GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ɗan lungun da ɗaya Bedside drower’n take ta shiga.
Kana ta kalli Ummi fuska a juye tace.
“Naɗe min carpet ɗin nan.
To Ummi tace da sauri ta fara naɗe carpet ɗin.
Bayan ta janyeshi da kyar ne, ita kuma Shatu.
A hankali tasa hannun damanta bisa jikin gadon ba tare da ta ɓallashi ba ko, ta cire wani abu a jikinshi ba, ta yunƙura ta tura gadon tare da cewa.
“Bismillahirahamanirahim”.
Da sauri Ummi taja da baya cike da mamaki da tsoron ganin yadda take tura tamfatsetsen gadon mai ɗirkekiyar katifa da ko tura katifar kawai aikine.

Guuuuuuh haka sautin tura gadon yake badawa.

Saida ta turashi har jikin Waldurob.
Kana ta tsaya a tsakiyar inda gadon yake kafin ta turashi.
Dai-dai lokacin kiran Jamil ya shigo wayarta.

Da sauri taje ta buɗe mushi.

Kana suka shigo,. A falon suka bar Ɗalha mai tayis,
kana Jamil ya amshi kayan aikin yabi bayan Ummi yana cewa.
“Yauwa ɗalha ɗan jirani bari inzo mu isa kaga wurin”.

To ɗalha yace kana ya fara cin abincin da Ummi ta saka mishi.

Suna shiga suka maida ƙofar falon suka rufe.

A inda Ummi ta barta a han suka sameta.
Da sauri ta miƙawa Jamil hannun tare da cewa.
“Bani gudumar da ma’ɓamɓarin.”
Cikin sauri ya iso tare da ajiye ɗan buhun ya fito da gudumar da Maɓamɓarin yana mai mamakin yadda aka tura gadon yace.
“Bari Aunty Shatu nuna min ina zan fasa”.
Da sauri tace a a, ku ɗan matsa gefe, musamman ma kai koma can”.
Ta nuna mishi gefe.
Sake mata gudumar yayi jin ta fizgeshi.
A hankali ya tashi sabida cewa da tayi ya tashi.
Ido suka zuba mata, ita kuwa, gudumar tasa ta rinƙa buga tayis ɗin dake wurin saida ta fasa uku lafiyeyyu.
Kana ta ture fasassun tasa maɓamɓari tana ɓalle sauran, saida ta ciresu kab.
Sannan ta fara fasa fulon simintin dake ƙasan.
Da mamaki Ummi ke kallon wurin sabida tasan babu wani fulo da akayi kafin asa tayis ɗin.
Fasashi tayi kana ta fara caccaka ƙasan wurin da matonin, tanayi yana fito da ƙasa.

Shiru sukayi ganin ramin yayi zurfi kuma ba komai.

A haka taci gaba da tono tana kuma faɗaɗa ramin ta ƙasa.

Wani irin zabura Jamil da Ummi sukayi lokacin da suka ga wani baƙin hayaƙi yana fitowa cikin ramin.

Ita kuwa Shatu da sauri tasa hannun damanta taci gaba da tonon.
Tare da yin mgna da sauri tace.
“Jamilu buɗe windows da sauri hayaƙin nan ya fita”.
Cikin rawan jiki yace to.
Kana ya fara buɗe wa da sauri sabida, hayaƙin ya fara cika ɗakin.

Yana buɗe windows ɗin kuwa hayaƙin ya fara fita.
Tonon taci gaba dayi tare da cewa.
“Inama da akwai wani yardajjen mu a kusa, bayan ku biyun nan da yabi hayaƙin nan zaigane mana ina zai shiga cikin sashukan mutanen gidannan shaidar aiki ya koma kan wanda ya yishi.”
Da sauri Jamil yace.
“To ko in fitane inbi hayaƙin”.
Cikin sauri tace.
“A a kada ka fita ku tsaya kaida Ummi.”

Numfashi suka fara sauƙewa, a hankali lokacin da sukaga duk hayaƙin ya gama fita.
Sai kuma suka fara takowa suna zuwa inda take ganin yadda hannunta dake cikin ramin yake karkarwa.
Ga wata zufa dake keto mata kamar da bakin kwarya.
Wani marfin tukunyar ƙasa ta ɗago.
Kana a hankali ta ɗago tukunyar.
Ta ajiyeta gefe kana ta koma ta jingina tana mai jan numfashin.
Cikin sauri Ummi taje ta kunna sauran wutan ɗakin duka, ya zama kamar farin wata.

Jamil ne ya fara leƙa cikin tukunyar.
Da sauri yace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummi zo ki gani”.
Ya ƙarishe mgnar yana sunkuyowa da kai hannunshi zai kama tukunyar ƙasan cikin sauri da ƙarfi Shatu ta buge hannunshi da hannunta na hagu tare da cewa.
“Jininka ɗaya da Yah Sheykh in ka taɓa duk abun zai iya dawowa jikinka.”

Ta ƙarishe mgnar da ɗago hannun ta na dama tasa a ciki.
Tukunyar da sauri ta rumtse idanunta sabida wani irin masifeffen tsikara da taji an mata a hannunta.

A can ƙasar Cameroon kuwa cikin Rugar Duno dake, kusa da Rugar Malam Babayo.
Ba’ana ne zaune bisa buzun aikinshi.
Da kasko a gabanshi yana kallon cikin kaskon gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi cikin tashin hankali da fargaba yace.
“A’a A a Mata kada ki taɓa, baki amince na baki mgnin kariyar tonar sihiriba, iya ganin idan a zuba sihiri a abinci yake na shayar dake shi nanma a bisa dole baki saniba.
Kada ki taɓa zai cutar dake”.
Ya ƙarishe mgnar hawaye na zubo mishi, Allah ya sani baya son abinda zai cutar da Shatu ko kaɗan.

Ita kuwa Shatu a hankali ta fara fito da wasu irin tabka-tabkan layu wanda aka liƙesu da yadin al’kyabba daga gani kasan na Sheykh ne sabida shi ɗaya kesa irinsu a masarautar Joɗa tun yana ɗan yaro matashinsa.
Wani dogon ajiyan zuciya taja tare da fizgo wani dogon maciji a cikin tukunyar ƙasar.
Da sauri Ummi taja da baya, shi kuwa Jamil sai leƙowa yakeyi.

A dai-dai lokacin kuma Sheykh dake cikin Office dinshi na cikin Genaral Hospital Ɓadawaya shi ɗaya, dan yau ba mutane sosai dudu mutun biyar ne kuma ya gama dubasu ya musu komai, yana zaune ko za’a turo wasu.
Wani irin zabura yayi ya miƙe tsaye da ƙarfi tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Sai kuma ya sunkuyo yana kallon yadda babbar yatsarshi ta ƙafar dama wacce zanen maci ke kanta take rawa kar-kar.
Da sauri ya juya ya nufi bathroom ɗin cikin Office dinshi.
Cikin sauri ya zare malum-malum ɗin jikinshi juyowa yayi ya ajiyeta saman kujerarshi.
Kana da sauri ya nufi Bathroom sabida yadda yakejin ana fizgo wani abu kamar jijiya a jikinshi tun daga saman cikinsa kusa da ƙirjinsa, har zuwa kan ɗan yatsarshi.
Da sauri ya cire rigarshi da snglet ɗin, da ido yabi zanen dake jikinshi wanda samanshi zanen kan macijine.
Gaba ɗaya jikinshi rawa ya farayi tamkar mazari.
Duk wata jijiya dake jikinsa saida ta tashi tsaye.
Cikin tashin hankali yake ambaton sunayen Allah da duk addu’o’in da sukazo bakinsa.
Hannunshi yasa ya damƙi bnnarshi data miƙe tayi wani irin harbawa da masifar ƙarfi, riƙeta yayi da kyau jin yadda take tashi tana kumbura da cika tana tsawo tamkar zata faso boxes ɗin shi ta fito woje.
Wannan shine babban tashin hankalinshi dan tsawon shekaru kusan ashirin bai sake ji ko ganin bnnarshi ta miƙe kamar hakaba sai yau.
Karkarwa duk jikinshi keyi, hatta jijiyoyin kanshi dana damatsan hannunshi tasowa sukayi ruɗu-ruɗu jijiyar goshinsa har harbawa takeyi”.
Innalillahi wa innailaihi rajiun yaketa maimaitawa, yanajin kamar ana jan jijiyoyin jikinsa.
A haka ya maida kayanshi kana ya fito.
Sai dai bai samu damar maida gariyar ba, zama kawai yayi bisa kujerar yana rawan sanyi.

A haka abokinshi Dr Arabi ya shigo ya sameshi cikin mamakin ganin yadda yake karkarwa yace.
“Dakta Jabeer lfy kuwa meya sameka”.
Cikin muryar alamun zazzaɓi yace.
“Zazzaɓi ne Arabi. Sanyi nakeji”.
Da sauri ya iso inda yake taimaka mishi yayi ya saka mishi gariyar.
Kana ya kamoshi ya kawoshi bisa tattausan kujerar 3 str dadake cikin Office ɗin ya kwantar dashi.
Aunashi yayi tare da kiran wata Nurse ya gaya mata magungunan da zata amsa musu a Pharmacyn nasu, cewa Dr Jabeer ba lfy.
Ai lokacin ɗaya sai gata da manyan likitoci har uku.
Cikin tarin kulawa, suka fara dubashi ganin yana gab da fita haiyacinsa ne, yasa suka mishi allurar bacci.
Da sauri Dr Arabi kuma ya kira, Jalal ya sanar mishi.
Jalal kuwa dake falon Hajia Mama ba tare da ya gaya mata ba ya miƙe da sauri ya fita.
Tana tambayarshi lfy.
Yace lfy sabida baison tayar mata da hankali.
A bakin ƙofar fita ya haɗu da Ya Affan da sauri ya kamo hanunshi suka juya yana cewa.
“Ya Affan Hamma Jabeer ba lfy, yana Genaral Hospital Ɓadawaya, yanzu Yayan abokina Umar Dr Arabi abokinshi ya kirani ya gaya min yace baida lfy sosai fa”.
Ai da sauri Affan ya fara lalubo car key dake cikin al’jihunsa cikin kiɗima da tashin hankali yace.
“Muje, muje da sauri mu tafi a maidashi Valli Hospital yafi kwararrun likitoci”.
Kusan a tare suka shiga motar Affan suka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button