
Sannan duka anan sunayen dana irga miki da fari kowa zai iya yin sarki tunda daga ɗan sarki sai jikokinsa na gegen ƴaƴa maza, shiyasa su kunne biyu sukeyi a rawanunsu.
A hankali ya kalli Ummi data fito da Hijabi a jikinta ta zauna kusa da Shatu.
Tare da cewa.
“To kinji bayanin ƴaƴan ƴaƴa maza na sarki.”
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Na gane kuwa Ummi, yanzu gaya min na ƴaƴan yaran sarki mata kuma inji”.
Gyara zama Jamil yayi tare da cewa.
“To sukuma sarautar gefen yaya mata sune.
1 Madawaki
2 Garkuwa
3 Makama
4 Majidadi
4 Waziri
5 Matawalle
6 Sarkin yaki
7 Magayaki
8 Jarma
9 Talba
10 Shatima
11 Ubandoma
12 Ɗan kadai
13 Magajin gari
14 Ɗan masani
15 Barma.
Ɗan sauƙe numfashi yayi tare da ci gaba da cewa.
All of these hakimai ne wanda sukeyin kunne daya a rawunansu.
Kuma wasu a cikinsu jikokin sarki ne ta bangaren mamansu, mum dinsu ce yar sarki kamar dai mu a Masarautar su Sitti ko za’a bamu mulki iya waɗannan za’a bamu kinga baza suyi kunne biyu ba shiyasa suke kunne daya amma suma hakimai ne manya kuma yan majalissar sarki also akwai kin makers a cikinsu.
Sai dai su cikin jerinsu babu wanda zai gaji sarautar sarki kamar dai mu yanzu bazamu gaji Jadda ba da masarautar gargajiyace sai dai da yake nasu na musulcine, in Kuma a masarautar Joɗa ne sunayen da na ƙirga miki na forko cikinsu za’a iya bamu, domin yanzu GARKUWA da aka bawa Hamma Jabeer matsayinsa yafi ƙarfin hakan shiyasa Magauta basu damuba.”
Ya ƙarishe mgnar da cewa kin gane ko Aunty Shatu,
Kinga shiyasa da aka bawa Ya Jafar Galadima cikin kwana goma aka sabauta manashi.
Ana tsoron kada tarihin Sarki Bala da mahaifinshi Madu ɗan Sarki Sule ya maimaita kanshi a kan ƴaƴan ɗakinmu.
Shiyasa da aka bawa Hamma Jabeer Garkuwa mu bamu soba.
To sauƙin abin ma ɗaya ne da suga sarautar gefen ƴaƴan ƴaƴa mata aka bashi duk da shi jikan ɗan ɗan ɗansa namiji ne”.
Ajiyan numfashin tayi kana a hankali tasa hannunta ta tallaɓe habarta, cikin alamun nisan zango na tunani da nazari.
A hankali Ummi ta matso kusa da ita cikin sanyi da kuma yin ƙasa da murya tace.
“Shatu ni kuma in tambayeki wani abu mana”.
Kanta ta jujjuya a hankali ta buɗe baki tace.
“Na sani! Ummi nasan abinda zaki tambayeni! Zakimin tambaya ne kan menene yasa da na shiga ɗakin Yah Sheykh na suma na fita haiyacina, ko?”.
Ta ƙarishe mgnar wasu hawaye masu ɗumi suna kwaranyo mata a fuskarta.
Cikin sanyin jiki ganin Ummi ta gyaɗa mata kai alamar eh.
Jamil ma jiki a mace ya zuba mata ido.
Tafin hannunta tasa ta sharce hawayenta murya na rawa alamun tana son danne kukanta tace.
“Ummi ɗakin Yan Sheykh ɗakine mai cike da hatsara a rayuwarshi.
Tabbas dan Allah yayi shi mutun ne mai ibada da imani da kekyawar zuciya, da yawan ambaton sunan Allah da zama da al’wala wlh da badan wannan nagartar da Addu’o’in da suka zame mishi abokan rayuwa suka zame mishi GARKUWA ba, kamar yadda Manzon Allah yace.
“Addu’a’u saiful muminin da tuni sun kasheshi sun sabauta rayuwarshi.
Ummi ban san komai ba kan masarautar Joɗa.
Amman dan al’farma Annabi da darajar Umaymah.
Zan taimaki Yah Sheykh iyakar iyawata.
Zan taimake shi akan abinda Allah ya bani ikon gani”.
A hankali Jamil ya zamo ya zauna a ƙasa.
Yana mai jin tsikar jikinshi na tashi.
Itama Ummi zamowa tayi ta zauna ƙasa.
Hakama Shatu a hankali ta zauna gaban Ummi hannunta tasa.
Ta kamo hannun Ummi cikin muryar kuka tace.
“Ummi ku yarda dani, ku bani haɗin kai, zan tone duk abun cutarwa dake ɗakin Yah Sheykh. Bazan cutar dashi ba, zan taimake shi kamar yadda Bappa na yake bani umarni duk sanda mukayi mgn dashi.
Ummi keda Jamil ina buƙatar taimakon ku.
Amman kafin nan ki gayawa Umaymah in ta amince,
sai inyi aikin amman kada a gayawa Yah Sheykh dan bazai yarda ba.”
Cikin tsoro ido cike da hawaye Ummi tace.
“To Shatu me zancewa Umaymah, me kika gani a ɗakin har ya firgitaki yasaki suma?”.
Cikin kuka tace.
“Ummi kada ku tsaya bincike a kaina.
Ni dai ku yarda dani bazan cutar da kowaba na cikin Masarautar Joɗa sai wanda ya cutar da kanshi Ummi bamu da sauran lokaci mai tsawo fa, komai zai iya faruwa da Yah Sheykh”.
Cikin tsoro da firgici Jamil yace.
“Ba matsala mun yarda dake, ni yanzu taimakon me zan miki?”.
Cikin sauri ta share hawayenta tare da juyowa ta kalli shi kana tace.
“Yauwa Jamilu zaka samo mana mai saka tayis, yazo da katon ɗaya na tayis ɗin irin na bedroom ɗin Yah Sheykh sak da sak.
Sai kuma kayi ƙoƙarin mu samu ya Sheykh in ya fita ya wuni sai dare zai dawo”.
Cikin sauri yace.
“Tayis da mai sawa ba matsala, batun in ya fita sai dare ya dawo kuma inaga.
Sai zuwa jibi ranar ne zaije asibitin gwamnatin Genaral Hospital.
To in yaje can wuni yakeyi wani lokacin sai dare zai dawo”.
Cikin gamsuwa da hakan tace.
“To ba matsala.
Ummi ke kuma ki kira mana Umaymah ki sanar mata, muyi abun da saninta.”
To Ummi tace kana a wurin ta kira Umaymah tayi mata bayani.
Ba wani neman ba’asi tace.
“A barta Ummin Jabeer na amince, tayi duk abinda ya dace a kan mijinta da yayanshi da ƙannenshi dama duk wani abu nashi”.
Cikin jin daɗi ta jinjina kai lokacin da take jin mgnar Umaymah.
Wani irin dogon numfashi taja mai ƙarfi sai gata ta tafi luuuh kan…!
Wasa farin girki? Shatu kadafa allura ta tono garma.
By
*GARKUWAR FULANI*
Ta konta, kamar maiyin bacci kamar wacce ta suma.
Cikin mamaki suka bita da ido kana suka juya suka kalli juna,
Cikin mamaki Jamil yace.
“Ummi suma ta kumayi ne?”.
Kai ta jijjiga mishi alamar a a.
Kana tasa hannun damanta ta gyarawa Shatu’n.
Kwanciyarta.
Tare da cewa.
“Bacci ne tayi”.
Kai ya kuma gyaɗawa cike da mamaki yace.
“Wannan baiwar Allah’n, itama da akwai abin al’ajabi tare da ita.
Da akwai abinda yake a duhu wanda bamu sanshi ba a kanta.”
Cikin gamsuwa da bayan shi Ummi ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Na daɗe da dasa ayar tambaya a kanta, sai dai bani da mai bani amsar dole sai zaman yauda kullum zai ƙara fahimtar dani ko wacece ita.
Yanzu dai Jamil wannan mgnar ta zama sirri tsakaninmu.
Da Allah kada kowa yaji!”.
Cikin nitsuwa yace.
“In Sha Allah Ummi babu wanda zaiji”.
To da haka dai sukaci gaba da hira a wurin.
Cikin Sa’a baccin nata baiyi nisaba ta farka.
Lokacin sallan azahar nayi suka watse.
Bayan sunyi salla da jimawa ne, ta miƙe a hankali ta nufi ɗakinshi.
A falo ta tsaya, tana nazarin to in ta shiga ta sameshi idonshi biyu fa?
Akwai abinda take son idonta ya ƙara gani dan ta tabbatar.
Shi kuwa Sheykh yana ciki, a kwance kamar mafi akasarin lokuta, waya yakeyi da Aunty Hafsat.
Tana ce mishi ya haɗata da amryar zasuyi mgna.
Cikin sanyi yace.
“Bacci, Aunty Hafsat Bacci fa zanyi, afwan ki bari sai anjima mana”.
Cikin sanyinta tace.
“Oho Jazlaan, nace ka haɗani da ita shine wannan magiyar yanzu Yezeed yazo ya nuna min hotunanta wai Hibba ce ta turo mishi.
Tamin kyau sosai, ina son yarinyar.
Zakiya ma tana amshi number ta, wurin Hibba tana kira kuma bata ɗagawa.
Jazlaan haɗani da ita nace ko!”.
A hankali ya yunƙura ya tashi zaune.
Cikin sanyin baccin daya fara yi yace.
“To ɗan katse kiran in naje zan kiraki.”
A hankali ya miƙe tsaye. Al’kyabbar sa ya ɗauka, tare da nufar bakin ƙofar.
Yana mai sa hannunshi cikin rigar al’kyabbar.
Har yazo bakin ƙofar bai gama sa hannun rigar ba ya buɗata da faɗi.
Ita kuma Shatu a hankali ta tura ƙofar.
Ta sako kai ciki dai-dai lokacin kuma shima ya sako kai waje.
Ba zato ba tsammani sukaji sunyi kiciɓis da juna ta faɗa cikin faffaɗan ƙirjinshi.
Cikin sauri ya sauƙo da hannayeshi dake buɗe kuma al’kyabbar na buɗe da faɗinta sanadin sauƙo da hannun da yayine sai ya zama ya sauƙe hannunshi kanta, yayi mata ƙawanya da faffaɗan al’kyabbar jikinshi ya haɗasu wuri ɗaya ya rufesu.