GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

A falon kuwa Lamiɗo da Galadima da Sarkin bakan.
Ne suka shigo bayan. Sallama yayi musu jagora.

A bisa kujera Lamiɗo da suka zauna sarkin baka kuma a ƙasa.
Hakama Ummi da Hibba.
Jalal da Jamil kuwa tun ɗazu suka fita, suka tafi Side ɗin Mama.
A can suka samu Ya Affan.

Cikin girmamawa Ummi ta ɗan rusunar da kanta tare da cewa.
“Barka da isowa Lamiɗo shugaba mai adalci”.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Barka dai Jakadiya mai gsky,
ya jikin ɗiyar taki, ina take”.
Cikin ƙara rusunar da kai tace.
“To jiki dai da asuba da sauƙi amman kwana mukayi babu bacci.
To rana na fitowa kuma ciwo ya harzuƙa ya zarta na baya”.
A hankali Lamiɗo da Galadima sukace
“Subahanallahi”.
Sarkin baka kuwa.
sunkuyar da kanshi yayi tare da sakin murmushin mugunta,
kana ya gyara riƙon da yayiwa wayarshi yadda, waɗanda suka sashi aikin zasuji bayanin komai da kunnensu.
da kiransu da ya haɗa.
A can kuwa magautan dariyar jin daɗin lbrin.
Sukayi.

A hankali ya kalli Ummi yace.
“Sauƙi a hankali yake samuwa, zai nayi yana lafawa har yazo ya bari gaba ɗaya”.
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa.

A hankali ta miƙe bayan Lamiɗo yace mata.
“Jeki kira min ita tazo”.
To tace kana ta nufi shashin Sheykh.

Shi kuwa Sheykh yana cikin fesa turare kenan.
Ya juyo ya kalli Aysha da ta tashi zaune da sauri tasa hannu a kanta tana yarfa ɗaya tare da cewa.
“Wash! Wash! Wayyoooooooo Allah na!’.
A hankali ya ajiye kwalban turaren kana yazo gaban gadon.
Tare da cewa.
“Sauƙo”. Cikin rawan jiki ta sauƙo tana yarfa hannunta.
Cikin haɗe fuska yace.
“In zakiyi kuka fice min a ɗaki”.
Cikin rauni tace.
“Yah Sheykh zafi! zafi!! zafin nakeji yana dawowa”.
Da sauri ya juyo ya kalli ƙofar ɗakin jin ana bugawa.
Jiyo muryar Ummi ne yasa ya juya ya nufi ƙofar.
Yana buɗewa tace.
“Sheykh, Lamiɗo ne yazo yana son ganin hannun nata”.
Kanshi ya ɗan gyaɗa kana yace.
“Fito kije, Ummi a kawo mata ɗan kwali ta ɗaure wannan dogon gashin da kitseshi ma aikine shiyasa ko yaushe kai a tsefe ai kuwa al’janu kam sayi ta shiga lodi-lodi”.
Da sauri Ummi ta miƙo mishi ɗan kwalin doguwar rigarta dake hannunta tun sanda ta wurgar dashi.
Kanshi ya juya tare da cewa.
“Fito”.
Cikin zubda hawaye ta fito.
Gaban Ummi ta tsaya tana cewa.
“Wayyo Ummey na”.
Cikin tausaya mata Ummi tace.
“Sannu ko”. Ta ƙarishe mgnar tana yafa mata ɗan gyalen.
Kana ta kama hannunta na hagu suka nufi falon.

Shi kuwa Sheykh hiraminshi yasa ya dai-dai-ta komai.
Sai dai abin da ya sashi jin kunyan kanshi da kanshi ganin.
Har yanzu bnnarshi a tsaye ƙiƙam duk da danneta da yayi da boxes.
shi da kanshi in ya sunkuyo yana ganin tudunta kaɗan danma manyan kayane a jikinsa.
matseta yayi kana ya buɗe al’kyabbar da kyau, sannan ya fito ya nufi falon yanajin yadda take harbawa duk da kai tsaye bawai sha’awa yakeji ko makamancin hakaba.

Wayarshi ce kaɗai a hannunshi ya fito.

A falon ya samesu tana zaune gaban Lamiɗo da Galadima.
Gefensu ya zauna.
Sarkin bakan dake gabanta yana kwaɓa mgnine ya kalla tare da cewa.
“A bar wannan mgin haka, kada a sake shafawa”.

Cike da mamaki Sarkin bakan ya ɗago ya kalleshi tare da cewa.
“Sabida me?”.
Idonshi na kan wayarshi yace.
“Nace kada a shafa ko”. Lamiɗo ne ya juyo ya kalleshi tare da cewa.
“Za’a shafa”.
Shi kuwa Sarkin baka ido ya zura musu.
Shi kuwa Sheykh miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Shike nan!”.
Ya ƙarishe mgnar da kallon hannun Aysha mai ciwon.
Kana ya juya ya kalli Ummi tare da cewa.
“Bari in ɗauko Umaymah ta iso”.
Da sauri Hibba ta miƙa tare da bin bayanshi tana cewa.
“Hamma Jabeer inzo muje”.
Kai ya gyaɗa mata, kana suka fita.
Ummi na ce musu.
“Allah ya kiyaye hanya”.
Amin Amin sukace sannan suka fice.

Ita kuwa Aysha zuwa yanzu ta fara gigicewa.
Sai mutsu-mutsu takeyi, tare da shishita.
Galadima ne ya kalli Sarkin baka yace.
“Kayi aikinka!”.
To yace kana ya fuskanceta da kyau yace.
“Kawo hannunki”.
Jiki na rawa ta miƙa mishi hannun tana mai lumshe idonta hawaye na zubowa.
“Sannu ko Mamana”. Lamiɗo ya faɗa cikin tausayawa sabida sunan mahaifiyarshi Aysha.

Ummi ma sannu ta mata.

Shi kuwa Sarkin bakan da yawa ya daƙumo maganin ya labta a kan hannun.
Sannan ya fara shafawa.

Wani irin zillo tayi tare da sunkuyar da kanta ta kifeshi kan hannun kujerar da Lamiɗo ke kai.

Gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi tamkar mazari.
A haka ya gama shafe magungunan sannan ya bata wani yace sai dare ta shanye shi.

Ummi ce ta amsa tare da yi mishi godiya.
Kana Lamiɗo da Galadima sukayi mata sannu da jiki suka tafi.

Suna fita, ta miƙe da sauri ta nufi falon ta.
Da sauri Ummi ma tabi bayanta tana cewa.
“Lafiya kuwa.”
Babu mgna tana shiga kan gado ta faɗa ta kife kanta a filo murya na rawa alamun sanyin zazzaɓi tace.
“Ummi rufeni rufeni sanyi zai kasheni a kashe min AC.”
Da sauri ta ajiye maganin kana ta rufeta da jibgegen blanket ɗin sannan ta juya ta kashe AC’n.

Ta dawo gefenta ta tsaya.
Cikin al’hini take cewa.
“Sannu! Sannu ko Aysha”.
Ina babu mgna sai karkarwa takeyi tamkar zata faɗo ƙasa.

Haka yasa hankalin Ummi tashi.

Shigowar Aunty Juwairiyya ce da ta kawo musu abincin rana.
Dana tarban Umaymah ne.

Cikin mamaki tace.
“Ummi ko dai in kira. Sheykh yazo muje asibitine gafa yadda take rawan sanyi”.

Ummi kam tama rasa bakin mgn, shiru kawai tayi tana riƙe da haɓa.

Suna cikin hakane Hajia Mama ta iso.
Cikin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummin Jabeer ya za’ayi da wannan yariyar ne? Mu tafi asibiti fa, da sauri ta juya ta fita zata kirawo Affan.

Tana fita da miti bakwai. Su Umaymah suka shigo.
Kai tsaye suka wuce har cikin ɗakin jiyo mgnar su Ummi a can.

Shi kuwa Sheykh, asibitin Valli ya wuce.

Umaymah na shiga ta isa bakin gadon.
Zama tayi a gefe tare dasa hannu ta buɗe borgon.
Ganin yadda taketa karkarwa ne, yasa Umaymah ɗagota ta ɗaura kanta bisa cinyarta.
Tana cewa.
“Innalillahi wannan wane irin sabon al’amari ne mai firgitarwa”.
Da sauri tace.
“Hibba kiyi gudu ki kirawo min Jazlaan kada ya fita.”
Da sauri Hibba ta juya ta nufi waje.

Ita kuwa Ummi da Aunty Juwairiyya ko sannu da zuwa Allah bai basu ikon yiwa Umaymah ba sabida ruɗani.

Wani irin numfarfashi ta fara fiddawa a jere-a jere sai ga jikinta ya fara lafawa da rawan da yakeyi.
Wani irin zufa ya fara tsastsafo mata duk ta inda hudar gashi yake a jikinta.

Cikin sanyi suka fara sauƙe ajiyan zuciya.
Suna cewa.
“Alhamdulillah”.

Gyara mata konciya Umaymah tayi ganin tayi bacci.
Buɗe mata borgon tayi kana ta kalli Juwairiyya tare da cewa.
“Kunna AC”.
To tace kana ta kunna.

Ajiyan zuciya ta sauƙe da ƙarfi.
Haka yasa Umaymah ta sauƙo kan gadon.
Cike da al’hinin abin suka fito falonta suka zauna.
Juwairiyya ce taja jakar Umaymah ta kai ɗakin Ummi.
Kana ta fito.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Umaymah sannu da zuwa ya hanya”.
Tallaɓe habarta tayi tare da cewa.
“Uhummmm Alhamdulillah Ummi ya mai jiki”.
Cikin sanyi tace.
“To jiki kam dai babu daɗi.
Sai dai godiyar Allah”.
Cikin sanyi tace.
“Dukkan tsanani yana tare da sauƙin.
Ya iyayenta sunji ko?”.
Kai ta gyaɗa alamun eh.
Juwairiyya ce taje falon ta kawo mata ruwa da abinci.
A hankali tace.
“Juwairiyya ajiye abin cinnan bazai ciwuba”.

Dai-dai lokacin Hajia Mama ta shigo da Affan yana cikin kiɗima.

Ganin Umaymah ne yasa suka zaune kusa da ita tare da cewa.
“Ya jikin nata”.

“Alhamdulillah ta samu tayi bacci.”
Umaymah ta basu amsa.
Cikin kula Hajia Mama tace.
“Sannunki da zuwa, ya hanya”.
Yauwa sannu Alhamdulillah tace.
Hibba ce ta dawo tacewa Umaymah kafin ta fitama ya tafi.
To kawai tace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button