ta farfaɗo suanta kuma Aysha”.
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
“Shirme in banda sakarci da raki mutun ya bar kansa da yunwa da gajiyan aiki mutun har ya suma”. Ya ƙarashe mgnar yana jinjina darajar sunanta a ranshi.
Cikin jin daɗin bai tsananta bincike ba tace.
“Akwai wani abune?”.
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“Wannan mahaukaciyar Gimbiya Saudatunce tazo take cewa wai taji lbrin ta haukace”.
Daga nan ya kauda zancen.
A hankali ya miƙe yana riƙe da wayar a kunne shi.
Dinning area ya nufa.
Murmushi yayi gano tabbas akwai abinda Umaymah ke ɓoye mishi.
Hannunshi yasa cikin zirin zirin igiyoyi masu duwatsu masu daraja sheƙin Daimond da sukayi Dinning area ɗinshi a madadin labule.
A hankali yasa hannunshin kan na’urar CCTV camera dake liƙe a gefen inda yake ajiye key, wanda duk abinda za’ayi a falon zai gani.
Cikin sanyi yace.
“Uhummm Umaymah kiyi mata faɗafa, ta dena hawan ƙawara kan mutanen masarautar Joɗa, ta kiyayi kanta da faɗa da magautana zasu ilatata.
Bata san komaiba a kaina ta tsaya matsayin baƙuwa Umaymah zafa suyi mata illa”.
Ya ƙare mgnar a hankali.
System ɗinshi dake kan Dinning table ɗin ya jawo.
kana yaja kujera ya zauna ya fara haɗa na’urar.
Ita kuwa Umaymah a hankali tace.
“To ya zatayi tunda ƙaddara ta kasantar da ita matsayin matarka, ko ita kurmace dole sai sun nemi yi mata illa sun sabautata.
Dole kasata cikin jerin mutanen da ka zame musu GARKUWA a masarautar Joɗa, tunda ita dai matarka ce, amanarka kuma”.
Shiru yayi yana jinta yana mai kallon fuskar System ɗinshi date ɗin shekaran jiya ya shiga.
ai kuwa Shatu ya fara cin karo da ita tana share falon da goge ko ina.
Sai kuma lokacin da suka shigo ita da Jamil da Hibba suka nufi bedroom ɗin sa.
A hankali yace.
“Uhmmm Umaymah sai anjima zan kiraki”.
To tace kana ya katse kiran.
Ido ya zuwa System ɗinshi.
tsaki yaja karo na forko da yaji da ya haɗa na’urar da cikin ɗakinshi.
Gashi yanzu baya ganinsu sai dai ihun Hibba, da fitowa da tayi da gudu ta kira Ummi da yadda suka shigo da Aunty Juwairiyya.
Kanshi ya gyaɗa lokacin da yaga sun fito a hankali ya rufe System ɗinshi.
Dafe kanshi yayi yana nazari.
Ya dade a nan sosai kana ya koma ɗakin shi.

Da dare misalin karfe sha ɗaya na dare saura.
Shatu ta kalli Hibba dake konce tuni tayi bacci.
Yasa ta miƙa a hankali ta nufi ɗakin Ummi.

A bakin ƙofar ta tsaya a hankali tayi sallama.
Cikin mamaki Ummi dake zaune bisa sallaya ta idar da shafa’i da wutri kenan taji sallamarta.
Juyowa tayi tare da amsawa tace.
“Shatu”.
A hankali tace.
“Na’am Ummi”.
Cikin mamaki tace.
“Lfy kuwa shigo mana”.
A hankali ta shigo tare da cewa.
“Lfy lau Ummi, nazo wurinki ne.”
“To”.
tace tare da nuna mata wurin zama bakin gadonta.

A hankali ta ƙaraso kusa da ita,
Gabanta ta zauna kan sallayan cikin nitsuwa tace.
“Ummi kiyi haƙuri ko zakiyi bacci na hanaki”.
Da sauri ta girgiza mata kai alamar a a.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“To Alhamdulillah”.
Sai kuma tayi shiru.
A hankali Ummi tace.
“Kina buƙatar wani abune?”.
Cikin nitsuwa tace.
“Uhum Ummi dama tambayarki nake son yi”.
Gyara zama Ummi tayi kana tace.
“Ina jinki”.
Itama zamanta ta gyara a hankali tace.
“Dan Allah Ummi in ba damuwa, dan Allah da Manzonsa ki sanar dani abinda Allah ya sanar dake a kan masarautar Joɗa mana.
Ummi kaina na kullewa da mutanen masarautar Joɗa, ban gane banbanci su da dankantakarsu da kuma. Alaƙarsu ba”.
Wani irin dogon ajiyan zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.
“To Shatu ai kin gama komai tunda kika haɗani da Allah da Manzonsa.
Kuma dama nace miki ki tambayeni duk abinda baki gane ba, zan gaya miki. To amman akwai wani abun sirrine garesu masarautar in na faɗa kamar cin amarsu ne, wani abun kuma nima kaina ban sanshi ba.
Hannun Ummi ta riƙe tare da zubda hawaye tace.
“Ummi gaya min yadda masarautar Joɗa take ko zan san irin zama da takun da zanyi da mutane da ɗaukar mataki kan abinda ke faruwa”.

A hankali Ummi ta gyara zamanta.
Ta jingina da jikin gado.
Kana itama Shatu ta gyara zamanta ya zama suna fuskantar juna da kyau.
Cikin sanyi Ummi ta fara bata lbrin.

         *Masarautar Joɗa*

tsohuwar masarautace.
wacce tun kafin zuwan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ƙasashen Afrika tana kafe da ƙafanta.
Kuma masarautar Fulɓe ce tun a wancan lokacin.

Lokacin da Shehu Usman Ɗanfodiyi ya iso nan ƙasashen hausa ya basu musulunci ya kafa tutocinsa tako ina tako wacce masarauta.
A lokacin Masarautar Joɗa sunanta masarautar Fulɓe.

Kuma lokacin Sarki Sule ne a kan karagar mulki. Baban Joɗa kenan wanda yake shi Joɗa shine kakan sarkinmu na yanzu wato Lamiɗo.

A lokacin sarki Sule yanada ƙarfin mulki yana da mata huɗu ƙwar-ƙwara biyar.
Allah ya azurtashi da arzikin yara a ƙalla sunfi hamsin a cikin matansa huɗu na aure.
Akwai wata ɗaya da ake kira Gimbiya sumaye ƴar sarkin kal’anace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button