GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Haɗe hannuyen nashi yayi ya sarƙafe yatsunshi wuri ɗaya, ya zama ya zagayeta tako ina yayi mata ƙawanya.
Ya cusa hancinsa cikin mayafinta yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinta dana kayanta.
A hankali ya kuma gyara kwanciyarshi da kyau kana yaci gaba da sauƙe sassauƙan numfashin.

Ita kuwa Shatu wani masifeffen tsalle da bugu zuciyarta keyi tamkar zaiyi tsalle ya fito woje.
Gaba ɗaya ida nunta kan sumar kanshi ta zubasu.
Tare da kallon tattausan sajenshi dake kwance lib-lib a gefen fuskarshi.

Wani sassanyan numfashi ta sauƙe tare da lumshe idonta cikin zuciyarta tace.
“Allah shi ƙara”.
Sai kuma tayi sauri ta buɗe idonta tana tambayar kanta.
“Allah shi ƙara me ɗin? Ya ƙara ruggumata ko meyeye”.
Cikin kauda zancen a ranta ta ɗan muskuta dan janye jikinta. Amman sai ta ji ya riƙeta gam-gam, yana ƙara cusa kanshi cikin jikinta yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren jikinta.

Cikin tsoro murya na rawa a hankali tace.
“Yah Sheykh!”.
Karab sautin muryarta ya ratsa kunnuwanshi.
Sai dai ko motsi baiyi ba,
A hankali ta kuma ce.
“Yah Sheykh! Yah Sheykh!!”.
Shiru babu amsa sai numfashin da yake fiddawa a hankali yana kuma shaƙan ƙamshin jikinta.
Cikin sanyi ta ɗan ɗago hannunta a hankali tasa taffin tattausan hannunta, ta ɗan rinƙa buge gefen fuskarshi a hankali a hankali tanayi tana cewa.
“Yah Sheykh! Yah Sheykh! ! Tashi wai Affan dasu Yusuf sunzo, shine Affan yace inzo in tasheka”.
A hankali ya buɗe idonshi,
Yanayin yadda take ɗan marin gefen fuskarshi da hannunta wanda ke ɗaure da agogo.
A hankali ya ɗago hannunshi ya ɗan kan hannunta ya kamoshi ya riƙe, cikin tsoro ta fara kiciniyar kwace hannunta,
Sai kuma tayi zuru, jin ya ja hannun da ɗan ƙarfi ya kawoshi dai-dai saitin fuskarshi.
Idonshi ya zubawa yatsun hannunta da kullum in ya gansu da jan lalle yake tuna mishi baya.
Da sauri tace.
“Wash Allah na”.
Jin ya murɗa hannun ya juyo da fuskar agogon inda zai gani.
Ƙarfe biyu da miti arba’in da ɗaya.
Du-du baccin 40 minutes yayi tazo ta tasheshi.

“Harda zuba min maruka”.
Ya faɗa a ransa.

Ita kuwa kan tattausan suman ta ajiye sinsiyar hannunta.
tana jin kanta na sara Especially in ta kalli saitin ƙasan gadonshi.”

A hankali ya sake hannunta kana ya yunƙura ya juya rigingine,
ya fuskanci sama, ita kuma tana zaune tana kallon ƙasa hakanne yasa suna fuskantar juna, cikin wani irin yanayi ya zuba mata ido na wasu sakanni.

Shigarta tayi masifar mishi kyau. Kodan tasa kalan kayan da yafi sone.
Cikin muryar bacci yace.
“Shine harda dukana? Meyasa ne ku mutanen garincan kuke son dukan mutun da kallon jikinsa?”.
Cikin tura baki tace.
“Cinyana, nagaji kanka nauyi”.
Bai janye idonshi a kantaba ya yunƙura ya tashi zaune tare da juyowa ya fuskanceta.
tanƙwashe sawunshi yayi tare da cewa.
“Me zaki kalla a jikina? Woto Kin zama kamar ɓarauniya ko? Me kike son gani? Wani abu kike sone?”.
Cikin tura baki tace.
“Nifa tada kai a bacci kawai nayi”.
Hannunshi yasa ya riƙo hannunta, yatsunta ya zubawa ido, cikin wata murya mai sanyi yace.
“Masha Allah, kinyi kyau.”
Wani irin sanyi taji kalmar tashi tasa mata a ranta, ido ta ɗan ɗago ta kalleshi.
Shima ita yake kallo, ido ya lumshe jin sautin zazzaƙar muryarta a hankali tace.
“Nagode”.
Tonƙoshe kansa yayi bisa kafaɗa kana hankali ya sake hannun nata.
Fuskarta ya kalla tare da taɓe baki yace.
“Waya koya miki irin sa lalle Mammeyyyyy nah!? Dan tafi ko wacce mace iya lalle”.
Cikin sanyi da nazartar yadda ya kira sunan Mammeyyyyy da yadda lokacin ɗaya idonshi suka fara sheƙin tsastsafo da zafafan hawayen da ba zubowa zasuyiba.
Cikin son gano meke cikin zuciyarsa tace.
“Ummeyy nah ce ta koya min tun ina ƙaramar”.
Yatsunta ya jujjuya kana ya miƙe tsaye.
A hankali ya juya ya nufi bathroom sabida baya son ta hango wutar ƙunar dake ransa.
Ita kuma binshi da ido tayi,
tare da langoɓar da kanta tana kallon sharabansa da gargasa yayi musu ƙawanya.

A haka ta shiga wani nazarin tana mai maimaita sunan da taji ya kira da cikekken so shaƙuwa ƙauna tausayi rauni shogoba Mammeyyyyy. Ta maimaita sunan a fili.

Shi kuwa Sheykh Jabeer al’wala yayi kana ya fito.
Yayi mamakin ganinta a zaune bata fita ba.

Hararanta yayi ganin yadda taketa kallonshi. Jallabiyar shi ya zura, kana yasa al’kyabbar, tare da sa Hiraminshi.
Sannan ya fesa turare.

Duk inda yayi tana binshi da ido.
Wayarshi da yafi yawan riƙewa ya ɗauka ya zura a al’jihunsa.

Sannan ya nufi bakin ƙofa inda takalminshi suke yana cewa.
“Wannan kallon maitan fa”.
Da sauri ta janye idonta.
Cikin daƙilewa yace.
“Kada ki cinyeni da ido fa. Bana son kallo, ko kina bina bashine?.”
a hankali ta miƙe tare da lumshe ido ta biyu bayanshi.
Tana gyara mayafinta tare da cewa.
“Ni ban kalleka ba”.
“Uhummm.” yace a taƙaice.
Kusan a tare suka fito.
Yana gaba tana bayanshi,
Suka fito tsakiyar falonshi.
Tsayawa ya ɗanyi ya gyara masaƙalin Al’kyabbar tashi.
Shiyasa ya zama a jere suke tafiya tana gefen damanshi.
A haka suka fito cikin corridor’n.
Suka doshi Falon cikin kwarjini da dacewa da juna sai ƙamshi da sheƙi zallan kyau sukeyi.

Da Sallama a bakinshi suka kutsa kai cikin falon.
Wani irin dariyar jin daɗi Affan da suke can Dinning area yayi, suna cin abinci da Ummi ta matsa suci.
Wani irin murmushi Yusuf da Aryan ma sukayi tare da miƙewa suka nufi inda uban gidan nasu ke tsaye da kekyawar tauraruwarshi mai haskawa.
Affan kuwa wayarshi ya zaro yana kekkebta musu hoto tare da cewa.
“Ga amarya, ga ango, suna carabki da zallan kyau da ƙamshi”.

Murmushi sukayi dukansu, ita kuwa Shatu tana tsaye gefenshi.

A haka su Affan suka iso.
Suna Isa Affan ya ruggumeshi shima Sheykh ruggumeshi yayi tare da make ƙeyarsa.
Da sauri ya janye kanshi tare da cewa.
“Wayyo Allah na yanzu Hamma Jabeer na girma harda yaran nawama ban wuce dukaba”.
Murmushi yayi tare da, Ruggume Yusuf da Aryan Allah ya sani yana masifar son yaran nan har gobe bashi da ɗalibai sama dasu yana sonsu so na musamman, duk sanda ya gansu yakan tuna ƙuruciyarsu tun suna yan shekara goma sha biyar-biyar yake tare dasu shi ya horas dasu.
Yana tura irin tarin ƙalubale da suka fuskanta a gasar Polo da kuma irin nasarorin da suka samu Especially Yusuf nashi yana tuna yadda yaran suke sheƙiyanci in sun haɗu, yana jinsu tamkar su Jamil.

Cikin murmushin ya shafa kansu tare da cewa.
“Sannunku da zuwa”.
Cikin jin daɗi sukace to.

Bisa kujera ya zauna su kuma suka zauna a ƙasa a gabanshi kan carpet.

Ita kuwa Shatu a hankali ta juya ta nufi kitchen ganin Ummi ta nufi can.
Hibba kuwa na gefensu tana gayawa su Jalal ga Ya Affan fa.

Da gefen idonshi ya bita da kallo.
Har ta ɓacewa ganinsa, Allah ya sani yana son abu blue baya iya cire idonshi kan abu mai kalar shiyasa yake jin baya gajiya da ganinta, da zai samu kada tayi nesa dashi, dan tayi mishi kyau sosai farar fatarta ta fito fes kamar balarabiya ji yake tamkar ya bita duk inda tayi.

Cikin murmushin ya kalli Aryan yace.
“Aryan Ina su Yusuf ƙaramin”.

“Alhamdulillah suna lfy Malam”.

Kai ya jinjina tare da cewa.
“Masha Allah”.
Sai ya kuma kalli Yusuf yace.
“Ina mai sunana baka zomin da shiba”.
Murmushi Yusuf yayi tare da cewa.
“Malam baka tambayi Aryan ƙaramin ba da yakeso ya zama kamarka sai ka tambayi mai sunanka”.
Dariya sukayi kana yace.
“Ayyah my Aryan, sun kusa tafiya ai in sha Allah Jami’atul Madina zaiyi karatunshi”.
Da sauri suka juyo suka kalli Jalal da Jamil da suka shigo da sauri.
Ruggume Affan sukayi suna cewa.
“Oyoyo ya Affan”.
Hannu ya basu suka tafa kamar sa’ao’,insa ne su.
Cikin dariya yace.
“Tun ɗazu nake kiranku bakwa ɗagawa.
Nace waɗannan ana can cikin hayani “.
Murmushi Jamil yayi tare da miƙawa Yusuf hannu wanda ke cewa.
“Oh wato Affan kawai kuka gani mu ko oho ko”.
Cikin ɗan sakin fuska Jalal yace.
“Afwan Hamma Yusuf ya Aunty Zahra da Mama”.
“Suna lfy. Sun gaidaku”. yace tare da bashi hannun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button