GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Gimbiya Sumaye inrin matannane da Allah ke jarabta da haihuwar wabi.
Bima’ana tana haihuwa kuma yaran na rasuwa.
A haka har ta haifi yara kusa goma kuma bata da rayeyye ko ɗaya.
Cikin ƙwar-ƙwaran sarki Sule ne ɗaya ta ɗauki ɗanta na miji ta bata halak malak kwanan yaron uku a hannunta ya rasu.
Wata cikinsu ta kuma bata still shima kwananshi uku ya rasu.
A haka duk ƙwar-ƙwaran sarki Sule saida suka bata yara suna rasuwa.
Daga nan uwar gidan Sarki Sule wacce take babarbariya ce.
Tasa mata suna cikin wasa na tsakanin Fulani da bare-bari amman a zahiri da gaske takeyi.
Gsky mai tafiya da wasa kenan.
Sai ta sawa Gimbiya Sumaye suna da fillanci wai
Ɓadamaya ma’ana wai duk wanda ya matso kusa da ita zai mutu, ko wanda ya bata riƙon ɗa kowa kwana uku ne mutuwa zaiyi.
Kamar da wasa sunanta ya zama Gimbiya Ɓadamaya.
Mutanen masarautar akayi ta mata izgili da habaici.
Takan zauna tayi ta kuka.
babu mai rarrashi dan ita masarautarsu nada nisa a lokacin kuma babu ko Radio bare waya.

Anan Allah ya bata wani ciki ta haifi ɗan ta namiji.
Akasa mishi suna Umar faruq.
Sai Gimbiya Sumaye take kiranshi da Joɗa ma’anar Joɗa shine zauna.
Da haka sai aka maida abun ba’a aka rinƙa kiran yaro da Joɗa.
Allah cikin ikonsa ta yaye yaro lfy lau.
Ta kuma haihuwa na goma sha biyu.
Yariyar watanta biyar ta rasu, sai aka rinƙa mata dariya ana cewa saura Joɗa shima ya Dilli.
Wato wai saura Joɗa shima ya tafi.
Cikin ikon Allah kuwa ya raya Joɗa ya girma.
Ya zama shine ƙarami cikin ƴaƴan sarki Sule kenan.

Bayan wasu shekaru, sai Sarki Sule yace to shi zaiyi murabus, a cikin yayanshi yace zai naɗa babban ɗanshi Madu.
Ɗan Gimbiya Falmata.
Sai ko sauran ƴan uba duk suka tashi akece to sai ayi zaɓen manyan.

To akwai ɗan Madu wanda yake mai ilimin addini dana zamani sunanshi Bala, sai ya shiga cikin masu neman mulkin ya kafa hujja da cewa.
“Babanshi Madu jahiline dan haka a bashi shine ya dace da mulkar garin.
Haka kuwa akayi aka ba Bala mulkin masarautar Fulɓe.
Dole babanshi Madu wanda shine Magajin gari ya ƙaura ya bar garin.
Tunda kinga bazai yiwuba ace yana mahaifinshi ya rinƙa serving ɗan shiba da baƙinsa ba.

Haka dai Bala yayi mulki tsawon shekaru arba’in inda Joɗa kuma yake matsayin Galadima tunda ɗan tsohon sarki ne.
To shi kuma Sarki Bala sai Allah ya azirtashi da tarin ya’ya mata ɗan shi na miji daya ne,
Sadik.
Ya bawa Sadik sarautan Sardaun.
Bayan wani lokacin sai tsoro ke rufe Sarki Bala kada fa abinda ya samu babanshi ya sameshi.
Wato kar ɗanshi bai gaji mulkiba kamar yadda sarautar ta tsallake babanshi ta dawo kanshi.
To shinefa ya tura ɗan shi Sadik wuraren sauran sarakunan ƙasar, cewa zaiyi murabus zai bawa Sadik mulkin.
To dama bisa ƙaida dole sai sarakunan sun yarda.
Cikin Sa’a kuwa duk sarakunan suka yarda sukasa hatimin amincewa a takardun.
To a kan hanyar dawowanshi ne kuma Allah yayi mishi rasuwa.
Wannan abu yayi masifar tada hankalin Sarki Bala.
Da mahaifiyarsa Gimbiya Salame, da kakarsa Gimbiya Falmata.
Saboda wannan pain ɗin mutuwar ɗan nasa, shene ya tattara yaranshi mata kab ya Aurar dasu.
Harda ƴar shekara takwas duk ya kwashesu ya aurar.
Sabida wai baya son ya mutu baiga aurensu ba.
Ya musu aure ya kuma basu sarauta.
Suka zama hakimai.”

Cikin sanyi Shatu tace.
“Tirƙashi duk wannan don son mulki ne?”.

Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Uhum ai akan sarauta babu abinda ba’ayi sabida matsalar sai kowa yace shi ɗan sarkine zai gada.
Sabida in basu gadaba sarautar tabar hannunsu, Shatu Sarauta masiface a zuciyar masoyansa da zasu iya komai a kanta.”
Kai Shatu ta gyaɗa tare da cewa.
“To Ummi ina jinki”.
Gyara zama tayi tare daci gaba da cewa.
“To in takai ce miki a ƙarshe dai Joɗa shiya zama sarki wanda shine ɗan ƙaramin a ahlin Sule.

A lokacin ne kuma sunan jihar nan ya dawo Ɓadawaya sabida.
Nunawa duniya ba haka bane duniya Allah zai iya baka zai iya hanaka.
Masarautar Fulɓe kuma ta zama masarautar JOƊA.
Sabida sunan sarkin kenan.
Kuna ya zama adalin sarki mai son baƙi duk inda baƙo yazo zai wuce.
Sai Sarki Joɗa ya bashi wurin zama yace mushi Joɗa wato zauna ga wurin zama kayi kasuwanci kayi kiwo ki ciya ka ciyar kasha ka shayar.”
Shiyasa Jihar Ɓadamaya tayi zarra da tarin ƙabilu sabida son baƙi da basu muhallin zama a wancan lokacin kawai fili za’a yanka a baka ka zauna in Kai baƙone

To babban ɗan Joɗa shine Bubayero wato kakan Lamiɗo.
Bayan Joɗa ya rasune Bubayero ya hau kan karagar mulki masarautar Joɗa.
Ahlin Gimbiya Falmata kuma suna yaɗuwa suma buri da kwaɗayin sarauta na jiƙa a ransu duk burinsu suga yadda sarauta zata dawo ɗakinsu.
To koda Bubayero zaiyi murabus ya bawa ɗansa Nuruddeen mulki sai ya aurawa ɗansa yar bappan shi jikar Madu ɗanshi.
Sukayi aure aka naɗa Sarki Nuruddeen da matarsa yakura.
Bayan anyi aurene da shekara biyu.
Ya auro wata ƴar masarautar su Gimbiya Sumaye.
To itace tazo ta haifi Lamiɗo.
Ita waccar bata taɓa haihuwa ba.
To shima Lamiɗo sai ya auro yar masarautarsun Gimbiya Sumaye, wato Gimbiya Aminatu a matsayin matarsa ta biyu.
To Galadima da kike gani yanzu bappan Lamiɗo ne ɗan autan su marigayi sarki Nuruddeen.

To shi kuma Lamiɗo da aka bashi mulki sai aka aura mishi yar zuriyar Gimbiya Falmata itace uwar gida.
Ta haifi Baba Basiru da Baba Nasiru da kuma Baba Kamal da kuma babban yayansu Marigayi Auwalu. Sai Dr Aliyu shi kuwa mamanshi daban itama ta rasu su biyu ta haifa da Gimbiya Surayyah.

To Mamansu Baba Nasiru.
Yanzu haka tana raye amman ta haukace babu mai shiga Side ɗinta, sai Lamiɗo da yaranta. Duk wanda yaje sai tace zatayi duka, ita da bakinta take bayanin Abbansu Sheykh da Gimbiya Aminatu da Gimbiya Aisha tayiwa asiri ya dawo kanta.

Galadima da yaga ya tsufane kuma baida ɗa namiji da zai gajeshi shine.
Yacewa Lamiɗo ya naɗan babban ɗan shi Auwalu mijin Gimbiya Saudatu a matsayin Galadima.

To bayan ya naɗa shi da shekara biyu ne, ya rasu.
To sai ya naɗa Ya Jafar ɗin nan da kike gani a matsayin Galadiman Masarautar Joɗa.
Lokacin lafiyarsa lau yadda kikaga Sheykh haka yake da ibada addini ilimi nitsuwa tausayi.

Kwananshi goma a kan mulkin washe gari za’a naɗa shi ne, ya dawo haka babu mgna sabida wani babban ibtila’i da tashin hankalin ɗaya samemu.
Kuma a lokacin an kusa amishi aure sabida sarautar da za’a bashi.
To wannan shine babban mafarin hargitsi da kitimurmurar dake masarautar Joɗa a yanzu.
Dan ranar da Jafar ya zama haka akwai babbar masifar data fi wannan muni daya faru a masarautar Joɗa.
Shine abunda yayi masifar girgiza mutane.

Lokacin Sheykh yana saudia yana karatu a jami’atul Madina.
Hankalin Hajia Mama yayi masifar tashi tayi ta suma tana sakewa Umaymah kuwa da Sitti mutuwace kawai da basuyi ba, dan baƙin ciki da tashin hankalin ɗaya samemu.

To kuma tun daga nan sai duk magautan suka dena kiyayyarsu kansu Jafar da ƙannensa.
Koda Jabeer yayi karatunshi a can yayi digirinsa na biyu da PHD dinsa duk a can.
Wani sabon tashin hankalin da Jabeer ya dawo Lamiɗo yabashi mulkin GARKUWAn FULANI, nanfa Magauta sukace zasu mutu.
Dan ma mulkin na gefen yaya mata aka bashi shine abin ya ɗanyi sanyi.
To kuma ingiza gabar sunga ɗawisun masarautar Joɗa tayiwa Jabeer abinda sai sarki takeyiwa.

To kinji lbrin a taƙaice sai a hankali zaki gane komai in kina bin komai a hankali.”
Numfashi mai sanyi Shatu ta sauƙe tare da cewa.
“Ummi wacece Gimbiya Aisha?”.
Da sauri Ummi tace.
“Baki santaba”.
Da sauri Shatu tace.
“Toh ina take?”.
“Bata nan”. Ummi ta bata amsa a gajarce.
Da sauri Shatu tace.
“Ta rasu ne?”.
Cikin zubda hawaye Ummi tace.
“Bamu san halin da take cikiba shine babban burin Sheykh a duniya, sanin inda take”.
Cikin sanyi Shatu ta kauda waccar tambayar dan ko Ummi bata amsa mataba ita ta gane matsayin Gimbiya Aisha. Haka yasa a hankali tace.
“Allah ya baiyana ta. Ya cika mishi burinsa.”
Amin Amin Ummi tace tana sharce hawaye.
Cikin nitsuwa Shatu tace.
“To Ummi mene kuma banbancin mulkin gefen yaya mata dana maza”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button