
Ba jinshi takeyi ba bare ta gane abinda yake nufi.
Da sauri ta yunƙura zata sauƙa.
Juyowa yayi ya kamata ya ajiyeta kusa dashi kana ya juyo suna fuskantar juna.
Cikin kuka ta faɗa jikinshi tana cewa.
“Umaymah hannu zai tsinke.
Zafi zai kasheni”.
A hankali ya ruggumeta tare dasa hannunshi ya kamo hannun dake ciwon.
Da sauri tayi tsalle zata zille hakan ne yasa ya ƙara ruggumeta gama ya haɗa jikinsu wuri ɗaya.
cikin sanyi ya fara mata karatu a kunne yana hura mata iskar bakinshi kan hannun
Ajiyan zuciya mai ƙarfi da numfarfashi ta fara sauƙewa da ƙarfi-ƙarfi.
Umaymah kuwa jin shirune yasa, ta nufo Side ɗinsa.
Ganin baya falone.
Tace.
“To ina suke ina ya kaita?”.
Ta ƙarishe mgnar tana tura ƙofar Bedroom.
Tana tura ƙofar sai kuma tayi sauri taja da baya sabida hangosu da tayi yana konce lib yayi rigingine ya ɗan jingina da allon kan gadon.
Kana ita kuma ya kontar da ita kan jikinshi, ya ɗaura kanta bisa ƙirjinshi hannunshi na kan…!
Jinyar Sheykh ta musamman ce. To ya zata kaya ne in ɗan gidan ba’ana yazo. Hege Sarkin baka wa yakewa aikin.
By
*GARKUWAR FULANI*
Ya ruggumeta da kyau a jikinshi.
Jinyadda taketa fizge-fizgen zata kwance kanta.
Wani irin tsuma jikinshi ya rinƙayi can cikin naman jikinshi yake jin tsuman.
A hankali ya manna kanta, kan faffaɗan ƙirjinshi,
hannunta mai ciwon data ɗaura a tsakiyar kan natane ya zubawa ido.
Sosai hannun yayi jazir sai kelli yaki, alamun kumburin da yayi.
A hankali yasa hannunshin ya tallabo hannun.
Wani irin ihu tasaka da ƙarfi.
Sai dai bai bari ihun ya fito daga bakinta ba, yayi maza ya rufe mata baki da tattausan tafin hannunshi yana ta mai-maita.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Tabbas da in ya barta ta kurma ihun shike nan ta tabbata zautacciya,
yin ihun da take son yi dai-dai yake da sihirin ya gama shiga jikinta ya ratsa zai kuma haukatata.
Shiru tayi tana zazzare idanunta da hawaye ke zuba babu ƙaƙƙautawa, shi kuwa Sheykh a hankali ya janye hannun nata data aza a kai ya tallabeshi da tafin hannunshi.
Sannan ya manna ƙirjinshi da nata ƙirjin da kyau.
Har suna iya juyo bugun zuciyar juna.
Sunkuyo da kanshi yayi tsakanin kafaɗarta da wuyatan
Bakinshi ya saita cikin kunnenta.
Hure gashin daya baje kan kunnen yayi ya matsa,
sannan ya kawo bakinshi gab da kunnenta har tattausan lips ɗinshi na taɓa tattausan kunnenta.
Lumshe idonshi yayi tare da gyara tsayuwar nasu da kyau.
Ita kuma sai fiffizgewa take sonshi jikinta duk yana karkarwa ga zufar dake tsiyayo mata.
Hannunta dake cikin hannunshi ya kalla yadda yaketa rawa, gashi zafi jau kamar wuta.
A hankali yayi gyaran murya tare da yin bisimilla.
Cikin ɗan-ɗaga sauti ya fara karanta Suratul Baqra cikin kunnenta cikin fidda harrufan da karsashin yadda zai ratsa kunnuwanta.
Yanashi yana cire tafin hannunshi dake bakinta,
wani irin manna kanta tayi da ƙirjinsa,
ta lumshe idonta wasu hawaye masu ɗumi suka fara kwaranya.
hannunta na hagu dake da lfyar tasa bisa kafaɗanshi ta zagayo wuyanshi da kyau.
Shi kuma hannunshi da ya janye daga kan bakinta ya maida kan ƙugunta ya ruggumeta tsam a jikinshi.
A haka yaci gaba da karatu, in yazo wasu ayoyin yakan maimaita karshensu kafin ya kuma kama forkon na gaba.
A hankali ta fara sauƙe wasu tagwayen numfarfashi, ji takeyi azaba da raɗaɗin yana ɗan lafawa.
Al’farma Annabi da Alqur’ani kenan.
A hankali ta daina duk fizge-fizgen ta dawo sai kukan da takeyi mai sauti amman sautin a hankali ne.
Kuka take sosai ganin hakane, ya gyara tsayuwar tasu.
Kana ya tallabo kanta ya kalleta.
A hankali ya girgiza kanshi tare da jawota suka nufi bakin gado.
Yana cewa.
“Uhummm baku samu wurin zamaba a kanta in Sha Allah bazamu zauna inuwa ɗaya dani da kuba, zaku bar jikinta.”
Ajiyeta yayi kan gadon kana shima ya hau ya zauna.
da sauri ya riƙo hannunta da take son maidashi tsakiyar kanta ɗin.
Karatu ya fara yanayi yana ɗan hura mata sassanyan iskan bakinshi.
Tub, tub, tub, haka yake ɗanyi tare da fesa iskar, kana ya zuba mata ido cikin idanunta.
A hankali tayi ƙasa da kanta.
Shi kuwa haɗe fuska yayi tare da cewa.
“Ɗago ki kalleni mana”.
Kai ta girgiza alamun a a.
Shikuwa hannunshi ɗaya yasa ya tallabo haɓarta, dan ta kalleshi da sauri ta rumtse idanunta.
Cikin kausasa murya yace.
“Buɗe idon ki kalleni!”.
A hankali ta buɗi baki cikin irin Muryar da yaji tayi mgna kwanaki dashi tace.
“Bazan iyaba, kunyarka nakeji!”.
Watsa mata wani kallo yayi tare da cewa.
“Ƙarya ne, bakiji kunyan Allah’n daya haliccemu ya halicceku ya kuma yi mana iyaka a tsakaninmu ya hanaku cutar damu, ta hanyar mazonsa ya ƙaiyade muku dukkan motsinku, ya hanaku cutar da bani Adam.
Duk bakiji kunyarsu ba, kika shiga jikin yarinya ƙarama, kina sata yin wasu abun da ba halinta ba,
bakiji tsoron Allah daya hanakuba.
Bakiji kunyar iyayenta ba, kina cutar musu da ɗiyarsu sai ni?”.
Cikin sanyi murya cike da alamun tsufa, tace.
“Ni bana cutar da ita, Ni ba muguwa bace, ban taɓata cutar da ita ko wani nataba duk tsawon shekarun da nake tare da ita”.
Da sauri cikin faɗa yace.
“To meyasa zaki shiga jikinta”.
A hankali cikin zubda hawaye tace.
“Ni tun tana jaririya nake jikinta, kuma ni makaran gadone na ahlinsu daga wurin kakarta mahaifiyar mahaifinta”.
Da sauri yace.
“Rufe min baki, makaran gado,
Ku kuɗine ko wata kadara ce, ku cikin kadarorin da Allah (S.W.A) ya lissafa cikin jerin jadawalin abinda za’a gada?.
Ko dan kinga ina binki a hankali ne yasa zakiyi min zancen banza na mutanen banza”.
A hankali tace.
“Jikana ka kontar da hankalinka muyi mgna”.
A fusace yace.
“Waye jikan naki, kina Jinnu ina bani Adam ta ina na zama jikanki.
An ƙi a kontar da hankali tsohuwa dake kinzo kin liƙewa yarinya kina ƙoƙarin sata tana yaye suturar jikinta tana shirin yin ihu.
Ko baki san cewa matar aure bace, baki san daraja da kimar dake cikin aure bako?”.
Cikin fushi itama tace.
“Ni bani nasata yarda kallabin kanta ba, zafin ciwo da takeji ne ya gigitata yasata yarda kalkabinta.
Sannan batun ihu da kakeyi kuwa.
Aikin da mugayen Masarautar Joɗa sukayi data taɓane yake shiga jikinta.
Ni kuwa na zone sanadin karatun Rugyan da kayi ta mata, amman duk wancan abun da takeyi ni bana kusa ma.
Kuma ni ba mai cutarwa bace.
Batun darajar aure kuma na fika sani.
Kai kama tsaya inda takene bare ka raya auren ka tabbatar da ita matarka ce kai mijinta ne?.
Kasa sabgogi a gabanka, kana sane da magautanka sun saka a tsakiya kayi, burus dasu, suna neman rabaka da rayuwarka.
Ita kuma dole in taimaketa sannan dama Aysha in dai bata da lfy ko zazzaɓi ne tana kuka haka ciwonta yake.”
Cikin haɗe fuska yace.
“Eh wato da ban ƙonaki bane, kikemin baki ko. T taimako bana son taimakonki ki fitamin a jikin matata, bana so, zakisa tayi ihu ta fita tsakiyar masarauta bayan kin san inada magautan to meyasa zaki nemin abinda zaisa magautana farin ciki.
Tai mako kuma bama so, muda mukeda ubangijin taliƙai wanda yasan zahiri da baɗinin shi yake taimaka min, ba tare da yasa mana ciwon kai ko fita haiyaci ko kukaba dan haka fice min a jikin matata”.
Murmushi tayi tare da jinjina kai kana tace.
“Matarka kuma yau”.
A hatsale yace.
“A a matarki ce, in ba matata ba?.”
Sai kuma yayi bisimilla zai fara karatu da sauri tace.
“Tsaya Muhammad Jabeer ɗan Habibullah jikan Nuruddee, Bubayero, Joɗa, Sule Usmanu jinin sarki Muhammad Bello, ni bazanyi faɗa da kaiba kafi ƙarfin haka duk da ni ba cutar daku nakeyi ba. Naga ranka ya ɓaci ina jinin.
Wai matarka kace ko?”.
Wani irin kallo yayi mata tare da ɗago hannun shi zai shararamata mari yana cewa.
“Wai ne ma ko?”.
Da sauri tayi murmushi tare da cewa.
“Kamar gibtawar ido zan gudu jikinta, ka kwaɗa marin a kanta”.
Ai fa a kufule ya kai marin.
Hannunshi na isa fuskarta tana yin atishawa.
Zafin marin ya sauƙa kan fuskarta cikin azaba ta ɓare baki tare dasa kuka tana mai shafa haɓarta ido na zubda hawaye a gigice idonta na ganin duhu sabida zafin marin bata gama dawowa haiyacinta ba murya na rawa tace.
“Wayyo Allah na me nayi maka zaka mareni, ka barni inji da ciwo ɗaya mana”.
Hararanta yayi tare da miƙewa ya sauƙa gadon yana cewa.
“Mutun jiki duk al’janu, sai hegen bakin rashin kunya mutun in ba lfy bazaiyi addu’a ba sai kuka”.